Buhari Ya Gagari Korona – Fadar Shugaban Kasa

Rahoton dake shigo mana daga Fadar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta ce shugaban ƙasar lafiyarsa ƙalau bayan an samu rahoton cewa makusantansa sun kamu da cutar korona a ƙarshen mako. Mai magana da yawun fadar Femi Adesina ne ya bayyana hakan lokacin da ya bayyana ta cikin shirin Sunday Politics na gidan talabijin na Channels ranar Lahadi. Da aka tambaye shi ko Buhari ya killace kansa sai ya ce: “Ina ganin shugaban ƙasa lafiyarsa ƙalau, yana ci gaba da ayyukansa kamar yadda ya saba. Amma idan wani na kusa da…

Cigaba Da Karantawa

Zamfara: ‘Yan Daba Sun Tarwatsa Taron PDP

Rahotanni daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar wasu gungun matasa dauke da makamai da ake kyautata zaton ‘yan daba ne sun kai hari filin da jam’iyyar PDP take gudanar da taro a birnin na Gusau. Gidan talbijin na Channels ya rawaito cewa tun da fari an so a gudanar da taro a Zaitun Oil mill, da ke bayan hukumar alhazai amma aka sauya zuwa Command Guest House da ke Gusau. Rahotanni sun ce ‘yan dabar siyasa sun yi wa wurin dirar-mikiya da sanyin safiyar ranar Litinin inda…

Cigaba Da Karantawa

Ba Zan Manta Tagomashin Da Harkar Fim Ta Yi Mini Ba – Safna Maru

Tsohuwar Jaruma a Masana’antar shirya fina-finai ta Kannywwod Kuma Furodusa Sapna Aliyu Maru tace ba zata manta da harkar fim ba domin ita ce ta zamo Silar duk wani abu da ta samu a rayuwar ta. Jarumar ta bayyana Hakan ne a lokacin tattaunawar su da Jaridar Dimukaradiyya in da take bayyana cewa. “Magana ta gaskiya duk wanda ya sanni da harkar fim ya sanni, duk da cewar a yanzu na Dade ba na yin fim saboda harkokin da suke gaba na, Amma dai alhamdulillahi harkar fim ta yi mini…

Cigaba Da Karantawa

Za Mu Koyar Da Matasa Dubu 30,000 Ilimin Fasahar Zamani – Pantami

Rahoton dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Pantami, yace za’a horad da karin matasan Najeriya sama da 30,000 ilimin fasahar zamani. An ruwaito cewa wannan na ɗaya daga cikin amfanar da yan Najeriya za su yi da hadin guiwar ma’aikatar sadarwa da kamfanin Huawei Technologies Nigeria. Ministan ya yi wannan jawabi ne yayin rattaba hannu a yarjejeniyar fahimtar juna (MOU) tsakanin ɓangarorin biyu, da nufin ƙara inganta ilimin zamani (Digital Literacy) ga yan Najeriya. Kazalika kamfanin ya yi…

Cigaba Da Karantawa

Babu Bambanci Tsakanin Musulmi Da Kirista A Bauchi – Gwamna Bala

Rahoton dake shigo mana daga Jihar Bauchi na bayyana cewar Gwamnan jihar Bala Muhammed, ya bayyana cewa kiristoci suna da yanci kwatankwacin na yan uwansu musulmai, wanda ya kamata a girmamashi a faɗin Jihar Bauchi. An ruwaito Gwamna Bala Muhammed na faɗin haka yayin da shugaban kungiyar kiristoci, (CAN), Rabaran Abraham Damina, ya jagoranci tawagar kiristoci suka kai masa ziyarar bikin Kirsimeti a fadar gwamnatin Jihar Bauchi ranar Asabar. Gwamnan yace a baya an watsar da kiristoci a harkokin gwamnatin jiha, amma gwamnatinsa ta kara yawan su a cikin gwamnatinsa…

Cigaba Da Karantawa

Babu Sauran Sulhu Da ‘Yan Bindiga Sai Kisa – Masari

Labarin dake shigo mana daga Jihar Katsina na bayyana cewar Gwamnan Jihar Aminu Bello Masari ya yi fatali da maganar zaman sulhu da yan bindigan, waɗanda suka addabi jiharsa da sauran jihohin arewa ta yamma. Masari ya bayyana matsayarsa ne yayin zantawa da kafar watsa labarai ta DW hausa, ranar Asabar. Gwamnan ya maida martani ga wasikar dake yawo ta neman zaman sulhu, wanda gawurtaccen ɗan bindiga Bello Turji, ya aike wa gwamnati. Gwamna Masari, wanda a baya gwamnatinsa ta rungumi tattaunawar sulhu, yace ba sauran tattaunawar sulhu tsakaninsu da…

Cigaba Da Karantawa

Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Bi Gida-Gida A Zariya

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar wasu ‘yan bindiga sun fasa gida-gida a yankin Wusasa dake Zariya inda suka sace mutune. An ruwaito cewa maharan sun farmakin yankin ne mintuna kaɗan bayan dare ya raba, inda da farko sun yi awon gaba da mutum 8 kafin suka sake dawowa suka sace Mutum 5. Da yake tabbatar da faruwar lamarin, shugaban yankin Wusasa, Isyaku Yusufu, yace maharan sun shiga gida-gidan waɗan da suka sace yayin da suke bacci. Kakakin rundunar yan sandan Kaduna, ASP Muhammed Jalige, bai daga kiran wayar…

Cigaba Da Karantawa

Rashin Adalcin Da ‘Yan Najeriya Ke Yi Wa Buhari Ya Wuce Hankali – Minista

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya roki yan Najeriya su daina ɗora wa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, laifin duk kalubalen da suke fuskanta a ƙasa. Amaechi, wanda tsohon shugaban ƙungiyar gwamnoni ne, ya yi wannan furucin yayin wata hira da Channels TV mai taken, “Hard Copy.” Minsitan ya yi ikirarin cewa mutane suna zargin shugaban ƙasa Buhari da abin da bai shafe shi ba, inda suke ɗora wa shugaban laifi akan abin da hakki akai. “Komai muka ɗauko sai mu dora wa gwamnati,…

Cigaba Da Karantawa