Adamawa: An Shawarci Ma’aikatan Kananan Hukumomi Da Hada Kai

Rahotanni daga Yola babban birnin Jihar Adamawa na bayyana cewar An kirayi ma’aikatan kananan hukumomi da su kasance masu hada kansu a koda yaushe domin ganin an samu cigaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumomin wato NULGE a jiha dama kasa baki daya. Shugaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi a Najeriya shiyar jihar Adamawa Hamman Jumba Gatugal ne yayi wannan kira a lokacin da yake karban rantsuwa a matsayin shugaban kungiyar a jihar Adamawa, An dai gudanar da bikin rantsar da sabbin shugabannin kungiyar a gidan saukan baki na kungiyar dake Yola. Hamman…

Cigaba Da Karantawa

Da Dumi-Dumi: Gwamnati Ta Sanar Da Ranakun Hutun Kirsimeti

Labarin dake shigo mana yanzu daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayya ta sanar da ranakun 27 da 28 na watan Disambar 2021 da kuma ranar 3 ga watan Janairun 2022 a matsayin ranakun hutun Kirsimeti hade da na sabuwar shekara. Wannan na fitowa ne daga sanarwar da ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ya fitar a yau Laraba wadda aka rarraba ta ga manema labarai a Abuja. A cikin sanarwar da ta iso mana da safiyar yau Laraba Ministan ya bayyana cewar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari…

Cigaba Da Karantawa

Ta’aziyyar Ganduje Ga Kwankwaso Ta Haifar Da Surutai

Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar Gwamnan Jihar Abdullahi Ganduje ya yi wa tsohon ubangidansa, Sanata Rabiu Musa-Kwankwaso, ta’aziyyar rasuwar Inuwa Musa-Kwankwaso kanin tsohon Gwamnan. An ruwaito cewa, sakon ta’aziyyar na kunshe a wata takarda da kwamishinan yada labarai, Muhammad Garba, ya fitar a ranar Talata a Kano mai ɗauke da sa hannun Gwamnan. Ganduje ya kwatanta mutuwar Injiniyan aikin noman da babban rashi ga ‘yan uwansa, jiha da kasar baki daya, duba da irin kwazo da kwarewar da yake da ita. “Ya kebance kansa a matsayin ma’aikacin gwamnati…

Cigaba Da Karantawa

Ta’aziyyar Ganduje Ga Kwankwaso Ta Haifar Da Surutai

Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar Gwamnan Jihar Abdullahi Ganduje ya yi wa tsohon ubangidansa, Sanata Rabiu Musa-Kwankwaso, ta’aziyyar rasuwar Inuwa Musa-Kwankwaso kanin tsohon Gwamnan. An ruwaito cewa, sakon ta’aziyyar na kunshe a wata takarda da kwamishinan yada labarai, Muhammad Garba, ya fitar a ranar Talata a Kano mai ɗauke da sa hannun Gwamnan. Ganduje ya kwatanta mutuwar Injiniyan aikin noman da babban rashi ga ‘yan uwansa, jiha da kasar baki daya, duba da irin kwazo da kwarewar da yake da ita. “Ya kebance kansa a matsayin ma’aikacin gwamnati…

Cigaba Da Karantawa

Uwargidan Shugaban Kasa Ta Tura Ma’aikatanta Hutun Dole

Rahoton dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar uwargidan shugaban ƙasa Aisha Muhammadu Buhari, ta umarci ma’aikatan ofishinta su fara hutun sai baba ta gani, a wani ɓangare na tunkarowar ƙarshen shekara da kuma bikin kirsimeti. Cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafinta na Instagram, an bayyana cewa za a rufe ofishin ɗungurngum, har abun da hali ya yi. ”Za a iya riƙa gudanar da muhimman ayyuka ta Internet kamar yadda aka yi a baya’, don haka daga yanzu kowa ya tafi hutu sai an ji…

Cigaba Da Karantawa

Kasafin Kudin 2022: Majalisa Ta Amince Da Tiriliyan 17

Labarin dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar bayan watanni biyu suna tattauna a kai, yan majalisar wakilai sun amince da daftarin kasafin kudin Shekarar 2022. ‘Yan majalisan sun yi wasu sauye-sauye cikin abinda Shugaba Buhari ya gabatar a kasafin Daga ciki akwai karawa wasu ma’aikatu kudi da kuma kiyasin farashin danyen man fetur. Majalisar wakilan tarayya a ranar Talata, 21 ga Disamba 2021, ta amince da daftarin kasafin kudin 2022 da Shugaba Muhammadu Buhari ya gabata mata a watan Oktoba. Maimakon Naira Tiriliyan 16.39 da Buhari…

Cigaba Da Karantawa

Matsalar Tsaron Kaduna: El Rufa’i Ya Gana Da Buhari

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, ya samu ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Aso Villa a Abuja ranar Talata. Ya samu rakiyar Samuel Aruwan, kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna. Bayan ganawar gwamnan da shugaban kasan, wani hoton Gwamna El-Rufai da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana wanda ya janyo maganganu daga jama’a. Kamar yadda hadimin shugaban kasar, Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na Facebook, an ga Gwamna Malam Nasir Ahmad El-Rufai a gurfane…

Cigaba Da Karantawa

Buhari Ya Nuna Dattaku A Fatali Da Kudurin Zabe – Gwamnoni

Ƙungiyar gwamnonin Najeriya ta ce shugaba Muhammadu Buhari ya yi abin a yaba kan ƙin sanya hannu kan sabuwar dokar zaɓe da Majalisar Dokokin ƙasar ta amince da ita. Shugaban ƙungiyar kuma gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi ne ya bayyana hakan bayan wata ganawa da shugaban ƙasar a fadarsa da ke Abuja. Ya ce gwamnoni ba sa adawa da duk wani shiri na fitar da ƴan takara, sai dai ya kamata a yi abun da hankali zai ɗauka. Gwamnan ya ce ”Bajintar da shugaban ƙasa ya yi ta amincewa da…

Cigaba Da Karantawa