Dole A Dakatar Da Kisan ‘Yan Arewa – Matawalle

“Ya zama dole a matsayina na gwamna kuma mai kishin Arewa da nayi magana akan abubuwan dasu ke faruwa a kasar nan. Wannan ba magana ce ta siyasa ba. Lokaci yayi da zamu faɗawa kanmu gaskiya domin dawwamar zaman lafiya da cigaban ƙasarmu, da kuma kare Nijeriya daga afwaka tashin hankalin da wasu ɓata-gari ke son jefa ta a ciki. Duba da yadda mukeyin siyasa a ƙasar nan, za ayi tsammanin jawabi irin wannan daga gwamna ko wani shugaba na jam’iyar APC zai fito, ba ni ba cikakken ɗan jam’iyar…

Cigaba Da Karantawa

Katsina: An Yi Odar Karnuka Domin Gadin Makarantu

Gwamnatin jihar Katsina ta amince da tura Karnuka gadin makarantun kwanan jihar domin taimakawa jami’ar tsaro wajen dakile ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane. Kwamishinan ilimin jihar, Dr Badamasi Charanchi, ya bayyana cewa gwamnatin ta yanke shawaran haka ne domin karfafa matakan tsaro a makarantun kwanan jihar. “An bamu shawaran tura Karnuka kowace makaranta saboda suna da horaswa na gano wani mai yunkurin kutse fiye da dan Adam.” “Wadannan karnukan idan aka tura su, zasu ankarar da dalibai da sauran jami’an tsaro idan wasu yan bindiga na kokarin zuwa.”…

Cigaba Da Karantawa

Aminu Kano Ya Cika Shekaru 38 Da Rasuwa

Shahararren ɗan siyasan a arewacin Najeriya, Marigayi Mallam Aminu Kano wanda ya riƙa fafutukar karɓowa talakawa ƴancin su, Ya rasu ne ranar 17 ga watan Afrilu 1983 a jihar Kano zamanin mulkin Alh. Shehu Aliyu Shagari yana mai shekara 62 a duniya. Allahu Akbar! A TAƘAICE: Da farko Malam Aminu Kano yana tare da jam’iyyar NPC kafin ya ɓalle da jama’ar sa zuwa NEPU. Malam da mutanen sa sun gamu da tsangwama daga manyan NPC a NEPU, A 1954 yayi takarar kujerar majalisa ya sha ƙasa hannun Maitama Sule daga…

Cigaba Da Karantawa

Ban Da Alaka Da ‘Yan Ta’adda: Sakatare Da Direbana Duk Kiristoci Ne – Pantami

Ministan Harkokin Sadarwa Isa Ali Pantami yace bayanan da aka fitar yan kwanakin nan akan yana da alaka da Yan Taliban da Al-Qaeda ba gaskiya bane. Ministan ya kara dacewa baya da wata rashin jituwa da Kiristoci, inda ya bayyana cewa Direban sa da Sakatare gami da Mai taimaka masa, Dukkanin su Kiristoci ne. Pantami ya bayyana haka a wata zantawa da Jaridar Peoples Gazette tayi dashi a ranar Juma’ar nan data gabata. Yace”Direba na sunan sa Mai Keffi wanda addinin kiristanci yake bi. kuma akwai Ms Nwosu wadda Sakatariya…

Cigaba Da Karantawa

Saudiyya Ta Aike Kur’anai Miliyan Guda Ga Kasashe 29

Ma’aikatar kula da harkokin addini ta saudiyya, ta fara raba kur’anai miliyan 1,200,000 fassararru cikin yaruka 21 zuwa kasashe 29 a fadin duniya a matsayin kyauta. Jirgin wanda ya fara hadin kai tsakanin ofishin jakadancin Saudiyya da ibiyoyin addini da al’ada da kuma Saudiyya a wadancan kasashen. Da yake magana a lokacin gabatar da taron, Ministan harkokin addinin musulunci Dakta Abdallatif Al Al-Sheik, wanda kuma yake lura da harkokin cibiyar dab’i ta Sarki Fahad, ya yi matukar godiya ga mai yi wa masallatan harami hidima Sarki Salman kan wannan taimako…

Cigaba Da Karantawa

Buga Takardun Kudi: Babu Gaskiya A Maganar Obaseki – Ministar Kudi

Gwamnatin Najeriya ta karyata ikirarin da Gwamnan Jihar Edo ya yi cewa ta buga Naira biliyan 60 ta zuba cikin kudaden kasafin da ta ke rabawa a watan Maris. Ministar harkokin Kudade, Kasafi da Tsare-tsare Zainab Ahmed ce ta karyata Gwamna Obaseki, a lokacin da ta ke wa manema labarai bayani a Fadar Shugaban Kasa. Minista Zainab ta kara da cewa ikirarin Obaseki abin takaici ne kuma abin haushi, saboda ko kadan ba gaskiya ba ne. “Wannan ikirari da Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki ya yi ni dai a bangare…

Cigaba Da Karantawa

Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Nemi Miliyan 500 Kuɗin Fansar Ɗalibai

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Iyayen daliban kwalejin horar da aikin noma da gandun dabbobi dake yankin ƙaramar Hukumar Igabi Afaka a jihar Kaduna, sun ce an bukaci su biya kudin fansar ‘ya’yansu har naira miliyan 500 kafin a sako su. An bukaci da su cire rai daga tallafi ko taimakon gwamnati wurin ceto rayukan ‘ya’yansu, duk da 10 daga cikin daliban an sako su kuma tuni suka sadu da iyayensu, sauran suna cikin daji tun a ranar 11 ga watan Maris na 2021. A yayin tattaunawa da…

Cigaba Da Karantawa

Saɓa Alkawarin Da Jonathan Ya Yi Ne Silar Faɗuwarshi Zaɓe – Aliyu

Tsohon gwamna Mu’azu Babangida Aliyu ya tabbatar da cewa wasu gwamnonin jam’iyyar PDP sun juya wa Goodluck Jonathan baya a babban zaben 2015, sakamakon saɓa alƙawarin da ya yi musu gabanin zaɓe. Tsohon gwamnan ya ƙara da cewar shi da wasu gwamnonin Arewa a wancan lokaci sun yi wa Jonathan zagon-kasa ne saboda saba yarjejeniyar da suka yi dashi, su kuma suka yi amfani da damar da suke da ita wajen kawar dashi. A cewar Babangida Aliyu, wanda ya yi mulki zuwa 2015, tsohon shugaban Najeriyar ya karya alkawarin da…

Cigaba Da Karantawa

Bashin Da Ake Bin Najeriya Ya Haura Tiriliyan 33 – Hukumar Kula Da Basussuka

Babbar Darakta a Ofishin kula basussukan Najeriya ta ƙasa DMO, Patience Oniha, ta ce basussukan da ake bin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohin yanzu ya kai N33.63 trillion. A jawaban da ta saki a shafin sadarwanta na Tuwita, Oniha ta ce jita-jitan da ake yadawa kan adadin bashin da ake bin Najeriya yasa ta wallafa jerin basussuka. A cewarta, “yana da muhimmanci in fayyace cewa wannan bashin na gwamnatin tarayya ne, birnin tarayya, da jihohin Najeriya 36,” “Bashin ba na gwamnatin tarayya bane kadai, gwamnonin jihohi da birnin tarayya na…

Cigaba Da Karantawa