Saura Ƙiris Abubuwa Su Daidaita A Najeriya – Osinbajo

Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbaj a ranar Lahadi, ya karfafa wa ‘yan Nijeriya gwiwa da cewa “su yi babban fatan cewa nan bada dade wa ba, abubuwa za su daidaita a kasar nan” kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito. Osinbajo ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da yayi da manema labarai bayan kammala bikin Ista a ranar Lahadi a Aso Villa Chapel. A cewar wata sanarwa daga babban hadiminsa na musamman kan yada labarai da, Laolu Akande, Osinbajo ya yi addu’ar cewa Najeriya za ta dandana alheri…

Cigaba Da Karantawa

Zanga-Zangar Landan Adawa Ce Da Rashin Kunya Ga Buhari – Abba

An bayyana zanga-zangar da wasu ‘yan Najeriya mazauna Ingila suka yi wa Buhari a birnin Landan da cewar tsantsar adawa ce da rashin kunya wadanda suka yi Zanga-Zangar suka gwada wa Buhari. Bayanin hakan ya fito ne daga bakin wani jigo a jam’iyyar APC ta Jihar Kaduna Alhaji Abdullahi Gambo Abba lokacin da yake tsokaci akan Zanga-Zangar a yayin wata tattaunawa da manema labarai da ya yi a Kaduna. Abdullahi Gambo Abba wanda ke riƙe da Sarautar Jakadan Hayin Banki Kaduna ya ƙara da cewar, abin da wadannan ‘yan Najeriyar…

Cigaba Da Karantawa

Ku Sanya Najeriya Cikin Addu’o’i Lokacin Easter – Mr LA

Honorabul Lawal Adamu Usman (Mr LA) tsohon dan takarar majalisar dattawa mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya ya taya daukacin al’ummar kirista murnar bukin ranar Easter. Mr LA ya kuma yi kira na musamman ga daukacin mabiya addinin kirista da su cigaba da yiwa kasar addu’ar samun dauwamanmen zaman lafiya yayin shagulgulan bikin Esther. Mr LA ya bayyana hakan ne a Kaduna yayin ganawa da manema labarai Jim kadan bayan ya kaiwa wata ziyara a cibiyar kula da marayu, kananan yara da marasa karfi a nan garin kaduna.Daga karshe Ya…

Cigaba Da Karantawa

Ba Zan Taɓa Yin Sulhu Da ‘Yan Bindiga Ba – El Rufa’i

Gwamnatin Jihar Kaduna ƙarƙashin jagorancin Gwamnan jihar Nasir Ahmad El-rufa’i ta musanta labarin da ake yaɗawa cewa an naɗa wata tawaga da zata jagoranci tattaunawa da ‘yan bindiga a fadin Jihar. Kwamishinan tsaro da al’amuran cikin gida, Samuel Aruwan, ya bayyana haka ga manema labarai a ranar Lahadi. Ya ce gwamnatin Kaduna ƙarƙashin jagorancin Malam Nasir Ahmad Elrufa’i ta ji labarin ana yaɗa jita-jita a kafar sada zumunta cewa gwamnatin ta naɗa wakilai da zasu tattauna da yan bindiga a madadinta. A jawabin da kwamishinan ya yi a madadin gwamnan…

Cigaba Da Karantawa

Badaƙakar Filaye: Masarautar Kano Ta Bijirewa Umarnin Kotu

Kwanaki kaɗan bayan da wata Babbar Kotu a jihar Kano ta ba da umarnin hana Masarautar Kano yanka filaye a Filin Sallar Idi na ‘Yar Akwa, majalisar masarautar ta yi biris da umarnin Kotun inda ta ci gaba da yanka filayen. Da yake jawabi ga manema labarai a farfajiyar filin ranar Asabar, shugaban kwamitin filin daga yankin, Tijjani Yahaya, ya ce sun yi mamakin cewa bayan umarnin kotu, sai kawai suka wayi gari da safe suka ga ana aikin yankan filin. Ya bayyana cewa, ’yan sanda dauke da makamai a…

Cigaba Da Karantawa

Najeriya Ta Zama Filin Karkashe Mutane – Kukah

A saƙonsa na bikin Ista na wannan shekara ta 2021 Babban Limamin Cocin Katolika na Sakkwato, Bishop Matthew Kukah, ya yi amfani da damar wajen ƙara sukar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari. A sakon nasa na Ista na 2021 mai taken, ‘Kafin daukakarmu ta tashi’, malamin ya ce masu tayar da kayar baya suna cin karensu babu babbaka a karkashin kulawar Buhari, ba tare da tsoro ko fargaba ba. Bishop Kukah ya ƙara da cewa Buhari ya bayyana kungiyar Boko Haram a matsayin wani yanayi na kananan gobara da ke haifar…

Cigaba Da Karantawa

Obasanjo Da Gumi Sun Bukaci Gwamnati Ta Yi Wa ‘Yan Bindiga Afuwa

Tsohon shugaban kasa Chief Olusegun Obasanjo da Fitaccen Malamin addinin musulunci Sheik Ahmed Gumi sun nemi gwamnatin Buhari ta yi wa tubabbun ‘yan bingida afuwa, domin samar da kyakkyawan tsaro mai ɗorewa a ƙasar. Wannan na zuwa ne bayan wata ziyara da Malamin addinin ya kai wa tsohon shugaban Najeriyan a gidansa da ke Abeokuta babban birnin jihar Ogun. Obasanjo ya ce, “Yan bindigar da suka shirya fita daga daji da kuma daina muggan laifuka, a yi musu afuwa a gyara halayyarsu a koya musu ayyuka a basu jari ya…

Cigaba Da Karantawa