Neja: ‘Yan Bindiga Sun Harbe Mutum 16 Suna Cikin Sallah A Masallaci

Bala’in ya faru ne ana tsaka da gabatar da ibadar Sallar Asubahi da misalin ƙarfe biyar da rabi na subahi. Sakataren Gwamnatin jihar Neja Malam Ahmad Matane, shine ya shelantawa manema labaru cewar bakin labarin ya faru ne da asubancin ranar Laraba a ƙauyen Baare dake ƙarƙashin karamar hukumar Mashegu. Rahotan yace a take aka bindige mutane a kalla su 16 yayin da wasu da dama sun kareraye suna kwanciyar jinya. Kamar yadda rahotan ya riske mu waɗanda ake zargin sun zo ne da asubahi ana Sallah kusan su 200…

Cigaba Da Karantawa

Da Dumi-Dumi: An Bindige Kwamishina A Jihar Katsina

Rahoton dake shigo mana yanzu daga Jihar Katsina na bayyana cewar wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun yi wa kwamishinan Kimiyya da Fasaha na jihar Katsina, Dokta Rabe Nasir kisar glla. An ruwaito cewa an bindige shi ne a gidansa da ke Fatima Shema Estate da ke birnin Katsina da yammacin nan. Wata majiya wacce ta tabbatar da lamarin ta ce: “An bindige marigayi Nasir ne bayan sallar La’asar a gidansa da ke nan Fatima Shema Estate.” Marigayi Dr Rabe Nasir mashawarci ne na musamman ga Gwamna…

Cigaba Da Karantawa

Buhari Ya Yi Fatali Da Kudurin Zaben ‘Yar Tinke

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban kasa Buhari yayi watsi da kudirin Zaben ‘Yar Tinƙe da sauran kwaskwariman da akayiwa dokokin zaben kasar nan. Yace kowace Jam’iyyar siyasa tanada damar yin kalar zaben cikin gida din da take so. Idan ba a manta ba a ranar 10 ga watan Nuwambar wannan shekara ne Majalisar kasar mu ta sanyawa dokar gyara da kwaskwariman kundin tsarin dokokin zaben kasar nan hannu wanda ta mikawa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu domin a fara aiki da sabon tsarin a…

Cigaba Da Karantawa

Hanyoyin Sadarwar Zamani Na Da Rawar Takawa Wajen Bunkasa Kasa – CITAD

Cibiyar bunƙasa ilimin kimiyya da cigaban zamani CITAD ta yi kira da babbar murya ga gwamnatin tarayya da bada gudunmawar da ta dace wajen inganta hanyoyin sadarwar zamani domin cigaban kasa. Babban Darakta na Cibiyar Yunus Zakari Ya’u ya bayyana hakan lokacin da yake gabatar da jawabi a taron manema labarai da cibiyar ta kira a Kaduna. Ya ƙara da cewar kashi na 16 na taron haɓaka tsarin amfani da Internet na ƙasa da ƙasa da aka gudanar a kasar Poland ya tabbatar da tasirin da ilimin kimiyyar hanyoyin sadarwar…

Cigaba Da Karantawa

Da Dumi-Dumi: Buhari Ya Dira Birnin Ikko

Rahotanni daga fadar Shugaban ƙasa birnin tarayya Abuja na bayyana cewar mai girma Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa Legas babban birnin kasuwanci na Najeriya domin ƙaddamar da wasu ayyuka a yau. Rahotanni na cewa cikin ayyukan da zai ƙaddamar har da wasu sabbin jiragen ruwa na yaƙi a tashar ruwa ta sojin ruwan ƙasar da ke Victoria Island. Tuni hukumar kiyaye haɗura ta jihar Legas LASTMA ta ba jama’a shawara da su kiyayi bi ta titin Ahmadu Bello sakamakon ziyarar shugaban. Tuni sojoji da ƴan sanda da jami’an DSS…

Cigaba Da Karantawa

Karshen Shekara: Za A Samu Ambaliyar Matalauta A Najeriya – Ministar Kudi

Gwamnatin Tarayya a ranar Talata ta ce akwai yiwuwar yawan talakawa ya karu zuwa miliyan 109 nan da karshen shekarar 2022. Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-tsare, Zainab Ahmed, wacce ta bayyana hakan ta ce sabbin mutum miliyan 11 na iya fada wa kangin talauci a cikin shekarar sakamakon annobar COVID-19. Ta yi wadannan kalaman ne a Abuja, a ci gaba da taron da ake yi kan annobar COVID-19 mai taken ‘Fadan karshe wajen yaki, tare da murmurewa daga annobar COVID-19’. Ministar, wacce ta sami wakilcin Darakta Janar na Ofishin Kasafin…

Cigaba Da Karantawa

Buhari Ya Ci Amanar ‘Yan Najeriya – Sheikh Bello Yabo

Labarin dake shigo mana daga Jihar Sokoto na bayyana cewar a wajen wani sabon karatu da Sheikh Bello Yabo ya yi, ya yi Allah-wadai da gwamnatin Muhammadu Buhari, yace mulkinsa bai tsinana komai ba illa fitina da wahala ga Talaka. Legit.ng Hausa ta samu faifen wannan karatu da Shehin Malamin ya gabatar, inda ya yi wa gwamnatin tarayya Allah ya isa, yace an zalunce al’umma. “Muhimmancin mulki shi ne ya kare rayuwa, dukiya da mutuncin talakawa, duk mulkin da ya kasa yin wannan, ai sai mu ce gara babu da…

Cigaba Da Karantawa

Kano: Ban Da Abokin Gaba A Siyasa – Ganduje

Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar Gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya yi magana a kan sabaninsa da bangaren Malam Ibrahim Shekarau a rikicinsu na cikin gidan APC. Da aka yi hira da shi a Gidan Rediyon RFI Hausa, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa sam ba wani abin mamaki ba ne don an samu rashin jituwa a siyasa. A cewar Dr. Abdullahi Ganduje, uwar jam’iyya ta na kan kokarin sasanta wannan rikicin cikin gidan. “Ana nan ana sasantawa, kamar yadda ka sani, uwar jam’iyyar ta shiga. Kuma samun…

Cigaba Da Karantawa

Zamfara: An Yanke Shawarar Sulhu Da Shugaban ‘Yan Bindiga Turji

Rahotanni daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Sakamakon hare-haren wuce gona da iri a yankin Shinkafi a jihar Zamfara, musamman kan matafiya dake kan hanyar da ta hada Gusau zuwa Sabon Birni, a jihar Sokoto, an aika da sabon jakada domin ganawa da kasurgumin dan bindiga, Turji. A farkon watan Nuwamba, Turji ya yi watsi da tawagar Shinkafi ta neman tattaunawa, wadanda rahotanni suka ce sun je wurinsa domin neman zaman lafiya, duba da yadda kashe kashe suka kazamce a yankin. Wani mazaunin garin Shinkafi, Alhaji Ali…

Cigaba Da Karantawa

2023: Mika Ragamar Mulki Hannun Inyamurai Ne Mafita – Austin Braimoh

Labarin dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar yayin da aka fara yakin neman zaben 2023, shahararren ‘dan gwagwarmayar nan, Austin Braimoh ya ba jigon APC, Asiwaju Bola Tinubu shawara akan makomar babban zaɓe dake tafe. Austin Braimoh yana cewa ya kamata Asiwaju Bola Tinubu ya hakura da burin zama shugaban Najeriya, ya ba ‘Yan Ibo dama, suma jarraba tasu sa’ar a gani. Da yake magana da ‘yan jarida a ranar Laraba, 8 ga watan Disamba, 2021 a birnin tarayya Abuja, Braimoh ya yi kira ga manyan…

Cigaba Da Karantawa

Matsalar Tsaro: Buhari Zai Wadata Jami’an Tsaro Da Manyan Makamai

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya kara jaddada kudirin gwamnatinsa na wadata mayakan kasar da isassu kuma ingatattun kayan aiki don ci gaba da tunkarar matsalolin tsaro dake addabar kasar a sassa daban-daban. Shugaba Buhari wanda ya bayyana wannan kudurin yayin da yake bude babban taron manyan hafsoshin sojin kasar da kuma manyan kwamandojin sojojin daga ko’ina cikin kasar. Yace tsaro na daya daga cikin manyan manufofin gwamnatinsa don haka za ayi duk wani abu mai yiwuwa don inganta sashin. Shugaban wanda Babban…

Cigaba Da Karantawa