Ba Za Mu Yafe Bashin Da Muke Bin Najeriya Ba – Bankin Bada Lamuni

A daidai lokacin da ɗimbin bashi ya yi wa Najeriya tarnaki a wuya, Hukumar bada Lamuni ta Duniya, IMF ta cire Najeriya daga cikin jerin kasashen da zata yafewa bashin da take bi. Zuwa yanzu Hukumar ta ware wasu kasashe 28 da zata yafewa bashin, inda za’a yi amfani da wasu kudi da aka ajiye na ko ta kwana wajen biyawa wadannan kasashen bashin da hukumar ke binsu. Kasashen da aka yiwa yafiyar dai sune, Afghanistan, Benin, Burkina Faso, Burundi, Central African Republic, Chad, Comoros, Democratic Republic of the Congo,…

Cigaba Da Karantawa

Usman Alkali Ya Zama Sabon Shugaban ‘Yan Sanda

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin mataimakin Shugaban ‘Yan Sandan Najeriya Usman Alkali Baba, a matsayin sabon shugaban rundunar ‘yan sandan Najeriya. Usman Alkali ya maye gurbin Mohammed Abubakar Adamu, wanda wa’adin Shugabancin sa ya ƙare kamar yadda dokokin kasa suka tanada. Ministan kula da harkokin ‘yan sandan Najeriya, Maigari Dingyadi ne ya sanar da hakan ga manema labaran gidan gwamnati a ranar yau Talata. A ranar 4 ga watan Fabrairun shekarar nan ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara wa’adin mulkin shugaban ‘yan sandan Najeriya Mohammed Adamu.…

Cigaba Da Karantawa

Usman Alkali Ya Zama Sabon Shugaban ‘Yan Sandan

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin mataimakin Shugaban ‘Yan Sandan Najeriya Usman Alkali Baba, a matsayin sabon shugaban rundunar ‘yan sandan Najeriya. Usman Alkali ya maye gurbin Mohammed Abubakar Adamu, wanda wa’adin Shugabancin sa ya ƙare kamar yadda dokokin kasa suka tanada. Ministan kula da harkokin ‘yan sandan Najeriya, Maigari Dingyadi ne ya sanar da hakan ga manema labaran gidan gwamnati a ranar yau Talata. A ranar 4 ga watan Fabrairun shekarar nan ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara wa’adin mulkin shugaban ‘yan sandan Najeriya Mohammed Adamu.…

Cigaba Da Karantawa

Katsina: Kwastam Ta Kwashe Shinkafar Da Ake Rabawa Talakawa

A cikin daren jiya ne da misalin ƙarfe ɗaya na dare (01:00Am) jami’an kwastam suka shiga cikin kamfanin Alfijir Bread, inda suka kwashe musu buhunnan shinkafar da su ke rabawa al’ummah, a cikin watan Ramadan mai girma a duk shekara. Kamar yadda Gidauniya Tv ta ruwaito, ta samu zantawa da shugaban ma’aikan kamfanin Alfijir Bread Abubakar Nashala, inda yake cewa “na yi mamakin yadda aka kwashe mana buhunnan shinkafa guda 51 da zamu rabawa bayin Allah, a cikin watan ramadan mai daraja, kuma shinkafar siyota mukai a cikin ƙasar nan…

Cigaba Da Karantawa

An Bada Umarnin Kamo Tsagerun Da Suka Kaiwa ‘Yan Sanda Hari A Imo

Babban Baturen ‘Yan sandan Najeriya Sufeta Janar Mohammed Adamu, ya dora alhakin kai hari ofishin yan sanda na jihar Imo akan kan kungiyar Tsagerun Inyamurai (IPOB) inda ya bayyana fusatarshi akan haka da kuma ɗaukar matakan da suka dace wajen ladabtar da Tsagerun. A cikin sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sanda, CP Frank Mba ya fitar a madadin sufeta janar na ‘yan sandan, ya ce Shugaban ‘yan Sandan ya umurci kwamishinan ‘yan sandan jihar Imo ya gudanar da sahihin bincike da nufin gano wadanda suka kai harin domin su fuskanci…

Cigaba Da Karantawa

Barazanar Yajin Aiki: Ministan Ilimi Ya Gayyaci Malaman Jami’o’i

Biyo bayan barazanar sake tsunduma yajin aiki da kungiyar malaman jami’o’i a Najeriya ta kuduri aniyar yi, Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya gayyaci shugabannin kungiyar malaman jami’o’in (ASUU), zuwa wani taron gaggawa domin lalubo bakin zaren. Taron wanda aka shirya yi a ranar yau Talata 06/04/21 yana zuwa ne bayan barazanar da kungiyar Malaman Jami’o’in ta yi na shiga wani yajin aikin. Bayanin hakan ya faru ne a yammacin Litinin yayin da daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar, Bem Goong, ya ruwaito Ministan yana bayanin cewa taron…

Cigaba Da Karantawa

Zanga-Zangar Landan: Masoyan Shugaban Kasa Sun Kunyata ‘Yan Adawa

Bayan wata zanga-zangar ds wasu ‘yan Najeriya da ake zaton ‘yan adawa ne mazauna birnin Landan suka yi wa Shugaban ƙasa Buhari a masaukin shi dake babban birnin kasar, inda zanga-zangar ta rikide wani abu daban ta hanyar zage zage da cin mutunci. Daga bisani gungun wasu masoya Shugaban kasar a birnin Landan suma sun gudanar da wata zanga-zangar lumana da nuna goyon baya ga Buhari da kuma kishin Najeriya. Masoya Shugaban kasar sun isa masaukin Shugaban Najeriya dake birnin Landan gidan da aka fi sani da ‘Abuja House’ da…

Cigaba Da Karantawa