Kano: Jaruma Sadiya Haruna Ta Fita Daga Daurin Talala

Fitacciyar matashiyar nan da ke amfani da kafofin sada zumunta, Sadiya Haruna, ta kammala ɗaurin-talalar da wata kotun shari’a da ke Jihar Kano a arewacin Najeriya ta yi mata. Mai magana da yawun hukumar kula da gidajen yarin jihar, DSP Musbahu Lawan Kofar Nasarawa ne ya tabbatar wa BBC Hausa labarin a ranar Talata. Alkalin kotun Mai shari’a Ali Jibrin ya yanke wa Sadiya Haruna hukuncin ɗaurin-talala na wata shida, inda ya yi umarni ta riƙa zuwa makarantar Islamiyya domin koyon “tarbiyya” da kuma “sanin yadda za ta riƙa mu’amala…

Cigaba Da Karantawa

Kimanin ‘Yan Najeriya 100 Cutar Lassa Ta Kashe A 2021 – NCDC

Rahoton dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar a yayin da annobar korona ke ci gaba ratsa sassan Najeriya, sabon rahoton hukumar NCDC ya nuna cewa zazzaɓin Lassa ya halaka mutum 92 a shekarar 2021. Kazalika, rahoton ya ce ya zuwa lokacin rahoton Mako na 50, jumillar mutum 454 ne suka harbu da zazzaɓin a ƙaramar hukuma 66 da ke jiha 16 na faɗin Najeriya da kuma Abuja babban birnin ƙasar. Jiha uku daga ciki da suka haɗa da Edo (197) da Ondo (159) da Taraba (21)…

Cigaba Da Karantawa

Adamawa: An Shawarci Kiristoci Da Koyi Da Halayyar Yesu Almasihu

An kirayi mabiya addinin kirista a jihar Adamawa da suyi koyi da halayen Yesu Almasihu domin samar da hadin kai dama wanzar da zaman lafiya a tsakanin Al’umma baki daya. Shugaban kungiyar kiristoci a Najeriya shiyyar jihar Adamawa, Bishop Stephen Dami Manza ne yayi wannan kira a lokacin da yake magana da manema labarai dangane da yadda ake gudanar da bikin kirsimeti a Yola. Bishop Manza yace koyi da halayen Yesu Almasihu zai tamaka wajen nunawa juna kauna da kuma samun cigaban mabiya addinin na kirista a jiha dama kasa…

Cigaba Da Karantawa

Bamu Da Burin Da Ya Wuce Yin Aure – Tagwayen Shirin Dadin Kowa

Jaruman shirin Dadin Kowa Hassana Yusuf da Hussaina Yusuf wadanda aka fi sani da’ yan biyun Shirin Dadin Kowa sun bayyana aniyar su ta yin aure a nan gaba kadan. Jaruman su bayyana Hakan ne a lokacin tattaunawar su da Dimukaradiyya in da su ke cewa. “Mu a yanzu babban burin mu shi ne nan gaba kadan mu yi aure wannan shi ne abin da ya rage a gare mu domin duk wani suna da a ke yi a cikin harkar fim mun riga mun yi”.Hassana da Husaina Da muka…

Cigaba Da Karantawa

Zulum Ya Taka Wa Masu Gwarzantashi A Kafafen Sadarwa Birki

Rahotanni daga Birnin Maiduguri na Jihar Borno na bayyana cewar Gwamnan jihar da ke arewa maso gabashin Najeriya, Babagana Umara Zulum, ya roki masu kwatanta ayyukansa da na sauran gwamnoni su daina a kafafen sadarwa na zamani. Ya yi rokon ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Isa Gasau ya fitar ranar Litinin. Gwamnan ya yaba wa mutanen da ke tallata ayyukansa a shafukan sada zumunta, sai dai ya ce bai kamata a rika kwatanta “ayyukan da na sauran gwamnoni ba, tun da dukkan jihohin suna da bambanci”.…

Cigaba Da Karantawa

Korona Ta Yi Tasiri A Harkar Fasahar Zamani – Pantami

Labarin dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, Ministan Sadarwa na Najeriya, ya ce cutar Korona ta kara habaka bukatar yin la’akari da fasahar zamani ta yadda za a magance kalubalen da annobar ta haifar. An ruwaito cewa, ministan ya bayyana hakan ne a yayin taron gudanar da harkokin mulki na intanet na Afirka ta 2021 mai taken ‘Ci gaban sauye-sauyen fasahar zamani a Afirka ta fuskar rikici.’ Ministan ya fadi haka ne a lokacin da yake magana ta bakin wani darakta…

Cigaba Da Karantawa

Ba Domin Buhari Ba Da Najeriya Ta Dade Da Wargajewa – Malami

Rahotannin dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Antoni Janar na ƙasar nan kuma ministan shari’a, Abubakar Malami SAN, yace shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ceci Najeriya daga rushewa cikin shekarar farko da kafa gwamnatinsa. Abubakar Malami yace Buhari ya samu kasar nan a dai-dai lokacin da tattalin arziki ke gab da rushewa, wanda ka iya jawo watsewar ƙasar baki ɗaya kowa ya kama gabansa. Ministan, wanda ya faɗi haka a wani shirin gidan Radiyo a jihar Kano, yace kowane bangare na tatattalin arzikin Najeriya ya samu…

Cigaba Da Karantawa

Malaman Addini Sun Taka Muguwar Rawa Wajen Jefa Najeriya Halin Da Take Ciki – Mahadi Shehu

An bayyana cewar malaman addini sun taka wata irin muguwar rawa wajen jefa Najeriya halin da ta tsinci kanta ciki na taɓarɓarewar tsaro da koma baya. Bayanin haka ya fito ne daga bakin sanannen ɗan kasuwar nan mazaunin garin Kaduna Dr Mahadi Shehu a yayin wata tattaunawa da manema labarai da yayi a Kaduna. Dr Mahadi ya kara da cewar wadannan Malaman Addini sune suka hau munbari suka yi ma wata Jam’iyya kamfe suka tsarkake ‘yan takarar ta, sannan a hannu guda suka kafirta wata Jam’iyya da ‘yan takararta. “Matsalolin…

Cigaba Da Karantawa