An Damke Wanda Ya Tsokani ‘Yar Gwagwarmaya Kan Auren Malala

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya, SSS, ta kama wani mai amfani da kafar facebook, Ibrahim Sarki Abdullahi sakamakon tsokanar ƴar gwagwarmayar nan mai rajin kare haƙƙin mata, Zainab Nasir a kan ra’ayinta kan aure. Wata majiya daga hukumar ta baiyanawa jaridar DAILY NIGERIAN cewa Abdullahi na nan ya na shan tuhuma a kan yadda ya ke tsokanar mutane a kafar sadarwa. Tun a baya ne dai Zainab ta taɓa baiyana matsayinta a kan aure, in da ta ce “aure ba nasara ba ne”, batun da ya haifar da cecekuce a…

Cigaba Da Karantawa

Safarar Muggan Kwayoyi: NDLEA Ta Kama Ma’aikatan Tashar Jiragen Ruwa

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta ce tana tsare da ma’aikata 12 na tashar jirgin ruwan Apapa, dake Jihar Legas saboda yadda suke da alaka da shigo da hodar ibilis mai nauyin kilogiram 32.9 wanda darajarsa ta kai Naira biliyan 9.5. Kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, Wanda ya bayyana hakan ranar Asabar yace a ranar 13 ga watan Oktoba ne hukumar ta kama wata jirgi a tashar jirgin ruwa ta Apapa sakamakon bayanan sirri da aka samu daga abokan huldar kasa da kasa da…

Cigaba Da Karantawa

Ku Cire Kunya Ku Gaya Mini Gaskiya – Rokon El Rufa’i Ga Talakawan Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya kalubalanci jama’ar Kaduna su rika fada mashi gaskiya ko bashi shawara ba tare da tsoro ko shakkar komi ba a duk lokacinda bukatan hakan ta taso domin ta haka ne kawai shugaba ke iya gane yana tafiya akan daidai ko akasin hakan. A wani jawabi da Gwamnan yayi a wajen taron talakawa da masu ruwa da tsaki da shuwagabannin kungiyoyi na jihar Kaduna ya ce “Kar aji kunya, Ni dai nasan ba mai tsoro na tunda tsawo ma bani dashi balle karfi” Taron…

Cigaba Da Karantawa

Shan Paracetamol Ba Bisa Ka’ida Ba Na Lalata Hanta – Likita

Wata fitacciyar likita, Esther Oke ta baiyana cewa shan ƙwayoyin maganin paracetamol ba bisa ƙa’ida ba babban haɗari ne ga lafiyar ɗan-adam. Oke ta baiyana cewa ƴan Nijeriya da dama sun ɗauki tsawon shekaru su na shan paracetamol ba bisa ƙa’ida ba sakamakon jahilci. Ta yi ƙarin bayani cewa irin waɗannan magungunan masu rage raɗaɗi na ɗauke da sinadari mai ƙarfi na paracetamol wanda ya ke lalata hantar ɗan-adam idan a na shan shi ba tare da ƙa’ida ba. “Shan ƙwayoyi kamar guda 3 a maimakon 2 da wasu su…

Cigaba Da Karantawa

Shugaban Liberty Talabijin Ya Karbi Lambar Yabo Ta Zama Gagara Badau

Jaridar yanar gizo ta politics Today ta karrama Shugaban rukunin kanfanin ATAR communications, mamalakin gidan talbijin da rediyo na liberty da jaridar voice of liberty (Muryar yanci) Dr Ahmed Tijjani ramalan da lanbar yabo na Gagara Badau na shekarar 2021 saboda gudunmuwar da ya kawo a harkar yada labarai a yankin arewa da kasa baki daya. Karramawar da akayi wa dr Ahmed Tijjani Ramalan ya biyo bayan cigaban da ya kawo a yankin arewacin kasar nan da Najeriya baki daya. Mun duba yadda yake tafiyar da gidajen radio, talbijin da…

Cigaba Da Karantawa

Tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Katsina Ya Rasu

Allah Ya karbi ran tsohon Shugaban majalisar dokokin jihar Katsina Kabir Ahmad Kofa bayan fama da rashin lafiya. Kabir Ahmad Kofa ya rasu ne a daren Asabar wayewar Lahadi a wani asibiti dake a cikin birnin Katsina. Kabir Ahmad Kofa ne shugaban majalisar dokokin jihar Katsina daga shekarar 1999 zuwa 2007, daga nan ya zama dan majalisar wakilan Nijeriya a shekarar 2007 zuwa 2011 duk a jam’iyyar PDP. Bayanai sun ce za a gabatar da jana’izarsa da misalin karfe goma na safiyar Lahadin nan a masallacin GRA Katsina.

Cigaba Da Karantawa

Daukakata A Fim Daga Allah Ne – Azeema Gidan Badamasi

Jarumar Kannywood mai tashe, Hauwan Ayawan wacce aka fi sani a matsayin Azeema a cikin shiri mai dogon zango na tashar Arewa24 wato ‘Gidan Badamasi’ ta yi bayani kan yadda ta shahara a lokaci guda a masana’antar. A cikin wata hira da Daily Trust ta yi da ita, jarumar haifaffiyar jihar Kaduna ta bayyana cewa bata taɓa sanin cewa wata rana za ta shahara haka ba duk da cewar ta taso da sha’awar yin fim tun tana yarinya. Jarumar ta yi godiya ga Allah kan wannan mataki da ya kai…

Cigaba Da Karantawa

Bauchi: Kungiyar Izala Ta Horar Da Matasa Sana’ar Dogaro Da Kai

Kungiyar Jama’atu Izalatul Bid’a wa’Ikamatus Sunnah karkashin Jagorancin Sheikh Abdullahi Bala Lau ta horas da matasan yankin Arewa maso gabas sana’o’i domin du dogara da kansu. Taron bada horon ya guda ne a jihar Bauchi inda ala koyawa matasan yadda ake hada sabulu da manshafawa da man wanke gashi da sauran kayayyakin kamshi da na girki. Shugaban kungiyar Sheikh Bala Lau ya bayyana cewar burinsa ne yaga matasa suna samun dogaro da kansu domin rufawa kansu asiri. Ya kuma kara da cewar kungiyar zata cigaba da koyawa mutane sana’o’i daban…

Cigaba Da Karantawa

Siyasar Dauki Dora Ta Kare A Najeriya – Kawu Sumaila

Tsohon hadimin Shugaban Ƙasa kan harkokin majalisa, Abdurrahman Kawu- Sumaila ya baiyana cewa zamanin ƙaƙaba ƴan takara a siyasar Nijeriya ya wuce. Kawu-Sumaila ya kuma baiyana cewa ya kamata jam’iya mai mulki, APC ta ɗauki darasi a kan zaɓen gwamna na Anambra, inda ɗan takarar jam’iyar APGA, Charles Soludo ya lashe zaɓen. Kawu-Sumaila ya yi wannan kira ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Asabar. A saƙon da ya wallafa, tsohon wakilin Takai da Sumaila a majalisar wakilai ta tarayya ya ce shi bai…

Cigaba Da Karantawa

Jama’ar Gari Sun Kwaci Sarkin Noman Kano Daga Hannun ‘Yan Bindiga

Ɗaruruwan mutane ne a garin Chiromawa da ke wajen birnin Kano su ka ƙwaci wani shugabansu, Alhaji Yusuf Nadabo, mai shekara 80. Shi dai Nadabo shine mai gidan man Chiromawa Petroleum Station, sannan shine Sarkin Noman Kano. DAILY NIGERIAN HAUSA ta samu bayanan cewa su dai ƴan ta’addan, waɗanda su ka zo da muggan makamai domin yin garkuwa da Nadabo, sun dira a ofishin sa ne da ke Bakin Tasha da misalin ƙarfe 7:35, in da su ka riƙa harbi sama domin su razana jama’a. Ai kuwa harbin nan na…

Cigaba Da Karantawa

Rundunar Sojin Najeriya Ta Yi Wa Manyan Hafsoshi Ritaya

Labarin dake shigo mana daga Hedkwatar tsaro ta ƙasa na bayyana cewar Rundunar Sojojin Najeriya ta yi wa wasu Janar-janar har 12 ritaya. An yi wa waɗanda aka yi wa ritayar faretin bankwana a Cibiyar Horas da Zaratan Sojoji ta Jaji, ranar Juma’a, a Kaduna. Waɗanda aka yi wa ritayar sun haɗa da Manjo Janar shida, Burgediya Janar biyu da kuma wasu manyan hafsoshi biyu. Manjo Janar ɗin da aka yi wa ritaya ɗin sun haɗa da Lamidi Adeosun, I. Birigini, C.M Abraham, E.C.C Agundu, T.O.B Ademola, A.M Jalingo da…

Cigaba Da Karantawa