Kaduna: Mafarauta Sun Fasa Garken ‘Yan Bindiga

Wasu mafarauta a kauyen Udawa da ke karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna sun kama wani dan bindiga a wani daji da ke kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari. Mafarautan sun kuma kubutar da wasu mutanen kauyen guda 9 da aka yi garkuwa da su a farmakin da suka kai wa ‘yan bindigar da ke addabar yankin. Jaridar Aminiya ta rawaito cewa mafarautan sun yi wa barayin kwanton bauna ne kwanaki bayan da suka far wa ayarin motocin matafiya a kan babbar hanyar. Wani mai fada a ji a yankin…

Cigaba Da Karantawa

Gwarzon Kare ‘Yancin Bakar Fata Desmond Tutu Ya Mutu

Fitaccen ɗan gwagwarmayar nan ta ƙwato ƴancin baƙaƙe a Afirka ta Kudu, Acibishof Desmond Tutu ya rasu. Fadar Shugaban Ƙasar Afirka ta Kudu ce ta sanar da rasuwar Tutu, wanda ya lashe kyautar gwarzon zaman lafiya ta duniya. Fadar ta ce Acibishof Tutu ya rasu a yau Lahadi ya na da shekaru 90 da haihuwa. Kawo yanzu dai fadar shugaban kasar ba ta baiyana abin da ya haifar da rasuwar ta sa ba. Sai dai kuma tun a shekarar 1990 likitoci su ka gano ya kamu da cutar jeji, inda…

Cigaba Da Karantawa

Duniyar Fina-Finai: Jaruma Maryam Jan Kunne Ta Dawo Fim

A yanzu haka dai tsohuwar jaruma a Masana’antar shirya Fina finan hausa Kanywood Maryam Jankunne ta dawo harkar fim bayan ta shafe tsahon shekaru da ba a ganin fuskarta a cikin Masana’antar. Maryam ta shiga harkar fim a shekarar 2005 daga bisani tayi Aure a shekarar 2008. Jankunne na daya da ga cikin jarumai mata da suka taka rawa a masana’antar Kannywood a shekarun baya kafin tayi Aure. Maryam tayi zamani da irin su Fati Muhammad, Rukayya Dawayya, Rashida mai sa’a, Mansurah Isah da sauran jaruman da suka yi fice…

Cigaba Da Karantawa

Za A Kara Daukar Matasa Dubu 400 Aikin N-Power – Ministar Jin Kai

Labarin dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministar Ayyukan Agaji, Jinƙai da Inganta Rayuwa, Sadiya Farouq ta bayyana cewa kwanan nan za a ƙara ɗaukar matasan N-Power 400,000. Ta yi wannan albishir ne ranar Laraba a Kano, lokacin da ta ke jawabi wurin rufe kwas ɗin horas da matasa fasahar N-Knowledge a Kano, waɗanda aka kammala horar da su a ƙarƙashin Rukunin C. Minista Sadiya ta ce ƙarin matasa 400,000 ɗin da za a ɗauka duk su na cikin matasa miliyan ɗaya da Shugaba Muhammadu Buhari…

Cigaba Da Karantawa

Babu Alaka Tsakanina Da Shugaban ‘Yan Bindiga – Sanata Marafa

Rahotanni daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar ɗaya daga cikin shugabannin jam’iyyar APC na jihar Sanata Kabiru Garba Marafa, ya ce ba ya da alaka da gawurtaccen dan bindigan nan, Abdulmuminu Moossa dake jihar Sokoto. Sanatan ya bukaci ‘yan sanda, jami’an hukumar DSS da sauran jami’an tsaro da su gabatar da rahoton da zai nuna alakarsa da Moossa, kamar yadda wadanda ya kira da sunan maƙiya ke yaɗawa. A wata takarda wacce ofishin kamfen din sanatan ya saki a ranar Juma’a, ya ce lokaci ya yi da…

Cigaba Da Karantawa

Buhari Ya Nesanta Kanshi Da Rikicin APC A Jihar Kano

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Fadar Shugaban kasa ta yi fashin baki game da ikirarin da wasu yan siyasa a jihar Kano ke yi na cewa Shugaba Muhammadu Buhari na marawa wani tsagin shugabancin APC baya. Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya barranta maigidansa daga maganar marawa wani tsagi baya. Ya bayyana hakan a jawabin kar ta kwana da ya saki da daren Asabar, 25 ga Disamba, 2021. Za ku tuna cewa APC ta rabe biyu a jihar Kano ana…

Cigaba Da Karantawa

Sabuwar Korona: Najeriya Na Mataki Na Uku A Nahiyar Afirka

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta bayyana cewa mutum 49 ne ke dauke da kwayoyin cutar korona samfurin Omicron a Najeriya zuwa yanzu. Manajan kula da shashen yaɗuwar cututtuka na Hukumar NCDC, Luka Lawal, ne ya sanar haka a taron da ya yi da manema labarai a Abuja. Lawal ya ce daga ranar Litini Najeriya ta zama ƙasa ta uku a jerin kasashen Afrika da samfurin Omicron ta fi yawa baya ga kasashen Afrika ta Kudu dake da mutum 1,296…

Cigaba Da Karantawa