Adamawa: An Roki Gwamnatin Buhari Ta Janye Kudirin Cire Tallafin Fetur

An kira yi gwamnatin tarayya da ta yiwa Allah da manzonsa ta janye kudirinta na cire tallafin man fetur da tasa aniyar yi a shekara mai zuwa. Wasu mazauna jihar Adamawa ne suka yi wannan kiran a zantawarsu da wakilinmu a Yola fadar gwamnatin jihar ta Adamawa. Abdulrahman Musa mazaunin jihar Adamawa yace a gaskiya karin farashin mai din bazai haifar da ɗa mai ido ba, sai dai zai jefa talaka cikin kuncin rayuwa da kuma haifar da hàuhawan farashin kayayyaki a kasuwanni, harma dana sifiri. Abdulrahman yace shugaban kasa…

Cigaba Da Karantawa

Ilimi Ne Babban Jagora A Aikin Agaji – Shugaban ‘Yan Agajin Fityanul Islam

Daga Muhammad Sani Yusuf Nassarawa An bukaci ‘Yan Agajin Munazzamutul FItyanul Islam Su Kara Himma akan Aikinsu na Taimakawa Addini ta Kowacce Fuska ta Hanyar Samun Ilimin Aikin Agajin Wanda Shine Jagora. Wannan Kira ya Fitone daga Bakin Babban Kwamandan ‘Yan Agajin Babban Birnin Tarayya Abuja, Alhaji Yakubu Abubakar a Lokacin da Kungiyar ta Shirya Taron da ta Saba Gudanarwa na Karshen Shekara. Taron Wanda ya Gudana a Unguwar Daki Biyu dake Jabi Abuja ya Samu Halartar Shugabannin ‘Yan Agaji Daga Dukkan Kananan Hukumomin Babban Birnin na Abuja. Tunda Farko…

Cigaba Da Karantawa

2023: El Rufa’i Ya Roki Jama’a Su Goyi Bayan Wanda Ya Dagawa Hannu

Gwamna Malam Nasir El-Rufai ya yi kira ga jama’ar jihar Kaduna kwansu da kwarkwata su yarda dashi su marawa duk ‘dan takarar da ya dagawa hannu a 2023, domin yasan shi ya fi cancanta kuma yasan zai zama Gwarzon Gwamna. Anga Gwamnan a wani bidiyo cikin harshen turanci yana cewa “Wasu suna cewa wai abunda mukayi a yanzu ba za yiwu a maida hannun agogo baya ba, to ba haka bane, muddin akayi rashin sa’a wani talasurun dan PDP ya zama Gwamna a jihar Kaduna zai iya maida hannun agogo…

Cigaba Da Karantawa

Bauchi: Aljannu Ke Haddasa Haddura A Titunan Jihar – Hukumar Kiyaye Hadura

Rahotanni daga Jihar Bauchi na bayyana cewar Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) dake Jihar Yusuf Abdullahi, ya koka kan yadda aka samun yawaitar hadurran mota a jihar a cikin watan Nuwamba na wannan shekarar. Ya ce a cikin watan da ya gabata, mutane a kalla 35 ne suka mutu a wasu hadurran mota a fadin jihar, yayin da dama suka samu muguwar naƙasa. Kwamandan ya bayyana damuwarsa kan lamarin inda ya bayyana cewa: “Shaidanun aljanu sun mamaye hanyoyin Bauchi a ‘yan kwanakin nan.” Kwamanda Abdullahi, wanda ke jawabi…

Cigaba Da Karantawa

Borno: Hukumar Kula Da Filayen Jiragen Sama Ta Karyata Labarin Tashin Bam

Rahotanni daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar Hukumar kula da filayen tashi da saukar jiragen sama ta Najeriya (FAAN) ta musanta rahotannin tashin bam a filin jirgin saman Maiduguri. Wata sanarwa fa kakakin Hukumar FAAN, Henrietta Yakubu ya fitar, ta ce: “Ba a kai wa filin jirgin saman hari ba, kuma ba a kai hari ko wanne bangarensa ba.” “Game da rahoton da aka samu ta yanar gizo da ke cewa bam ya tashi a filin jirgi na Maiduguri da ake zargin mayakan Boko Haram ne suka…

Cigaba Da Karantawa

Dukiyar Attajiri Dangote Ta Sake Hawa Sama

Labarin dake shigo mana yanzu haka na bayyana cewar Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Aliko Dangote, yana kan ganiyar sake lashe wannan mataki a shekarar, matsayin da ya lashe tun a shekarar 2014 wanda kuma zai zarce a karo na biyu a jere a sashinsa na siminti. Tashin farashin hannun jarin kamfanin simintin Dangote da na man fetur da taki sun taimaka wajen bunkasa arzikinsa da ya kai dala biliyan 2.3 a bana zuwa dala biliyan 20.1 a ranar 3 ga watan Disamba, wanda ya kasance mafi…

Cigaba Da Karantawa

Matasan Kudancin Kaduna Sun Lashi Takobin Ganin Bayan ‘Yan Bindiga

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Matasan Kudancin Jihar sun sha alwashin cewa ba zasu sake naɗe hannu suna kallo yan bindiga na kai hari yankunasu, suna sace mutane ba. Matasan sun gargaɗi yan bindigan ne karkashin kungiyar mutanen kudancin Kaduna (SOKAPU) bangaren matasa, a wata sanarwa da suka fitar cikin fushi. A sanarwar da shugaban matasan SOKAPU na ƙasa, Kwamaret John Isaac, ya fitar, Matasan sun yi kira ga mutanen dake zaune a yankin kudancin Kaduna su tashi tsaye su daina jiran kowa, su kare kansu daga sharrin…

Cigaba Da Karantawa

Layukan Waya Miliyan 70 Basu Da Rajistar Ajiyar Banki A Najeriya

Rahotanni dake shigo mana daga Ikko Babban Birnin Jihar Legas na bayyana cewar an nuna damuwar cewa aƙalla layukan waya miliyan 70 ne ba a haɗa su da lambar ajiyar banki ba, wato BVN. Shugaban Kamfanin Hada-hadar Zamani na eTranzact, Niyi Toluwalope ne ya bayyana haka a Lagos. Toluwalope ya yi wannan iƙirarin a lokacin da ya ke jawabi a Taron Shekara-shekara na Ƙungiyar ‘Yan Jarida Masu Aika Rahotannin Hada-hadar Kasuwanci ta Najeriya (CAMCAN), taro na 24 da aka shirya a Legas. Ya ce mutum miliyan 150 a cikin mutum…

Cigaba Da Karantawa