‘Yan Bindiga Sun Bindige Jigon Kudancin Kaduna

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar easu yan bindiga sun harbe wani jigo a yankin Kudancin Jihar mai suna Mr. Christopher Madaki, tare da matarsa da kuma sirikarsa a garin Golkofa ta ƙaramar hukumar Jema’a jihar Kaduna. Kwamishinan tsaron cikin gida, Mr. Samuel Aruwan, shine ya sanar da haka a wani saƙo. Kwamishina yace: “Hukumar yan sanda ta jihar Kaduna da hedkwatar tsaro, sun aikewa gwamnatin jihar Kaduna rahoton kisan mutane uku yan asalin jihar. “A bayanan da muka samu bayan faruwar lamarin, yan bindigan sun farmaki gidan Christopher…

Cigaba Da Karantawa

Matsalar Tsaro: Ba Zan Je Sallah Daura Ba – Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya sanar da dakatar da zuwa mahaifarsa ta Daura domin ziyarar da ya saba zuwa a kowace sallar Idi. A cikin sanarwar daga Garba Shehu da ke magana da yawun shugaban, Shugaba Buhari y ace ya shirya gudanar da Sallar Idi a Fadarsa da ke Abuja kamar yadda ya yi a shekarar da ta gabata saboda halin corona da duniya ke ci gaba da fuskanta. Sanarwar ta ce Shugaba Buhari zai yi Sallar Idin da iyalensa da ma’aikatansa na kusa da shi da kuma wasu manyan…

Cigaba Da Karantawa

Ban Da Lokacin Ortom – El Rufa’i

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa bai taba daukar gwamnan Benuwai, Emmanuel Ortom da wani mahimmanci ba, domin gazawarsa ba ya misaltuwa, kullum, yana sukar gwamnatin tarayya ne kan gazawarsa. El-Rufai ya kara da ba da misalin yadda ma’aikatan jihar Benuwai ke bin bashin albashin watanni masu yawa a jihar, bai iya yin komai ba sai dai ya kullum gwamnatin tarayya ta gaza, ta gaza. ” Yana kanannade da matsalolin sa na rashin iya gudanar da al’amurar gwamnati a jihar sa, amma a kullum kukan sa, shine gwamnatin…

Cigaba Da Karantawa

Za A Gurfanar Da Masu Ɗaukar Nauyin Ta’addanci A Kotu – Malami

“Fitattun ‘yan Najeriya wadanda ke daukar nauyin ta’addanci za su fuskanci tsarin shari’a nan ba da jimawa ba kasancewar gwamnatin tarayya ta kammala shirye-shiryen gurfanar da su” Babban Atoni Janar na Tarayya, Abubakar Malami (SAN) ne ya bayyana wannan ci gaban a ranar Juma’a, 7 ga watan Mayu na wannan Shekarar da muke ciki. Malami wanda bai bayyana sunayen wadanda ake zargin ba ko kuma yawan mutanen da abin ya shafa ba ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai na Fadar Shugaban Kasa a Fadar Shugaban…

Cigaba Da Karantawa

Kano: Rikicin Cikin Gida Ya Kunno Kai A Kwankwasiyya

Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar hargitsin cikin gida ya fara tsakanin mabiyan kungiyar Kwankwasiyya dake jihar Kano. Hakan ya faru ne sakamakon rabon kayan abinci na azumi na miliyoyin naira da wani yayi wa ‘yan jam’iyyar a Kano, Hadimin sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Sanusi Surajo, ya sanar da cewa ya ga wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta inda Dakta Adamu Dangwani ke shirin farraka kan ‘yan Kwankwasiyyan. Dangwani tsohon kwamishinan ruwa ne kuma shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Kano yayin mulkin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso. A zargin…

Cigaba Da Karantawa

Tallafin Korona: Mun Raba Miliyan 25 Ga ‘Yan Najeriya – Gwamnan Babban Banki

Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya bayyana cewa yunkurin da kamfanoni masu zaman kansu sukayi na raba kayan tallafin Koronan bilyan 25 ya taimakawa talakawa sosai a lokacin da aka yi zaman dirshan na kullen Korona. Gwamnan Babban bankin ya bayyana hakan ne a shirin kaddamar da wani Fim mai suna ‘Unmasked’ ranar Juma’a a jihar Legas. Emefiele, wanda ya samu wakilcin mukaddashin diraktan sadarwa na CBN, Osita Nwamsobi, ya bayyana cewa wadannan kamfanoni masu zaman kansu sun hada cibiyoyin killace masu Korona 39 a fadin tarayya. Yace, “Akan…

Cigaba Da Karantawa

Za Mu Sa Aljannu Cikin Almajiranmu Su Kau Da ‘Yan Bindigar Najeriya – Ɗahiru Bauchi

Babban malamin addinin musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya yi wata magana wanda ta ba dinbin mabiyansa da sauran al’umma mamaki. Shehin malamin ya bayyana cewa akwai wasu kebantattun mutane da su ke iya sadu wa da aljanu. Ya ce ya na daga cikin masu mu’amala da su. Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya ce wasu suna ganinsu, har su yi magana da su, kamar yadda shaidanun mutane su ke hulda da shaidanun Aljanu. A cewar Sheikh Dahiru Usman Bauchi akwai Aljanu muminai, daga cikin su har mabiya Darikar Tijjaniya wanda…

Cigaba Da Karantawa