Kotu Ta Bada Umarnin Barin Kanu Ya Wataya

Wata babbar kotun tarayya a Abuja ta ba hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), umarni da ta tabbatar da shugaban ƙungiyar ƴan a-waren Biafra Nnamdi Kanu ya samu ‘cikakkiyar walwala’ yayin da yake tsare a hannunsu. Wannan umurni ya biyo bayan ƙorafin da lauyoyinsa suka yi na cewa wanda suke karewa an hana shi walwala ko canza kaya da yin addininsa ba ya iya wa a yayin da yake tsare. Sauraren shari’ar gaggawar da aka yi ya zo bayan tsegwamin da lauyoyinsa suka yi cewa ɗage shari’ar da aka yi…

Cigaba Da Karantawa

Takardun Bogi: Gwamnatin El Rufa’i Za Ta Sallami Malaman Makaranta 233

Labarin dake shigo mana yanzu daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Nasir El-Rufa’i ta sanar da cewa za ta sallami Malaman makaranta 233 bisa gabatar da takardun bogi. Shugaban hukumar ilmin kananan makarantun jihar SUBEB, Tijjani Abdullahi, ya sanar da hakan ranar Alhamis, 2 ga Disamba, a hira da manema labarai. “Kawo yanzu, an tantance takardu 450 ta hanyar tuntubar makarantun da suka bada. Makarantu 9 cikin 13 sun bamu amsa.” “Amsoshin da muka samu sun nuna cewa Malamai 233 sun gabatar da takardun bogi.…

Cigaba Da Karantawa

Kano: Daya Daga Cikin Malaman Da Suka Yi Mukabala Da AbdulJabbar Ya Rasu

Malam Mas’ud Mas’ud Hotoro, ɗaya da ga cikin malaman da su ka jagoranci mukabala da malam Abduljabbar Nasiru Kabara ya rasu. Jaridar Kano Focus ta ruwaito cewa Malam Mas’ud ya rasu ne a daren jiya Laraba, sakamakon haɗarin mota a kan hanyar Kaduna zuwa Zaria. Idan za a iya tunawa malamin na cikin malamai huɗu da su ka yi Muƙabala da Abduljabbar a kwanakin baya. Malamin shi ne wanda ya wakilci ɓangaren Ƙadiriyya ya yin zaman muƙabalar. Rahotanni sun baiyana cewa za a yi jana’aizar malamin a yau Alhamis a…

Cigaba Da Karantawa

Raina Yana Baci Idan Naji Ana Zagin ‘Yan Fim – Umma Shehu

Fitacciyar Jaruma a Masana’antar shirya finafinan Hausa ta kannywwod ta bayyana cewar duk lokacin da ta ji a nan zagin ‘yan fim tan jin rashin dadi a zuciyarta. Jaruma Umma Shehu wacce aka fi sani da Zuli a cikin shiri mai dogon zango na Gidan Badamasi ita ce ta bayyana Hakan a tattaunawar su da Dimokaradiyya, dangane da irin kallon da a ke yi wa ‘yan fim a cikin al’umma. Zuli ta ce “Magana ta Allah ba na jin dadi sam idan na ji a na zagin, sai dai Kuma…

Cigaba Da Karantawa

Borno: ISWAP Ta Sace Manyan Ma’aikatan Gwamnati

Rahotanni daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar wasu Miyagun ƴan ta’addan kungiyar Islamic State in West Africa, ISWAP, sun sace manyan ma’aikatan gwamnatin jihar Borno a ƙalla su biyar. An sace ma’aikatan ne a ranar Laraba, a lokacin da suka saka ido a kan aikin ginin titin Chibok-Damboa. Lamarin ya faru ne kusa da Wovi, a wani ƙauye da ke ƙaramar hukumar Chibok. Wata majiya ta shaida cewa ɗaya daga cikin ma’aikatan, direba, ya tsira daga harin. Wani babban jami’i ya tabbatar da afkuwar lamarin yana cewa:…

Cigaba Da Karantawa

Gwamnatin Zamfara Ta Fara Safarar Shanu Daga Waje

Labarin dake shigo daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Gwamnatin jihar ta kammala shirye-shiryen shigo da awaki da shanu daga kasashen Afirka ta Kudu da Norway a wani mataki na bunkasa matsugunan RUGA a jihar. Gwamna Bello Matawalle ne ya sanar da hakan a garin Kaura-namoda yayin taron horas da masu ruwa da tsaki da kuma jajircewa kan ci gaban shirin RUGA da Rahusa Ventures ta shirya wanda Sanata Sahabi Ya’u Kaura ya dauki nauyi. Gwamnan wanda ya samu wakilcin kwamishinan gandun daji da kiwo Dr. Ibrahim…

Cigaba Da Karantawa

Cimar Doya Ta Gagari Talaka A Jihar Kaduna

Rahotannin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar farashin doya ya yi tashin gwauron zabo lamarin da a yanzu sayen doya ke neman gagarar talaka. Wakilimu da ya leka babbar kasuwar ‘yan Doya dake Kaduna ya samu zantawa da wasu daga cikin Dillalan Doyar, inda suka bayyana yadda farashin ya yi mummunan tashi sama a cikin shekara guda. Malam Bala mai Doya ɗaya ne daga cikin Dillalan Doyar dake kasuwar, ya bayyana cewar a halin yanzu kwaryar Doya wadda a baya suke saye akan farashin kudi naira dubu…

Cigaba Da Karantawa

An Kafa Kwamitin Gano Masu Sayar Da Kadarorin Da Aka Kwace Hannun Barayin Gwamnati

Ministan Shari’a Abubakar Malami ya kafa Kwamitin Bankaɗo Waɗanda Su Ka Fara Sayar Da Kadarorin Gwamnatin Tarayya, waɗanda aka ƙwato daga hannun ɓarayin gwamnati. Kafa kwamitin ya biyo bayan ɓullar wasu rahotanni a jaridu da su ka ce wasu a cikin Ma’aikatar Harkokin Shari’a sun fara sayar da kadarorin da gwamnatin ta ƙwato a ɓoye ta ƙarƙashin ƙasa. Cikin wata takardar da Kakakin Malami ya raba wa manema labarai a ranar Talata, ya ce, “Ministan Shari’a Abubakar Malami bai bada iznin a fara sayar da kadarorin ba. Kuma idan ma…

Cigaba Da Karantawa