Shugaban Turkiya Na Ziyarar Kwanaki Biyu A Najeriya

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya fara wata ziyarar kwana biyu a Najeriya, inda ake sa ran zai gana da takwaransa Shugaba Muhammadu Buhari da kuma ƙulla yarjejeniyoyi tsakanin ƙasashen biyu. Wata sanarwa da babban mataimaki na musamman kan hakar yaɗa labarai ga shugaban Najeriya, Mallam Garba Shehu ya fitar ta ce Erdogan da mai ɗakinsa Emine sun isa Najeriya ne daga Angola, kuma bayan kammala ziyarar, ana sa rai za su isa ƙasar Togo. Ta ce Najeriya na ɗaukar Turkiyya a matsayin wata babbar aminiya kuma tana yi wa…

Cigaba Da Karantawa

Buhari Ya Taya Gowon Murnar Cika Shekaru 87

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya taya tsohon shugaban kasar na soji, Janar Yakubu Gowon murnar cika shekaru 87 da haihuwa. Buhari ya ce yana wa tsohon shugaban fatan alheri da yawan shekaru masu albarka cikin koshin lafiya. A wata sanarwa da kakakin shugaba Buhari ya fitar, Malam Garba Shehu na yabawa Yakubu Gowon bisa rawar da ya taka wajen ci gaban Najeriya, da kuma gudunmawarsa wajen tabbatuwar zaman lafiya da hadin-kai. Shugaba Buhari ya ce Najeriya ba za ta taɓa mantawa da kyawawan ayyukan da Gowon ya kawo ko ya…

Cigaba Da Karantawa

Da Dumi-Dumi: Buhari Ya Sauke Shugaban Hukumar PPPRA

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin Tarayyar karkashin jagorancin Muhammadu Buhari ya sauke shugabannin hukumomin dake kula da harkokin hada-hadar man fetur na DPR da PPPRA da PEF a Najeriya. Wannan, kamar yadda muka samu na zuwa ne biyo bayan soke hukumomin uku a ɓangaren mai kamar yadda sabuwar dokar man fetur ta PIB, ta tanada. Mai karatu dai zai iya tuna cewa Shugaban kasar ya sawa sabuwar dokar hannu a watan Agusta da ya gabata. An kafa wasu sabbin hukumomi biyu da za su maye gurbinsu,…

Cigaba Da Karantawa

Bauchi: Gwamna Bala Ya Dakatar Da Shugabar Hukumar Marasa Galihu

Daga Adamu Shehu Bauchi Gwamnan Bala Mohammed ya dakatar da shugabar hukumar kula da marayu da marasa galihu na Jihar Bauchi, Hassana Arkila akan zargin al’mundahana tare da sama da fadi Sanarwar ta fito ne daga fadar gwamnatin tare da sa hannun mai bawa Gwamna shawara ta fanin yada labarai Kwamred Mukhtar Gidado, kuma aka tura ma manema labarai Gwamnan nan take ya kafa kwamiti na musamman domin binciken zarge-zargen da ake ma hukumar karkashin jagorancin ita Hasana Arkila na badakala a hukumar. Sanarwar tace gwmana Bala ya ce, dakatarwar…

Cigaba Da Karantawa

Adamawa: An Kama Mace Cikin Masu Garkuwa Da Mutane

A kokarinta na dakile dukkanin ayyukan ta’addanci a fadin jihar baki daya, rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa tana tsare da mutane uku ciki harda wata mace wadanda ake zargi da yin garkuwa da wani yaro ɗan shekaru Tara da haihuwa. Kakakin rundunan ‘yan sandan jihar Adamawa DSP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar, wanda kuma aka rabawa manema labarai a Yola. Sanarwar tace bayan kama wadanda ake zargin an kuma ceto yaron da suka yi garkuwa dashi biyo bayan samame da…

Cigaba Da Karantawa

Maulidi: Ramalan Ya Roki Musulmi Da Koyi Da Halayen Manzon Allah

Shugaban Gidajen Talabijin da Rediyo na Liberty Alhaji Ahmed Tijjani Ramalan ya yi kira ga al’ummar Musulmi da yin koyi da halayen Manzon Allah, a daidai lokacin da ake cigaba da gudanar da bikin Maulidi. Ramalan ya bayyana hakan ne a cikin sakon murnar bikin Maulidi da ya fitar, inda ya bukaci jama’ar musulmi da rungumar halayen Manzon Allah na so da taimakon juna da nuna jin kai a tsakanin al’umma. Ramalan ya ƙara da cewar hakika haihuwar Manzon Allah ya kasance alheri da nasara wadda ta game dukkanin mutane…

Cigaba Da Karantawa

Kaduna: Soji Sun Hallaka ‘Yan Bindiga Da Dama

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Jami’an tsaro sun harbe kwamandojin ‘yan bindiga 10 a Kwanan Bataru, wajen Fatika da ke karkashin karamar hukumar Giwa a jihar. Sannan har maboyar ‘yan bindigar ma ba ta tsira ba, sai da jami’an tsaron su ka banka ma ta wuta, suka fatattaki sauran ragowar ‘yan Bindigar da suka saura. Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a wata takarda sanarwa da ya fitar ranar Litinin. A cewar sa, jami’an tsaron sun…

Cigaba Da Karantawa

Zamfara: Matawalle Ya Kirkiro Sabbin Ma’aikatu

Rahotanni daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Gwamnan jihar Bello Matawalle ya tabbatar da samar da ma’aikatu 4 sannan ya zabo sababbin kwamishinoni na ma’aikatun. Ya bayyana hakan ne ta wata takarda wacce sakataren gwamnatin jihar, Kabiru Balarabe ya bayyana a Gusau ranar Litinin. A cewar Balarabe, ma’aikatun da ya kafa guda 4 su ne: 1-Ma’aikatar kula da dazuka da bunkasa kiwon dabobbi. 2- Ma’aikatar samar da dukiya da kuma samar da ayyuka. 3-Ma’aikatar yawon bude ido da kula da otal. 4-Ma’aikatar gina gidaje da bunkasa birane.…

Cigaba Da Karantawa

‘Yan Bindiga Ba Su Da Manufa Kamar Boko Haram Da IPOB – Mohammed

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan Sadarwa da Al’adu, Lai Mohammed ya ce yan bindiga da ke adabar yankin arewa maso yamma da wasu sassan arewa bata gari ne kawai, waɗanda ba su da wata manufa akan ta’addancin da suke yi. Lai Mohammed ya ce suna da banbanci da yan Boko Haram da yan kungiyar masu fafutikan kafa kasar Biafra wato IPOB, domin suna da manufofi da tuta akan ta’addancin su. A cewarsa, ‘yan bindigan bata gari ne kawai amma ba su jayayya da ikon Nigeria a…

Cigaba Da Karantawa

Bikin Maulidi: Buhari Ya Bukaci Al’umma Su Sanya Kasa Cikin Addu’a

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga al’ummar Musulmi da sauran jama’ar ƙasa baki daya da suyi amfani da ranar bikin Maulidi wajen sanya Najeriya cikin addu’a na Allah ya fitar da kasar daga matsalolin da ta ke ciki. Buhari ya bayyana hakan ne a cikin jawabin da yayi kan bikin ranar Maulidi, wanda mai bashi shawara kan harkokin yaɗa labarai Malam Garba Shehu ya fitar. Shugaban ya bukaci al’ummar musulmi da su dage wajen yin koyi da halayyar Manzon Allah SAW na yafiya da tausayi ga jama’a domin…

Cigaba Da Karantawa