Da Dumi-Dumi: Sabuwar Korona Ta Yi Babban Kamu A Fadar Shugaban Kasa

Rahoton dake shigo mana yanzu daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Sabuwar nau’in cutar Korona ta barke a fadar Shugaban kasa, Aso VIlla, inda manyan hadiman Shugaba Buhari da manyan jami’an gwamnati suka kamu da cutar. An bankado cewa sakamakon gwajin da aka gudanar ya nuna cewa akalla manyan na kusa da Buhari guda hudu sun kamu da cutar. Daga cikinsu akwai Sakataren din-din-din na fadar Shugaban kasa, Tijjani Umar; Dogarin Buhari, ADC Kanal Yusuf Dodo; CSO Aliyu Musa da mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu. Hakazalika akwai…

Cigaba Da Karantawa

Kungiyar Inyamurai Ta Soki Buhari Kan Kisan Da ‘Yan Bindiga Ke Yi A Arewa

Ƙungiyar ƙabilar Igbo ta Ohanaeze Ndigbo ta bayyana takaicinta kan yadda ƴan bindiga a arewacin Najeriya ke kisan jama’a saki ba ƙaidi. Mai magana da yawun ƙungiyar Chief Alex Ogbonnia ya shaida wa jaridar Punch cewa yadda al’ummar arewa waɗanda a baya ke zaman ƴan ga ni kashenin shugaba Buhari ke fitowa suna zanga-zanga kan matsalar tsaro a baya bayan nan, na nuna yadda al’amura suka ɓalɓalce. ”Ba wai a arewa kaɗai ake zubar da jini ba, dukkan sauran sassan Najeriya ma irin na faruwa a halin da ake ciki”…

Cigaba Da Karantawa

Adamawa: An Shawarci Iyaye Su Dage Wajen Ba ‘Ya’ya Tarbiyya

An kirayi iyaye da su kasance masu ba ‘ya’yan su inganceccen tarbiya domin ba yara tarbiyya na gari yana da matukan muhimmanci a tsakanin al’umma baki daya. Mallam Muhammed Umar Zingin ne yayi wanna kira a lokacin da yake gabatar da nasiha a wajen taron kwamitin Women in Da’awa karo na farko a jihar Adamawa. Muhammed Zingina yace iyaye su sani fa samun yara nagari suna daga cikin abin da mutum zai bari suna yiwa iyayensu addu’a suna raye ko sun mutu, don haka yana da mutukar muhimmanci iyaye su…

Cigaba Da Karantawa

Tashin Hankali: Matashi Ya Babbaka Uwarshi Har Lahira A Jihar Neja

Mazauna unguwar Darusalam da ke Minna, Jihar Naija sun tashi cikin kaɗuwa da firgici bayan da wani matashi, mai suna Steven Jiya, ya bankawa mahaifiyarsa, Comfort Jiya wuta. Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa a ranar Litinin ɗin da ta gabata ne dai Steven, wanda ɗan ƙwaya ne, ya dawo da ga garin Suleja a Jihar Naija ɗin dai, inda bayan ya dawo gida ne, sai kawai ta raya masa cewa ya ƙona mahaifiyarsa. Jaridar ta ce a lokacin Comfort, wacce tsohuwar Shugabar makarantar sakandire ce, tana tsaka da girki…

Cigaba Da Karantawa

Harkar Fim Har Yanzu Ina Jan Zarena Bai Tsinke Ba – Abba Al-Mustapha

Fitaccen Jarumi a Masana’antar shirya fina-finai ta Kannywwod Abba Almustapha yace har yanzu ba a daina yayin sa ba, a cikin Masarautar kannywwod, duk da ba Koda yaushe ake ganin sa a cikin harkar fim din ba. Jarumin ya bayyana Hakan ne a lokacin tattaunawar su da Jaridar Dimukaradiyya dangane da masu cewar an daina yayin sa a harkar fim. Sai yace “Gaskiya ba daina yayina aka yi ba domin mun kafa tarihi a Masana’antar da baza a taba manta damu ba” Inda ya Kara da cewar “Kowa ya san…

Cigaba Da Karantawa

2023: Babangida Ya Goyi Bayan Osinbajo

Rahotanni daga Mina babban birnin Jihar Neja na bayyana cewar tsohon shugaban Kasa Ibrahim Badamasi Babangida ya ce mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ne ya fi dacewa ya jagoranci Najeriya a 2023. Babangida ya bayyana haka ne a lokacin da yake karbar bakuntar kungiyar ‘Osibanjo Grassroot Organisation’ a gidan sa dake garin Minna. ” Osinbajo mutum ne mai hakuri da hangen nesa sannan yana da tausayi da son hadin kai Najeriya. Hakan ya sa naga babu wani dan Najeriya da ya fi dacewa ya shugabanci kasar nan a 2023. ”…

Cigaba Da Karantawa

Kano: Shugaban Majalisar Malamai Ya Fice Daga APC

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar Shahararren malamin addinin musulunci a jihar kuma Shugaban majalisar Malamai ta Jihar Malam Ibrahim Khaleel, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar APC mai mulki. Shehin Malamin ya shaida wa jaridar Dailytrust cewa ya rubuta takardar murabus daga APC duk da har yanzun bai miƙa ta ga shugabannin jam’iyya ba. Ya ƙara da cewa dalilin da yasa bai miƙa takardar murabus ɗin ba shi ne saboda rikicin dake faruwa a APC reshen Kano, wanda a yanzu yake gaban kotu, ana buga shari’a.…

Cigaba Da Karantawa

An Shiga Binciken Gaskiyar Zargin Ko Malami Na Sarrafa EFCC

Hukumar EFCC da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin kasa taannati ta ce tana gudanar da bincike kan zargin cewa ministan shariar ƙasar, Abubakar Malami ne yake sarrafa hukumar, sai abin da ya ce ta ke yi. Binciken EFCC ya shafi wani sautin da ake yadawa ne ta intanet wanda a ciki ake zargin cewa Malami ne yake juya hukumar a binciken da ta ke gudanarwa da ya shafi cin hanci da rashawa. Hukumar EFCC ta ambato wani jami`inta mai suna Mohammed Idris, wanda ɗan sanda ne kuma…

Cigaba Da Karantawa

Kirsimeti: Ba Zan Sauka Daga Mulki Ba Sai Na Cika Alkawuran Da Na Yi – Buhari

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta yi watsi da duk alkawuran da ta yi ba lokacin yakin neman zaɓe kafin cikar wa’adinsa. Shugaban ya bayyana haka ne a sakonsa na Kirsimeti ga ’yan Najeriya, inda ya ce yana taya Kiristoci a Najeriya farin ciki kamar sauran mabiya a duniya don gudanar da bikin a wannan shekarar. A cikin saƙon, shugaban ya roƙi ƴan Najeriya su yi rigakafin korona domin rage bazuwar annobar. Ya kuma taɓo batun tsaro…

Cigaba Da Karantawa