Bauchi: An Yi Kiran Dawo Da Martabar Sarakuna A Dokar Kasa

Mai martaba Sarkin Bauchi Dokta Rilwanu Sulaiman Adamu yaja hankalin yan’majalisun jihohi da suci gaba da aiki tukuru don ganin an dawo ma da sarakunan gargajiya Martabarsu a cikin tsarin dokar kasan Najeriya. Sarkin yayi wan nan kira ne a lokacin da kakakin yan’majalisu na jihohi 36 suka kai mashi gaisuwar bangirma a fadarsa Jim kadan bayan sun kammala taronsu a garin Bauchi a kwana nan Dokta Rilwanu Sulaiman yace su ba Yan siyasa bane amma suna da daraja a cikin al’umma ya kamata ace ana mutunta su a ciki…

Cigaba Da Karantawa

Bauchi: An Yi Kiran Dawowa Sarakuna Martabarsu A Dokar Kasa

Mai martaba Sarkin Bauchi Dokta Rilwanu Sulaiman Adamu yaja hankalin yan’majalisun jihohi da suci gaba da aiki tukuru don ganin an dawo ma da sarakunan gargajiya Martabarsu a cikin tsarin dokar kasan Najeriya. Sarkin yayi wan nan kira ne a lokacin da kakakin yan’majalisu na jihohi 36 suka kai mashi gaisuwar bangirma a fadarsa Jim kadan bayan sun kammala taronsu a garin Bauchi a kwana nan Dokta Rilwanu Sulaiman yace su ba Yan siyasa bane amma suna da daraja a cikin al’umma ya kamata ace ana mutunta su a ciki…

Cigaba Da Karantawa

Idan Muka Fallasa Masu Ɗaukar Nauyin ‘Yan Bindiga Kowa Sai Ya Firgita – Buhari

Fadar Shugaban kasa ta ce gwamnatin tarayya ta gano wadanda ke daukar nauyin Boko Haram da ‘yanbinda da zai girgiza jama’a. Fadar, ta ce akwai alaka tsakanin masu daukar nauyin masu satar jama’a, ‘yanbindiga da kuma Boko Haram. A cewar mai Magana da yawun shugaban kasa Muhammadu Buhari, Mallam Garba Shehu, daga cikin masu daukar nauyin ‘yanta’addar, akwai ‘yan kasuwar musayar kudi da ke da jama’a a kasashen waje. Ya ce akwai shaidar da ke tabbatar da ana turo kudi daga Hadaddiyar Daular Larabawa, zuwa ga shugabannin kungiyar Boko Haram.…

Cigaba Da Karantawa

Jirgin Yaƙin Najeriya Ya Yi Ɓatan Dabo

Wani jirgin yakin sojojin saman Najeriya, samfurin Alpha Jet, wanda ake kai wa Boko Haram hari da shi, a Jihar Barno ya bace. Mahukuntan sojojin sama ne su ka bayyana haka a ranar Alhamis din nan da safe. Kakakin Hukumar Sojojin Saman Najeriya, Edward Gabkwet ya ce jirgin samfurin Alpha Jet ya bace daga idanun na’urar hangen jiragen sama, wato ‘radar’. Air Commodore Gabwet ya kara da cewa jirgin yakin ya bace, “yayin da ya ke kai farmakin agaza wa sojojin kasa a batakashi da Boko Haram a Arewa maso…

Cigaba Da Karantawa

Bauchi: Uwargidan Gwamna Ta Yi Gargadi Akan Kyamatar Masu Tarin Fuka

Uwar gidan Gwamnan jihar Bauchi, Hajiya Aisha Bala Mohammed tayi Gargadi ma al’umma da su guji nuna kyaman masu dauke da chutar Tarin fuka Tayi wan nan gargadin ne a taron tunawa da ranar Tarin fuka na Shekarar 2021 Wanda hukumar kulawa da ciwon sida da Tarin fuka da kuturta ta Jihar, da hukumar tallafin kasar Amurka (USAID) ta shirya aka gudanar a Jihar Bauchi Aisha tace abunda ma dauke da cutar yake so shine kauna da soyayya wanda hakan zai basu kwarin gwiwa wajen tunkarar yin magani sosai Uwar…

Cigaba Da Karantawa

Za A Kashe Biliyan 396 Wajen Sayen Rigakafin Korona – Ministar Kuɗi

Gwamnatin Tarayya tana tsara kashe Naira biliyan 396 don yin allurar rigakafin Korona a shekarar 2021 da 2022, domin shawo kan matsalar cutar wadda ke addabar Duniya gaba ɗaya. Ministar Kasafin Kudi da Tsare-tsaren Kasa, Zainab Ahmed ce ta bayyana hakan a ranar Laraba bayan taron mako-mako na Majalisar Zartarwa ta Tarayya, wanda Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta. Zainab ta bayyana cewa wannan adadi na iya raguwa matuka kasancewar Gwamnatin Tarayya na karbar karin gudummawar allurar rigakafin daga kamfanoni masu zaman kansu. Ministar Kuɗin ta ƙara da cewa…

Cigaba Da Karantawa

Tsohon Gwamnan Babban Banki Ya Tsallake Rijiya Da Baya

Rahotanni daga jihar Anambra na bayyana cewar wasu ‘yan bindiga ɗauke da manyan Bindigogi sun budewa tsohon gwamnan babban bankin Najeriya kuma dan takaran kujerar gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo, wuta. ‘Yan Bindigar sun yi nasarar kashe jami’an yan sanda uku dake gadinsa, sannan suka raunata wasu jama’a da dama. Wannan hari ya faru ne a garin Isuofa, a karamar hukumar Aguata a jihar Anambra yayinda yaje ganawa da wasu matasa a yankin a cigaba da tallata kanshi da yake yi na takarar gwamnan Jihar. Shaidun gani da ido sun…

Cigaba Da Karantawa

‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Gidan Jarumin Fina-Finan Hausa

Wasu ‘yan Bindiga dauke da muggan makamai sun shiga gidan wani fitaccen jarumin fina-finan Kannywood, Nasiru Bello Sani, wanda aka fi sani da Nasiru Naba da misalin karfe 1:00 zuwa 2:00 na safiyar Laraba. Sun kuma yi awon gaba da sabuwar motar da ya saya kirar SUV da sauran kayayyaki masu daraja. Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Naba ya shaida wa manema labarai cewa ‘yan Bindigar wadanda ke dauke da bindigogi, sun shiga gidansa da ke Maidile a cikin garin Kano da karfin tuwo. Sannan suka tafi da sabuwar…

Cigaba Da Karantawa

Shugabancin Kasa: Duk Wanda Ya Haura 70 Ya Ja Da Baya – Matasan Arewa

Kungiyar cigaban Matasan Arewacin Najeriya jihohi 19 har da Abuja, ta yi tsokaci dangane da halin da siyasar kasar nan ke fuskanta inda ya zamana tsofaffi ne ke ta karba-karba a tsakaninsu tare da yin watsi da matasa, bisa ga haka kungiyar ta ja layi ta bayyana ba zata lamunci haka ba, lallai duk tsohon da ya haura 70 ya koma gefe kawai. Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata takardar sanarwa wadda ta samu sanya hannun Shugaban Ƙungiyar na kasa Alhaji Imrana Nas kuma aka rarrabata ga manema…

Cigaba Da Karantawa