Ba Mu Yarda Da Rage Kwanakin Aiki Ga Ma’aikata Ba – CAN Ga El Rufa’i

Kungiyar Kiristocin Najeriya reshen jihar Kaduna, CAN, ta yi watsi da matakin gwamnan jihar Malam Nasiru El-Rufa’i na rage kwanakin aiki ga ma’aikatan gwamnati daga biyar zuwa hudu. A ranar Litinin ne gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da wannan mataki, wanda ta ce zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Disambar shekarar da muke ciki. A wata sanarwa da shugaban kungiyar Rabaran Joeshep Hayaf ya aike wa manema labarai a ranar Talata, CAN ta ce kada ma’aikatan gwamnati su yadda da wannan batu, domin kada a yi musu sakiyar-da-ba-ruwa…

Cigaba Da Karantawa

Kotu Ta Rushe Shugabancin APC Bangaren Ganduje

Wata kotun tarayya dake Abuja, a ƙarƙashin jagorancin Hamza Muazu ta rushe zaɓen shugabancin jam’iyar APC da tsagin gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya gudanar. Haka kuma mai shari’ar ya tabbatar da zaɓen da tsagin tshohon gwamnan Kano Ibrahim shekarau ya gudanar. An ruwaito cewar mai shari’ar ya ce zaɓen na ɓangaren Shekarau, wanda Haruna Ɗanzago ya lashe, ya samu sanya hannun mutum 7 daga cikin waɗanda uwar jam’iyyar ta turo jihar Kano domin gudanar da zaɓen. Alkalin kotun, Mai shari’a Hamza Muazu yace ya amince da zaben da bangaren Sanata…

Cigaba Da Karantawa

Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Umarci Ganduje Ya Biya Sanusi Miliyan 10

Wata babbar kotu a Abuja ta yanke hukunci a biya Sarkin Kano na 14, Muhammad Sanusi II tarar Naira Miliyan 10 saboda aika shi da akayi daga jihar Kano zuwa wata jihar aka killace shi bayan Gwamnati ta sauke shi daga Sarautar Sarkin Kano, Justice Anwuli Chikere, ne ya yanke hukuncin a yau Talata inda yace dokar masarautar Kano 2019 da akayi amfani da ita wajen killace Sarkin ta ci karo da kundin tsarin mulki na Nigeria 1999. A cewar Alkali Chikere, kundin tsarin mulkin Nigeria shine gaba da komi…

Cigaba Da Karantawa

Ma’aikata Na Turereniyar Yin Rigakafin Korona Kafin Cikar Wa’adi

Domin tabbatar da an yi wa ma’aikata rigakafin korona kafin cikar wa’adin gwamnatin Najeriya, rahotanni sun ce ma’aikata na rige-rigen yin rigakafi musamman a hukumomi da ma’aikatun gwamnati a Abuja. A ranar 1 ga watan Disamba gwamnatin Najeriya ta ce za a hana wa ma’aikatan da ba su yi rigakafin korona ba zuwa wurin aiki. Wannan ya sa ma’aikata da dama ke rige-rigen domin yin rigakafin korona kafin cikar wa’adin na gwamnati. Hukumomin Lafiya a Najeriya sun ce sun fara bi ofis zuwa ofis domin yi wa ma’aikatan gwamnati rigakafi.…

Cigaba Da Karantawa

Da Dumi-Dumi: Tambuwal Ya Haramta Aikin ‘Yan Banga A Sokoto

Rahotanni daga Jihar Sokoto na bayyana cewar Gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ta haramta ayyukan ƴan sa-kai a faɗin jihar tare da ƙarfafa aikin ƴan banga. Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal wanda ya sanar da ɗaukar matakin a ranar Litinin a wani taron tsaro na jihar, ya ce sha’anin yan sa-kai shi ya ƙara haifar da matsala a Zamfara da jihohin da ke maƙwabtaka da ita. Ya ce suna yin gaban kansu ba tare da bin doka da oda ba. “Ba za mu ci gaba da kyalewa…

Cigaba Da Karantawa

Messi Ya Lashe Kyautar Gwarzon Dan Kwallo Na Duniya

Dan kwallon tawagar Argentina mai taka leda a Paris St Germain, Lionel Messi ya lashe kyautar Ballon d’Or ta bana, karo na bakwai kenan a tarihi. Bayan da ya bar Barcelona kan fara kakar bana, Lionel Messi ya kara lashe babbar kyautar tamaula a duniya ta kashin kansa, duk da Barcelona na fuskantar kalubale a kakar nan. Messi wanda ya karya tarihin yawan kwallon da Pele ya ci a kungiya daya – dan kasar Argentina ya ci kwallo a kalla 20 a kaka 13 a jere a Turai, shine kan…

Cigaba Da Karantawa

Da Dumi-Dumi: Uwar Jam’iyyar APC Ta Dare Gida Biyu

Rahotannin dake shigo mana daga Abuja babban birnin tarayya na bayyana cewar rikicin jam’iyyar APC mai mulki ya bude wani sabon babi ranar Litinin yayin da matasa suka sanar da rushe kwamitin rikon kwarya na Gwamna Buni. Matasan karkashin kungiyar Progressive Youth Movement (PYM), sun tsaida ranar 26 ga watan Fabrairu a matsayin ranar gangamin taron APC na ƙasa. Da yake jawabi, sabon shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar APC, Prince Mustapha Audu, wanda ɗa ne ga tsohon gwamnan Kogi, Abubakar Audu, ya bayyana cewa sun fito ne domin ceto…

Cigaba Da Karantawa

Dattawan Arewa Sun Gargadi Buhari Kan Sakin Nnamdi Kanu

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Kungiyar Dattawan Arewa (NEF), a ranar Litinin, 29 ga watan Nuwamba, ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi watsi da bukatar wasu fitattun shugabannin Igbo, inda suka bukaci a sako Nnamdi Kanu, shugaban ‘yan awaren IPOB. Kungiyar ta bayyana cewa babu wani dalili na aminci, ingantacce ko kuma sanin makamar amincewa da bukatar, kuma ta shawarci shugaban kasa da kada ya jinkirta bayyana cewa za a bar tsarin shari’a yayi aikinsa akan Kanu. Dattawan sun bayyana haka ne…

Cigaba Da Karantawa

Babu Adalci Musulmi Ya Nemi Shugabancin Kasa Bayan Buhari – Kungiyar Kiristoci

Rahotanni daga birnin Ikko na Jihar Legas na bayyana cewar Kungiyar Kirista ta Pentecostal Fellowship of Nigeria, PFN, ta bukaci cewa kirista ne da dace ya gaji Shugaba Muhammadu Buhari a 2023, tana mai cewa rashin adalci ne wani musulmi ya sake zama shugaba. Shugaban kungiyar ta PFN na kasa, Bishop Francis Wale-Oke, ne ya yi wannan kiran a karshen taron kungiyar da aka saba yi duk bayan wata hudu, da wannan karon aka yi a Legas. “Ba mu tunanin ya dace wani musulmi ya sake zama shugaban kasa a…

Cigaba Da Karantawa

Cire Tallafin Mai Zai Jefa ‘Yan Najeriya A Wagegen Rami Gaba Dubu – Mahadi

An bayyana cewar babu shakka ko kokwanto cire tallafin fetur da gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Buhari ta yi zai jefa ‘yan Najeriya cikin wani mawuyacin hali na tsadar rayuwa inda komai a kasar zai yi tashin gwauron zabo fiye da yadda ake zato. Bayanin hakan ya fito ne daga bakin mashahurin ɗan kasuwar nan mazaunin Garin Kaduna Dr Mahadi Shehu lokacin da yake tsokaci akan cire tallafin fetur a wata ganawa da yayi da manema labarai a Kaduna. Dr Mahadi ya kara da cewar tun farko Najeriya ba…

Cigaba Da Karantawa