Ban Fahimci Aure Ba Sai Da Na Shiga Dakin Miji – Malala

Yar gwagwarmayar nan mai ikirarin kare hakkin yara mata yar kasar Pakistan, Malala Yousafzai wacce ta amarce a makon da ya gabata ta ce a baya bata fahimci aure ba sai yanzu da ta shiga ɗakin miji. Yar gwagwarmayar dai a baya ta bayyana karara ba ta goyon bayan aure. A wata hira da mujallar Vogue a watan Yuli Malala ta jaddada cewa; “Har yanzu, na kasa gane dalilin da ya sa mutane ke yin aure.” Ta cigaba da cewa “Idan kana son rayuwa tare da wani mutum, me ye…

Cigaba Da Karantawa

Bauchi: Gwamnati Za Ta Karbi Tallafin Biliyan 30 Don Kare Muhalli

Daga Adamu Shehu Bauchi Gwamnatin Jihar Bauchi zata karbo tallafin zunzurutun kudi kimanin naira Bliyan Talatin 30 daga Bankin duniya don kare muhalli daga gurbacewa a sanadiyan ambaliyan ruwa da yayi ma Jihar katutu a daminan bana da ta shige a mafi yawancin kananan hukumomin Jihar. Shugaban hukumar Kare muhalli na Jihar (BASEPA) Dr. Kabir Ibrahim ne ya shaida haka a lokacin aikin kwashe kasa da ya mamaye hanyoyi da gonaki a dalilin ambaliyan ruwan sama a Cheledi, cikin karamar hukumar Kirfi Ya ce maganan ambaliyan ruwa, ya daidaita wurare…

Cigaba Da Karantawa

Mutunta Juna Shine Maganin Rikicin Manoma Da Makiyaya – Sarkin Fulani

A cigaba da daukan matakan ganin kawo karshen takaddama dake faruwa a tsakanin manoma da makiyaya an shawarci manoma da makiyaya da su kasance masu fahintar juna da kuma mutunta juna wanda hakan zai taimaka wajen samun zaman lafiya a tsakaninsu yadda ya kamata. Sarkin fulanin Gundumar Masanawa dake karamar hukumar Kabo a jihar Kano kuma masanin Jimeta Yusuf Dan Umma ne ya bada wannan shawara a zantawarsa da manema labarai a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa. Yusuf Dan Umma yace rikici da ake samu a tsakanin makiyaya da manoma…

Cigaba Da Karantawa

Ta Kashe Mijinta Bayan Ya Kama Ta Da Kwarto

Ana zargin wata mata da caka wa mijinta, mai suna Abdullatif, wuka har sai da ya ce ga garinku nan bayan ya kama ta tana lalata da wani kwarto a cikin gidansu na aure. Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:00 na daren ranar Lahadi a unguwar Jattu da ke Karamar Hukumar Etsako ta Yamma a Jihar Edo. Lamarin ya faru ne lokacin da Abdullatif ya dawo ya sameta tare da mutumin a cikin dakinsu. Wata majiya mai tushe ta ce, “A baya, mijin yana…

Cigaba Da Karantawa

Babu Inda Nace Ayyana ‘Yan Bindiga Matsayin ‘Yan Ta’adda Zai Tarwatsa Najeriya – Gumi

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Shahararren malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, yace ana jingina masa maganganun da bai yi ba, ta hanyar ƙage da sharri akan ‘yan Bindiga domin kawai a ɓata mishi suna. Shehin malamin ya musanta maganar da ake jingina masa cewa wai ayyana yan bindiga a matsayin yan bindiga zai kawo karshen Najeriya. Malamin ya bayyana cewa sam bai faɗi haka ba, mutane ne ba su fahimnci abinda yake nufi ba. Gumi ya faɗi haka ne yayin da yake…

Cigaba Da Karantawa

Zan Shafe Tarihin Marafa A Siyasa – Mala Buni

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnan jihar Yobe, Mala Buni ya maida wa sanata Kabiru Marafa da zazzafar martani inda ya ce marafa karamin kwaro ne da ‘bai wuce ya murkushe shi ba.’ An ruwaito labarin korafin da Kabiru Marafa yayi kan ci gaba da shugabancin jam’iyyar APC da gwamnan Yobe Mala Buni ya ke yi cewa ya saba wa dokar kasa da ta jam’iyyar APC. Marafa ya ce babu inda dokar kasa ko kuma na jam’iyya ta ba wanda ke da mukamin gwamna ya rike kujerar…

Cigaba Da Karantawa

Gwamnatin Tarayya Ta Yi Rawar Gani Wajen Bunkasa Fannin Ilimi

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta himmatu sosai wajen ganin an samu ƙarancin yara waɗanda ba su zuwa makaranta a Najeriya. Wannan magana ta na ƙunshe ne ciki wata sanarwar da Mai Bada Shawara Kan Inganta Rayuwa Marasa Galihu, Maryam Uwais. An fitar da sanarwar ta hannun hadimar Uwais ɗin a fannin yaɗa labarai, Justice Bibiye. Uwais ta yi bayanin ne a wurin taron bayar da horo na makonni uku ga matasan da suka kammala digiri su 500 a Gombe. Matasan dai an koya masu horo ne a ƙarƙashin Shirin…

Cigaba Da Karantawa

Shari’ar Karbar Haraji: Gwamnatin Tarayya Ta Nemi Sulhu Da Gwamnoni

Rahotannin dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa mafi alheri shine a sasanta tsakanin jihohi da gwamnatin tarayya wajen kotu, kan batun shari’ar wanda ke da haƙƙin karɓar Harajin Jiki Magayi, wato ‘VAT’, wadda ake gwabzawa a kotu. Idan ba a manta ba, Babbar Kotun Tarayya ta Jihar Ribas da ke Fatakwal ce ta fara bai wa Jihar Ribas iznin cewa ita ke da ikon karɓar Harajin ‘VAT’ a Ribas, ba Gwamnatin Tarayya ba. Tun daga lokacin kuwa Gwamna Wike ya hana…

Cigaba Da Karantawa