2023: Bama Goyon Bayan Mulki Ya Koma Kudu – Matasan Arewa

Gamayyar kungiyoyin matasan arewa guda arba’in da biyu (42) a karkashin inuwar kungiyar shugabannin matasan Arewa (NYLF) sun bayyana bukatar gwamnonin kudu na neman mika shugabancin kasa ga kudu a 2023 a matsayin rashin tunani, cin fuska, da kuma tsokana. Shugaban kungiyar ta NYLF na kasa, Eliot Afiyo, wanda ya bayyana matsayin kungiyoyin a taron manema labarai a Yola, jihar Adamawa, ya ce gwamnonin kudu sun fallasa rashin gogewarsu da yarintarsu a siyasa da irin wadannan bukatun. Matasan na Arewa na martani ne ga buƙatar gwamnonin kudu na baya-bayan nan…

Cigaba Da Karantawa

Jigawa: An Ba Karuwai Wa’adin Wata Guda Su Fitar Da Mazan Aure

Rahotanni daga Karamar hukumar Gwaram ta jihar Jigawa na bayyana cewar ƙaramar Hukumar ta dauki sabbin matakai a yakin da ta ke yi da mata masu zaman kansu inda ta basu wa’adin kwanaki 30 su fice daga yankin ko kuma a aurar da su. Matan masu zaman kansu wadanda ba yan asalin jihar ko karamar hukumar bane za a mayar da su garuruwansu na asali muddin wa’adin ya cika ba su gabatar da Mazan Aure ba. Rahoton ya kuma ce wadanda kuma yan gari ne da ke da niyyar tuba…

Cigaba Da Karantawa

Buhari Na Nuna Kabilanci Wajen Rabon Arzikin Kasa – Gwamnan Binuwai

Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benuwai ya ce kololuwar yaudara da munafurci ne ya sa Gwamnatin Tarayya ta amince da Naira biliyan 6.25 don kiwon zamani a Jihar Katsina har ta riga ta saki Naira biliyan 5, yayin da ita gwamnatin ke neman dawo da burtalolin shanu da zimmar karfafa kiwo a fili a wasu jihohin na tarayya. Gwamna Ortom, wanda ya fadi hakan a filin jirgin saman Makurdi, yana mayar da martani ne ga bayanan da Gwamna Bello Masari ya yi, yayin kaddamar da aikin Madatsar Ruwa ta Zobe…

Cigaba Da Karantawa

Rundunar Soji Ta Shiga Farautar Makasan Janar Hassan Ahmad

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumomin tsaro sun fara bincike kan kisan wani Janar din soja, Hassan Ahmed, wanda wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka harbe a kan hanyar Lokoja zuwa Abuja. An ruwaito cewa sojojin na Najeriya da sauran hukumomin tsaro sun kaddamar da wani mummunan farmaki na hadin gwiwa a yankin Koton Karfe na Jihar Kogi, inda aka kai wa jami’in sojin hari. ‘Yar uwarsa wacce take cikin motar tare da shi, rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun…

Cigaba Da Karantawa

Kungiyar ‘Yan Jarida Ta Yi Watsi Da Umarnin NBC Na Yada Labaran ‘Yan Ta’adda

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kungiyar Mammalaka gidajen jarida na Talabijin da rediyo a Najeriya sun yi watsi da umurnin gwamnatin tarayya na cewa kafofin yada labarai su daina bayar da bayani kan hare-haren yan bindiga da masu garkuwa da mutane. Shugaban kungiyar Editocin Najeriya NGE, Mustapha Isah; shugaban gamayyar yan jaridan Najeriya, Chris Isiguzo; da Diraktan kungiyar dokokin kafafen yada labarai, Richard Akinnola, sun yi ittifakin cewa ba zasu bi wannan umurnin. A cewarsu, ba kafofin yada labarai ke kirkiran labarai ba, kawai suna sanar da…

Cigaba Da Karantawa

Imani Da Adalcin Buhari Ne Ya Sa Gwamnoni Ke Sauya Sheka Zuwa APC – APC

Jam’iyyar APC ta musanta zargin da PDP ta yi cewa Gwamnatin APC ce daga sama ke yi wa Gwamnonin PDP barazana da tursasawa su na barin jam’iyyar zuwa APC. Wannan raddi dai APC ta yi shi ne ga Gwamnonin PDP waɗanda su ka bayyana cewa barazana da tursasawa ce aka yi wa Gwamna Ben Ayade da Bello Matawalle su ka ka APC. Gwamnonin biyu dai sun canja sheƙa daga PDP sun koma APC a cikin watannin Mayu da Yuni bi-da-bi. Zargin Da Gwamnonin PDP Su Ka Yi: “Dukkan Gwamnonin PDP…

Cigaba Da Karantawa