Buhari Zai Ciyo Bashin Biliyan 82 Na Sayen Ragar Gidan Sauro

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin Shugaban ƙasa Buhari zata ciyo bashin bilyan 82 don sayen ragar kariya da cizon sauro a shekarar 2022. Wannan na kunshe cikin kasafin kudin da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar gaban majalisar dokokin tarayya kwanakin baya. Sai dai anasu bangaren ‘Yan majalisar sun ce gaskiya ba zasu yarda da wannan abu ba, dole sai an sake dubawa. Majalisar dattawar Najeriya ta yi Alla-wadai da shirin da ma’aikatar kiwon lafiyan Najeriya ke yi na karban bashin $200 million (N82,070,388,916.76) a kasafin kudin…

Cigaba Da Karantawa

Zaben 2023: Gwamnonin Kudu Sun Yi Taron Gaggawa

‘Ya’yan ƙungiyar gwamnonin yankin kudu maso yamma sun gana a jihar Legas domin tattaunawa a kan batun babban zabe dake tafe da kuma lamarin tsaro. Gwamnonin sun tattauna muhimman batutuwa wanda suka shafi matsalolin yankinsu, da kuma hanyar kawo cigaba. Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, shine ya karbi bakuncin takwarorinsa a gidan gwamnati, kwanaki uku kacal bayan harin da aka gidan yari a Ibadan. Gwamnoni biyar sun samu halartar taron, wanda aka fara shi da misalin ƙarfe 4:30 na yamma kuma cikin sirri. Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, shine bai samu…

Cigaba Da Karantawa

Da Ɗumi-Ɗumi: Tsohon Ministan Noma Abba Sayyadi Ruma Ya Rasu

Labarin dake shigo mana yanzu daga Jihar Katsina na bayyana cewar, Allah ya yi wa tsohon Ministan noma Alhaji Abba Sayyadi Ruma rasuwa a birnin Landan na kasar Ingila bayan fama da gajeruwar rashin lafiya. Majiyar mu ta shaida mana cewa Alhaji Abba Sayyadi ya rasu a wata asibiti dake a birnin Landan bayan ya ziyarci asibitin domin a duba lafiyarshi. Abba Sayyadi Ruma wanda aka haifa a ranar 13 ga Watan Maris shekarar 1962 ya rike mukamin sakataren Gwamnatin jihar Katsina daga bisani ya zama Ministan Noma da kula…

Cigaba Da Karantawa

An Damke Mutum 6 Kan Batan Dan Jarida A Abuja

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Rundunar yan sanda ta kasa ta ce ta kama mutum shida bayan batan dan jaridan nan na Vanguard Tordue Salem. Kusan mako biyu kenan da dan jaridar ya yi batan dabo a Abuja, babban birnin kasar. Ranar Litinin yan jarida karkashin kungiyar NUJ sun gudanar da zanga-zanga a hedikwatar ‘yan sanda a Abuja, kan abin da suka kira ‘nuna rashin damuwa’ kan batan abokin aikinsu. Sai dai jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan Najeriya Frank Mba, ya bai wa yan…

Cigaba Da Karantawa

Tsaro: Sama Da Mutum 20,000 Sun Yi Batan Dabo A Arewa

Labarin dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce sama da mutum 20,000 ne suka yi sama ko kasa saboda rikicin da ke faruwa a arewa maso gabashin Najeriya. ICRC ta ce yakin wanda aka shafe shekara 12 ana yi ya sa an yi asarar dubban rayuka, kuma miliyoyi sun rasa matsugunansu. A wani taron masu ruwa da tsaki da take gudanarwa a Maiduguri, ICRC ta ce ta yi rijistar sama da mutum 20,000 da suka ɓata a arewa maso gabas,…

Cigaba Da Karantawa

Kaduna: Matasa Sun Kone Dillalin ‘Yan Bindiga Kurmus

Wasu matasa a yankin ƙaramar Hukumar Igabi a jihar Kaduna sun Lakadawa wani mutum Mai suna Abdullahi Mohammad Gobirawa Dukan da ya Zama ajalinsa, tare da kone gidan sa. Fusatattun matasan sun aikata hakan ne sakamakon zargin mutumin da Zama Jakadan Yan bindiga wadanda suka addabi jihar. Da yake Karin haske Kan lamarin Kwamishinan Kula da harkokin tsaro da alamuran cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya ce Matasan sun aikata hakan ne, bayan da zarginsu ya yi karfi duba da yadda aka samu wasu da aka Yi garkuwa su…

Cigaba Da Karantawa

Ni Ne Halastaccen Shugaban APC A Jihar Kano – Zago

Mutumin da ɓangaren Sanata Ibrahim Shekarau ya zaɓa a matsayin shugaban jam’iyyar APC a jihar Kano da ke Najeriya ya ce shi ne halattaccen shugaban jam’iyyar duk da kwamitin uwar jam’iyyar na sauraron korafin zaɓe ya fito fili ya ayyana Alhaji Abdullahi Abbas na ɓangaren gwamna Ganduje a matsayin shugaban jam`iyyar. Alhaji Ahmadu Haruna Zago ya shaida wa BBC cewa babu abin da ya sha musu kai da aikin kwamitin sauraron korafin zaben, saboda zaben da suka yi sahihi ne. Wannan iƙirarin dai ya ƙara fito da darewar jam`iyyar APC…

Cigaba Da Karantawa

Wasanni: Kungiyar Arsenal Ta Sayi Dan Wasa Mai Shekara 4

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta kammala dukkanin shirye shiryen ta na sayen wani yaro mai shekaru 4 mai suna Zayn Ali Salman a matsayin ɗan wasan kungiyar. Hankalin shugabannin kungiyar ta Arsenal ya kai ga yaron ne a wani wasan ƙwallon ƙafa da yayi, inda suka nemi wakilan da su amince yaron ya ziyarci birnin London. A tarihin Shahararriyar Ƙungiyar kwallon kafan Zayn Ali Salman ya kasance ɗan wasa mai ƙananan shekaru da ta taɓa saye, kuma sayen nashi ya ɗauki hankalin duniya. Kocin Kungiyar ta Arsenal Mikel Arteta…

Cigaba Da Karantawa

Borno: Malaman Makaranta Za Su Dara

Rahotanni daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar Gwamnan jihar Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi alkawarin cewa zai fara biyan naira 30,000 ga malaman makaranta a matsayin mafi ƙarancin albashi. Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da mai taimaka wa gwamnan kan yaɗa labarai Isa Gusau ya fitar ranar Talata. Sanarwar ta ce a yanzu haka wasu malaman albashinsu bai gaza naira 11,000 ba sakamakon ayyukan malaman bogi. Zulum ya fadi hakan ne a ranar Litinin a yayin da yake ƙaddamar da kwamitin hukumar ilimi a…

Cigaba Da Karantawa

Za A Fuskanci Matsananciyar Yunwa A Najeriya – Bincike

Rahoton dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar wani bincike ya nuna cewa za a fuskanci tsananin tsadar abinci a Najeriya wanda hakan zai sabbaba yunwa saboda karancin noma a yankunan kasar. Hakan na zuwa a daidai lokacin da hukumar kididdiga ta Najeriya NBS ta sanar a rahotonta na watan Satumba cewa farashin shinkafa da kwai da garri da kuma tumatur ya tashi sosai. Yanzu haka a Najeriya ana kokawa kan tsadar buhun shinkafa da ya tasarma kusan naira 30,000. Hakama rahoton na NBS ya ce farashin…

Cigaba Da Karantawa