SALLAH: An Shawarci Musulmi Kar Su Manta Darussan Ramadan – Ramalan

A daidai lokacin da al’ummar Musulmi a faɗin duniya ke gudanar da bukukuwan karamar Sallah, Shugaban Kamfanin ATAR Communication mamallakan Gidajen Talabijin da Rediyo na Liberty Alhaji Dr Ahmad Tijjani Ramalan, ya bukaci al’umma da kar su manta darussan da suka koya a yayin ibadar watan azumin Ramadan. Ramalan ya bayyana hakan ne a cikin sakon barka da Sallah da ya aikewa jama’ar Musulmi na fatan kammala azumin Ramadan lafiya da bikin Sallah karama. Sannan ya yi addu’a Allah ya amshi ibadun da Musulmi suka yi da sauran ayyukan alheri…

Cigaba Da Karantawa

Ta’addanci: Fito Na Fito Da ‘Yan Bindiga Ne Magani – Sarkin Muri

Rahotanni daga Masarautar Muri Jalingo Jihar Taraba na bayyana cewar mai Martaba Sarkin Muri, Alhaji Abbas Njidda Tafida ya umurci mutanen masarautarsa su yi fito-na-fito da masu garkuwa da mutane da yan bindiga a maimakon su rika tserewa idan sun kawo musu hari, domin kawo karshen matsalar. Sarkin ya yi wannan jawabin ne a ranar Alhamis 13 ga watan Mayu a lokacin da mutane suka kai masa gaisuwar sallah yana mai cewa bata garin da ke adabar mutane kalilan ne idan aka kwatanta su da mutanen gari. “Idan sun kashe…

Cigaba Da Karantawa

An Zargi Hadiza Da Laifin Rashin Kunya Ga Manya

Rikicin cikin gidan da ake yi tsakanin shugabar NPA, Hadiza Bala Usman da Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya na neman ya dauki wani irin yanayi. Inda Ministan ya yi ƙari akan zargin da yake yi wa tsohuwar shugabar hukumar tashoshin jiragen ruwa NPA na kin dawo da Naira biliyan 165 a asusun gwamnati na CFR. Wani cikin ‘yan kwamitin da aka kafa ya shaida wa manema labarai cewa yanzu za su maida hankali ne a kan zargin Hadiza Bala Usman da laifin rashin kunya, da tsiwa ga manya. “Muna kallon…

Cigaba Da Karantawa

Jarumar Finafinan Hausa Khadijah Abubakar Ta Rasu

ALLAHU Akbar! Masu iya magana su ka ce rai baƙon duniya. Wannan batu haka ya ke. A safiyar ranar Alhamis, 6 ga Mayu, 2021 Allah ya yi wa jaruma Khadija Abubakar Mahmud rasuwa. Khadija ta rasu a garin Jalingo, babban birnin Jihar Taraba, da misalin ƙarfe 6 na safe a hannun mahaifiyar ta a kan hanyar su na zuwa asibiti. Cikin alhini, mahaifiyar ta shaida wa mujallar Fim cewa sun ɗauki Khadija sun kai ta wani asibitin kuɗi, amma da zuwan su likitocin asibitin su ka ga halin da ta…

Cigaba Da Karantawa

Bikin Sallah: An Tura ‘Yan Sanda Sama Da 4,000 Kano

Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar Rundunar ‘yan sanda a jihar ta tura jami’anta 4,144 don samar da tsaro a fadin jihar yayin bukukuwan Sallah da zai gudana a yau. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, ASP Abdullahi Haruna ya fitar a ranar Laraba a Kano kuma aka rarraba ta ga manema labarai a birnin Kano. Haruna ya ce za a tura ‘yan sanda zuwa wurare masu mahimmanci da suka hada da filayen Sallar Idi a lokacin bikin, da sauran wuraren taruwar jama’a. Kakakin ya…

Cigaba Da Karantawa

Yau Take Sallah A Najeriya Da Saudiyya

Yau Alhamis 13 ga wata Mayun shekarar 2021 ita ce ta kasance ranar 01 ga watan Shawwal na shekarar 1442 bayan hijirar FIyayen talikai Annabi Muhammadu SAW daga Makka zuwa Madina wato ranar Sallah ƙarama a kasashen Najeriya da Saudiyya. Tun da fari sai da fadar mai alfarma Sarkin Musulmi ta bada sanarwar duba jinjirin Wata a ranar Talata 29 ga Ramadan, inda sanarwar ta bayyana cewar idan ba a ga watan za’a cike Ramadan zuwa kwanaki 30 a ranar Laraba sannan ayi bukukuwan sallah a ranar Alhamis. Rahotanni daga…

Cigaba Da Karantawa