Sokoto: An Tabbatar Da Mutuwar Fasinja 35 A Motar Da ‘Yan Bindiga Suka Kona

Rahotan dake shigo mana yanzu haka daga jihar Sokoto na bayyana cewa ‘yan bindiga sun kona wata motar fasinja dauke da mutum 42. Rahotannin sun ce fasinjojin sun fito ne daga karamar hukumar Sabon Birni da ke jihar domin yin ƙaura zuwa wasu yankunan Najeriya, saboda ta’azzarar ayyukan ‘yan bindiga a inda suke. Wasu shaidu sun cewa BBC lamarin ya faru ne da misalin karfe 9 na safiyar ranar Litinin. “Motar ɗauke da fasinjojin ta tashi daga Sabon Birni, ta yi tafiyar da bai fi kilomita shida ba zuwa kauyen…

Cigaba Da Karantawa

Da Dumi-Dumi: An Hallaka Kwamandan ISWAP Abu Sufyan A Tafkin Chadi

Gamayyar harin sama da sojojin Nijeriya su ka kai ya hallaka wani babban kwamandan ISWAP, Abu Sufyan da mayaƙan sa da dama a yankin Tafkin Chadi a Jihar Borno. Jaridar PRNigeria ta jiyo cewa Rundunar Sojin Sama, NAF, a wani ɓangare na ‘Operation Hadin Kai’ ce ta kai hare-hare a kan gurin ajiye makaman ISWAP ɗin da ke Kusuma da Sigir a ƙaramar hukumar Marte a Borno, a ranar Lahadi. Rundunar ta kai harin ne bayan ta samu bayanan sirri cewa akwai ƴan ta’addan a yankin, inda su ke haɗuwa…

Cigaba Da Karantawa

Tsautsayi: Dan Tauri Ya Farke Cikinsa Da Wuka A Kano

Wani ɗan tauri mai suna Nadabo Alhassan ya gamu da ɓacin rana, bayan da ya farke cikinsa da wuƙa a yayin bikin ƴan tauri. An ruwaito cewa lamarin ya faru ne a garin Gani, Ƙaramar Hukumar Sumaila a Jihar Kano a ranar Lahadi. Tun da farko dai, a yayin bikin na ƴan tauri, Alhassan, ɗan shekara 40, ya zo ya yi kirari, ya yi kirari, sai kuwa ya riƙa daɓawa kan sa wuƙa a sassan jikinsa. An rawaito cewa, a yayin da Alhassan ya rufe idonsa yana ta gabzawa kansa…

Cigaba Da Karantawa

Bauchi: Mun Janye Amincewa Ga Kwamishinan Ilimi Akan Rashin Da’a – Majalisa

Daga Adamu Shehu Bauchi Majalisar dokokin Jihar Bauchi ta janye amincewar data yi ma Kwamishinan Ilimi na Jihar Dr. Aliyu Usman Tilde a bisa zargin rashin da’a da yayi ma yan’majalisar dokoki a lokacin zaman kariyar kasafin kudin ma’aikatar Ilimi ta jihar. Majalisar ta dauki matakin ne, a zaman ta na gaggawa a ranar litinin inda tace suna da hurumin amincewa ko kuma akasin haka, tsarin mulki ya basu wan nan damar biyo bayan kudirin da shugaban kwamitin Ilimi na majalisar Babayo Mohammed dannmajalisar Mai wakiltar Hardawa, ya gabatar Kuma…

Cigaba Da Karantawa

Adamawa: Majalisa Ta Amince A Nada Kwamitin Riko A Kananan Hukumomi

Majalisar dokokin Jihar Adamawa ta amincewa Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri da ya nada kwamitin rikon kwaryar shugabannin kananan hukumomi ashirin da daya dake fadin jihar ta Adamawa. Hakan ya biyo bayan cikar wa’adin zababbun shugabannin kananan hukumomin bayan da hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar ta kasa gudanar da zaben shugabannin kananan hukumomin, wanda ta kudiri aniyar gudanarwa a cikin wannan wata, wanda daga bisani ta ɗaga zaben zuwa illah masha Allah. Ranar takwas ga watan Disamba na wannan shekara wato wa’adin shugabannin kananan hukumomin zai zo karshen kamar…

Cigaba Da Karantawa

Adamawa: An Haramta Ayyukan Mafarauta

Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, a ranar Litinin ya haramtawa kungiyar kwararrun mafarauta ta Najeriya gudanar da ayyukanta a fadin kananan hukumomin jihar 21, biyo bayan rahotannin amfani da karfin iko. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai taken ‘Gwamnatin Jihar Adamawa ta haramtawa kungiyar mafarauta yin aikinta’ mai dauke da sa hannun Sakataren Yada Labarai na Gwamnan, Humwashi Wonosikou. Gwamnan ya bayyana cewa an samu rahotannin cin zarafi da rashin kula da cibiyoyin gargajiya da hukumomin tsaro da mafarauta ke yi, musamman a kananan hukumomi biyar da…

Cigaba Da Karantawa

Osinbajo Ya Ziyarci Dubai Kwana Biyu Da Dawowar Buhari

Rahotanni daga babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya tashi daga Abuja inda ya nufi birnin Dubai, hadaddiyar daular Larabawa UAE rabar Litinin. A cewar mai magana da yawun Osinbajo, Laolu Akande, mai gidansa ya tafi Dubai ne halartan taron kungiyar iskar Gas na girki. Ya bayyana hakane a jawabin da ya fitar ranar Litinin a birnin tarayya Abuja. A cewarsa, Osinbajo zai gabatar da jawabi a wannan taro da za’a kwashe kusan mako guda ana yi kuma manyan Ministocin kasashen duniya zasu…

Cigaba Da Karantawa

Kano: Adadin Daliban Islamiyya Da Ruwa Ya Ci Ya Doshi 50

Rahotanni dake shigo mana daga Karamar hukumar Ɓagwai ta jihar Kano na bayyana cewar an gano gawawwakin mutane 13 da ba a san inda suke ba tun bayan hadarin jirgin ruwan da ya auku a wani kauye a garin Bagwai, jihar Kano. An ruwaito cewa an gano gawarwarkin mutane 13 da suke nutse a hadarin ruwa. Hakan ya na nufin adadin mutanen da ruwan ya ci a mummunan hadarin da aka yi ya kai 42. Ana sa ran a safiyar ranar Talata ayi jana’izar wadanda suka riga mu gidan gaskiya…

Cigaba Da Karantawa

Cancantar Takara: Kotu Ta Ayyana Ranar Yanke Hukunci Kan Atiku

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Babbar kotun tarayya ta sa ranar 21 ga watan Fabrairu, 2022 domin yanke hukunci kan ko Atiku Abubakar, na da damar neman kujerar shugabancin kasa. Alkalin kotun, mai sharia Inyang Ekwo, shine ya sanar da ranar bayan kammala sauraron kowane bangare. A kara mai lamba FHC/ABJ/CS/177/2019, wata kungiya ta Nahiyar Afirka, (EMA) ta gurfanar da Atiku, jam’iyyar PDP, hukumar zaɓe INEC, da Antoni Janar na kasa inda ta kalubalanci cewa Atiku ba shi da damar neman kujerar shugaban ƙasar Najeriya kasancewar ba’a…

Cigaba Da Karantawa

Tabarbarewar Tsaro: A Yi Gaggawar Sallamar Monguno – Matasan Arewa

Gamayyar Kungiyoyin Matasan arewa sun yi kira da babbar murya ga gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaban kasa Buhari da ta sauya salon tsarin tsaro tare da yin gaggawar sallamar mai bayar da shawara kan tsaron kasa, Manjo Janar Babagana Monguno kan yawaitar kashe-kashe da farmakin da ake ta kai wa yankunan arewacin kasar nan. Kungiyar wacce ta hada kungiyoyin matasan arewa karkashin uwar kungiya mai suna Northern Ethnic Group Assembly (NEYGA), a wata takarda da ta sa hannu a kai ranar Lahadi ta hannun kakakin ta, Ibrahim Dan-Musa, ta ce…

Cigaba Da Karantawa