EFCC Ta Kwato Dala Miliyan 153 A Wajen Tsohuwar Ministar Mai

Hukumar dake yaki da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati, EFCC, ta sanar da kwato $153m daga hannun tsohuwar ministar man fetur Diezani Alison Madueke wadda ta tsere daga kasar zuwa Birtaniya a 2015. Jaridar Vanguard ta ambato shugaban hukumar Abdulrasheed Bawa yana cewa sun kwace akalla kadarori 80 da kudinsu ya kai $80m. “Muna fatan ganin lokacin da, watakila, za ta shigo kasar nan, kuma tabbas za mu yi nazari kan abubuwan da ta yi, sannan mu san matakin da za mu dauka nan gaba. Tabbas ba mu…

Cigaba Da Karantawa

Buhari Ya Yi Kiran Yin Al-Qunuti Ga ‘Yan Bindiga

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mika sakon gaisuwarsa ga Musulman kasar da ma na kasashen waje a yayin da ake shirin yin sallar Idi. Wata sanarwa da Malam Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasar ya aike wa manema labarai ranar Laraba ta ambato Shugaba Buhari yana fatan za a gudanar da bukukuwan sallah cikin “zaman lafiya, tsaro da ‘yan uwatantaka da kuma kauna ga kowa.” Ya kara da cewa hadin kai tsakanin Musulmai da Kiristoci yana da matukar muhimmanci musamman a wannan lokaci da kasar take fama da…

Cigaba Da Karantawa

Dalilina Na Jagorantar Sallar Idi Yau Laraba – Ɗahiru Bauchi

Fitaccen malamin darikar Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Bauchi ya bayyana cewa shi da mabiyan sa ba su yarda da cika azumi zuwa 30 ba, shine yasa suka yi sallar Idi ranar Laraba maimakon Alhamis da sarkin Musulmi ya sanar. A jawabin da yayi a filin Idi wanda ya karade shafukan sada zumunta a yanar gizo, Shehin malamin ya ce don saudi Arabiya bata ga wata ba, bai zama dole ace ba a ganshi a Najeriya ba. ” Lokuttan sallar mu na farilla ba daidai yake da na Saudiya ba saboda haka,…

Cigaba Da Karantawa

Zan Sauya Fasalin Darikar Tijjaniya – Sanusi

A hira da gidan rediyon BBC Hausa Khalifa Muhammadu Sunusi II ya bayyana wa BBC Hausa cewa baban abinda zai fara maida hankali a matsayinsa na halifan tijjaniyya na Najeriya shine, na farko zamu fara zama da junan mu ‘yan tijjaniyya (masu hannu da shuni) mu kara fahimtar juna, sannan mu duba kalu balen da tijjaniyya ke fuskanta da addinin musulunci baki daya, musamman arewacin Najeriya. Akwai matsaloli a harkar ilimi da iyali da yara da abinda ya shafi zawiyyoyi da tsangayu, zamu tafi da jagorancin Tijjaniyya daidai da ƙarni…

Cigaba Da Karantawa

A Shirye ‘Yan Bindiga Suke Su Ajiye Makamai – Tsohon Shugaban Inshora

Tsohon shugaban hukumar inshoran lafiya ta ƙasa (NHIS), Usman Yusuf, yace ‘yan bindiga na buƙatar tattaunawar zaman lafiya da malamai, saboda haka a shirye suke su watsar da makamansu domin rungumar zaman lafiya. Usman Yusuf ya bayyana cewa ya fahimci haka ne a taron da suka yi da yan bindigan kala daban-daban a cikin ayarin da ya kasance a ciki ƙarkashin jagorancin Sheikh Dr. Ahmad Abubakar Mahmoud Gumi. Yayin da yake jawabi a wata tattaunawa da yayi da gidan talabishin na Arise Tv ranar Talata, Yusuf yace: “Wannan shine abinda…

Cigaba Da Karantawa

Akwai Laifin ‘Yan Najeriya A Matsalar Tsaron Da Ake Ciki – Na’Allah

Sanatan mai wakiltar Kudancin jihar Kebbi, ya yi kira ga sauran mutanen Najeriya su taimaka wa gwamnatin tarayya wajen samar da zaman lafiya. Bala Ibn Na’Allah ya bayyana wannan ne jim kadan bayan ya gana da Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar Shugaban kasa a jiya. Ɗan majalisar Dattawan ya bayyana cewa ya ziyarci fadar Shugaban ƙasa ne domin ya yi zaman da ya saba yi da Buhari a kan sha’anin kasa. Sanata Bala Na’Allah bai yi bayani ko ya kai wa shugaban kasar ziyara ne da sunan…

Cigaba Da Karantawa

Ba A Samu Ganin Jinjirin Watan Salla A Najeriya Ba – Sarkin Musulmi

Kwamitin da ke bai wa Sarkin Musulmi shawara kan harkokin addini tare da hadin gwiwar Kwamitin Duban Wata a Najeriya sun ce ba su samu rahoton ganin jaririn watan Shawwal a Najeriya ba a yau Talata 11 ga watan Mayun 2021 wanda ya yi dai-dai da 29 ga watan Ramadan 1442 AH. Don haka Sarkin Musulmi, Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar CFR, mini ya ayyana Alhamis 13 ga watan Mayu 2021 a matsayin ranar Sallah kuma 1 ga watan Shawwal. Sarkin Musulmi ya taya Musulmin Najeriya murna tare da fatan Allah…

Cigaba Da Karantawa

Harin ‘Yan Bindiga A Fadar Shugaban Kasa Ya Tabbatar Da Gazawar Buhari – PDP

Babbar Jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta bayyana tsananin firgici da shiga tashin hankali game da fashin da ‘yan bindiga suka yi a kusa da fadar shugaban kasa, Aso Villa a babban birnin tarayya Abuja. PDP ta nuna damuwa kan lamarin, tana mai zargin rashin iyawar shugaba Muhammadu Buhari ta fuskar bai wa kasar cikakken tsaro don kare rayukan al’umma, wanda wannan tabbas abin takaici da baƙin ciki ne. A daren ranar Litinin ne fadar shugaban kasa ta fitar da wata sanarwa ta hannun mai magana da yawun shugaban…

Cigaba Da Karantawa