Za Mu Taimaka Wajen Ganin Abubuwa Sun Daidaita A Chadi – Buhari

Shugaba Buhari ya faɗa wa Janar Mahamat cewa Najeriya za ta tallafa wajen daidaita Chadi da kuma tabbatar da komawarta kan tsarin mulkin dimokuraɗiyya. “Najeriya ta san irin rawar da Chadi ta taka wajen taimaka mata a yaƙi da ta’addanci kuma muna godiya sannan za mu ci gaba da wannan alaƙar”, in ji Buhari. “Nahiya da al’adu sun haɗa ƙasashenmu waje guda, saboda haka za mu taimaka a cikin duk abin da za mu iya”. Buhari ya kuma bayyana mahaifin sabon shugaban Chadin wato Idris Deby Itno a matsayin abokinsa…

Cigaba Da Karantawa

An Gudanar Da Sallar Idi Cikin Ruwan Sama A Jalingo

Sakamakon saukan ruwan Sama kamar da bakin kwarya, ya jinkirta Sallar Idi Karama a Jalingo, Fadar Jihar Taraba. Wakilinmu Bashir Adamu ya ruwaito mana cewa duk da ruwan Saman Sallar Idin ya gudana cikin Annashawa da kwanciyar hankali. Jihar Taraba ta bi sahun sauran Jihohin Kasannan wurin gudanar da Sallar Idi Karama, duk da ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka wayi Gari da shi a garin Jalingo. Karamar Hukumar Lau, na daya daga cikin Kananan Hukumomi goma sha shida a Jihar da Taraba da ke yawan fuskantar matsalolin…

Cigaba Da Karantawa

Matsalar Tsaro: Najeriya Na Bukatar Addu’a – Limamin Sultan Bello

Babban Limamin Masallachin Juma’a na Sultan Bello Kaduna Dr. Muhammad Suleman ya yi kira ga jama’ar Musulmi da su sanya Najeriya cikin addu’o’in su a lokacin bukukuwan sallah dake gudana domin fita daga halin matsalar tsaro dake addabar kasar. Limamin ya yi wannan kiran ne a yayin gabatar da hudubar idin salla karama da ya jagoranta a filin idi na Masallachin Juma’a na Sultan Bello da ke Kaduna. Imam Muhammad Suleman ya kara da cewar tabbas Najeriya na cikin wani mawuyacin hali na taɓarɓarewar tsaro a wannan lokaci, kuma mafita…

Cigaba Da Karantawa

Goron Sallah: Ganduje Ya Yi Wa Fursunoni 123 Afuwa

Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar mai girma Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya saki fursunoni 123 daga gidajen gyaran hali a fadin jihar a matsayin wani goron sallah a gareshi. Ganduje, wanda ya sa aka saki fursunonin a gabansa daga gidan Kurkuku na Goron Dutse a ranar Alhamis ya ce anyi musu wannan karamcin ne albarkacin bikin karamar Sallah. Ya ce an zabi wadanda suka amfana da afuwar ne bisa la’akari da yanayin laifukansu da kuma alamun da ke nuna cewa sun gyaru sun sauya halayensu.…

Cigaba Da Karantawa

Buhari Ya Zama Kadangaren Bakin Tulu Ga ‘Yan Arewa – Matasan Arewa

An bayyana salon mulkin Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a matsayin wani tarnaki wanda ya zama wa ‘yan Arewa Ƙadangaren bakin tulu, a tsige shi ya zama matsala a barshi kuma Arewa ta cigaba da fuskantar tasku. Bayanin hakan ya fito ne daga bakin ɗaya daga cikin Shugabannin Ƙungiyar Matasan Arewacin Najeriya Kwamared Kamal Nasiha Funtuwa a yayin wata tattaunawa da manema labarai da ya yi a garin Kaduna. Shugaban Matasan yana mayar da martani ne dangane da kiran da kungiyar Dattawan Arewa ta yi ga Majalisa na ta tsige Buhari…

Cigaba Da Karantawa