Lauyoyin Nnamdi Kanu Sun Kai Buhari Kara Tarayyar Afrika

Lauyoyin jagoran ‘yan a-ware Biafra, Nnamdi Kanu, sun ce sun fara daukar matakin shari’a kan gwamnatin Najeriya da Kenya a hukumar kare hakkin dan adam ta Tarayyar Afirka, AU. Sun bukaci kasashen biyu su yi bayani dalla-dalla kan zargin tasa keyar wanda suke karewa zuwa gida ba tare da bin ka’idojin da suka dace ba. A wata sanarwa da babban lauyan Mista Kanu, Alloy Ejimako ya fitar, ya ce sun kai batun gaban AU ne saboda dukkan kasashen biyu mambobi ne na hukumar kare hakkin dan adam ta Tarayyar Afirka.…

Cigaba Da Karantawa

Rashin Lafiyar Maryam Yahaya Ya Haifar Da Surutai

Jaruma a masana’antar Hausa film Maryam Yahaya karamar yarinya ce, kafin shigarta Hausa film tana tallen kayan koli anan unguwarsu a birnin Kano, tana kuma soya awara a kofar gidansu, suna rufawa kansu asiri da iyayenta, wanda suke masu karamin karfi ne, wato talakawa abin tausayi Lokacin da aka shigar da yarinyar nan wasan hausa film tudun kirjinta bai gama girma ba, ma’ana bata gama zama cikakkiyar balagaggiya ba, da mutuncinta da komai, da farko Mahaifinta bai so ba, yaudaransa akayi aka jefa ‘yarsa wasan kwaikwayo Abokan sana’arta bayan sun…

Cigaba Da Karantawa

Kano: Majalisa Ta Bada Shawarar A Kama Rimin Gado

Majalisar dokokin Kano ta buƙaci a gaggauta kora da cafke shugaban hukumar korafe-korafe da yaƙi da rashawa na jihar da aka dakatar Muhiyi Magaji Rimin-Gado. Kamfanin dilancin labaran Najeriya wato NAN ya ce majalisar ta yanke wannan shawarar ne bayan wani zama da ta yi ƙarƙashin jagoranta, Hamisu Chidari, a ranar Litini. A lokacin gabatar da rahoton, shugaban kwamitin wucin-gadi da aka naɗa domin bincike akan zargin da ake yiwa Muhiyi, Musa Gama na jam’iyyar PDP ya shaida cewa mambobin kwamitin mai ƙunshe da mutum 12 sun kammala bincikensu da…

Cigaba Da Karantawa

Muna Fuskantar Barazana Domin Mu Sauya Sheka Zuwa APC – Gwamnonin PDP

Rahotanni daga Jihar Bauchi na bayyana cewar Shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP Aminu Waziri Tambuwal, ya yi zargin cewa gwamnonin da suka koma jam’iyyar APC sunyi hakan ne don kada a bincike rashawar da suka tafka a baya. An ruwaito cewa Tambuwal ya bayyana cewa sauran gwamnonin PDP ba za su tsorata ba da dukkanin wata barazana da za’a yi musu domin su canza sheka zuwa APC. Tambuwal, wanda ya samu wakilcin gwamnan Taraba, Darius Ishaku, ya yi magana ne a ranar Lahadi wurin taron da aka gudanar a gidan…

Cigaba Da Karantawa

Buhari Ya Cika Dukkanin Alkawurran Da Ya Yi Wa ‘Yan Najeriya – Jigon APC

Babban Jigon jam’iyya mai mulki ta APC a jihar Benuwai, Terhemba Ishegh, yace shugaba Buhari ya cika mafi yawan alƙawurran da ya ɗauka yayin yakin neman zaɓensa ga yan Najeriya, kuma ya kamata ‘yan Najeriya su nuna godiyarsu bisa ga hakan. Mr. Ishegh, wanda tsohon sakataren dindindin ne a jihar Benuwai, ya faɗi hakane yayin wata hira da yayi da Kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) a makurɗi. Yace Buhari ya kafa ayyuka da dama duk da ƙalubalen tsaron da ƙasar nan ke fama da shi, amma duk da haka…

Cigaba Da Karantawa