Kotu Ta Ɗage Shari’ar Zakzaky Zuwa Karshen Watan Biyar

Alkalin Kotun dake saurarar shari’ar jagorar ‘yan Shi’ar Najeriya Sheikh Ibrahim Zakzaky a Kaduna Mai Shari’a Gideon Kurada a zaman da Kotun ta yi a yau Laraba ya ɗage cigaba da saurarar ƙarar har ya zuwa ƙarshen watan biyar ranar 25 ga watan Mayu dake tafe. Da yake jawabi ga manema labarai jim kaɗan bayan kammala zaman shari’ar Dari Bayero, babban lauyan da ke jagorantar ‘shari’ar sirri’ na jagoran ‘yan Shi’ar da matarsa Zeenat, ya roki Babbar Kotu da ta dakatar da tuhumar ta yanke masu hukunci kamar yadda doka…

Cigaba Da Karantawa

‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Mahaifar Atiku Abubakar

Rahotanni daga garin Jada ta Jihar Adamawa Mahaifar tsohon mataimakin Shugaban kasa kuma ɗan takarar Shugabancin ƙasa ƙarƙashin jam’iyyar PDP Atiku Abubakar na bayyana cewar wasu mahara dauke da bindiga sun kaddamar da wani hari a tsakar dare a garin Kojoli da ke karamar hukumar ta Jada inda suka yi awon gaba da wasu mazauna garin biyu. Wani dan asalin garin, Dokta Umar Ardo, ya ce ‘yan bindigan sun isa garin ne da misalin karfe 1 na safiyar Lahadi kuma suka yi awon gaba da wasu fitattun mutane biyu bayan…

Cigaba Da Karantawa

Ƙetare: An Yi Yunƙurin Juyin Mulki A Nijar

A cikin daren Talata wayewar yau Laraba, da Misalin Karfe 3 ne aka jiyo harbe- harbe a fadar gwamnatin kasar jamhuriyar Nijar da ke a babban birnin Yamai. Rahotanni sun nuna cewa an kwashe sama da mintoci 15 ana jin harbe-harben kafin daga bisani abin ya lafa. Ya zuwa yanzu dai babu wani cikakkyen karin bayani akan abin da ya wakana. Amma rahotannin sun nuna cewa kura ta lafa komai na tafiya dai dai kamar yadda aka saba. Masu sharhi kan lamurran yau da kullum na ganin daga irin wadannan…

Cigaba Da Karantawa

Ni Ba Wakilin ‘Yan Bindiga Bane – Dr.Gumi

Mashahurin Malamin addinin Islama nan mazaunin garin Kaduna Sheikh Ahmad Abubakar Mahmoud Gumi ya fito fili ya fahimtar da jama’a matsayinshi na shiga tsakanin ‘yan Bindiga da gwamnati, inda ya fayyace cewa shi ba wakilin ‘yan Bindiga bane kamar yadda wasu jama’a ke bayyanawa. Dr. Gumi ya faɗi haka ne ya yin da tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya kai masa ziyara a gidan shi dake Kaduna ranar Talata. Shehu Sani ya kaima malamin ziyara ne domin tattauna batun akan ɗalibai 39 da aka sace a makarantar koyon…

Cigaba Da Karantawa

Kaduna: An Daina Ganin Ɗan El Rufa’i A Makarantar Gwamnati

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar tun bayan da aka koma karatu a wannan zangon, Abubakar El-Rufai, dan gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, bai koma makaranta ba, kamar yadda sauran ‘ya’yan talakawa suka koma. Indai jama’a basu manta ba a shekarar 2019, gwamna El-Rufa’i ya kai yaronsa makarantar Kaduna Capital School bayan alkawarin da yayi na cewar zai kai ɗaya daga cikin ‘ya’yan shi makarantar Gwamnati idan ya lashe zabe a shekarar 2019. An samu labarin cewa rashin zuwan yaron makaranta ba zai rasa alaka da matsalar tsaro da…

Cigaba Da Karantawa

Ganin Likita A Landan Al’adar Buhari Ce Tun Kafin Zama Shugaban Kasa – Shehu

“Babban abin da ya kamata jama’a su sani shine Buhari ya kasance yana zuwa duba lafiyar shi a birnin Landan tun kafin ya zama shugaban ƙasa a shekarar 2015, bisa ga haka babu dalilin surutan da jama’a ke yi akan fitar shugaban”. Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya bayyana hakan lokacin da yake ƙarin haske akan fitar da Shugaban ƙasa Buhari ya yi zuwa birnin Landan domin ganin Likita. Shehu ya bayyana hakan ranar Talata yayinda yake hira da manema labarai lokacin da jirgin Buhari ya tashi…

Cigaba Da Karantawa

Tuntuben Harshe Na Yi A Batun Daukar Matasa Miliyan 50 Soja – Tinubu

Jagoran jam’iyyar APC na kasa Alhaji Bola Ahmad Tinubu, ya yi gyaran fuska akan kalamin da yayi na a ɗauki sojoji matasa Miliyan 50 aiki, inda ya ce ba yana nufin gwamnatin tarayya ta ɗauki matasa 50 miliyan aikin soja ba, 50,000 yaso faɗa bakinsa ya kuɓuce. Bola Tinubu yayi gyara kalamansa ne a ranar Talata inda yace suɓutar baki ne yasa ya faɗi haka amma shi mutum 50,000 ya so cewa, a domin haka ya bukaci jama’a suyi mishi uzuri. An ga Tinubu na faɗa a wani bidiyo da…

Cigaba Da Karantawa

Ganin Likita: Ba Dole Bane Buhari Ya Mika Mulki Ga Osinbajo – Fadar Shugaban Kasa

Fadar Shugaban kasa ta fito fili ta yi ƙarin haske dangane da surutan da jama’a ke yi akan wajabci ko rashin wajabcin shugaban ƙasa Buhari ya miƙa mulki ga mataimakinshi Osinbajo a yayin tafiya ganin likita, inda ta bayyana cewar ba dole bane shugaban ya yi haka. Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya bayyana hakan a ranar Talata lokacin da ya bayyana a matsayin bako a shirin Politics Today na gidan talbijin din Channels. Ya yi bayanin cewa Shugaba Buhari bai sabawa…

Cigaba Da Karantawa

Ganin Likita: Ba Dole Bane Buhari Ya Mika Mulki Ga Osinbajo – Fadar Shugaban Kasa

Fadar Shugaban kasa ta fito fili ta yi ƙarin haske dangane da surutan da jama’a ke yi akan wajabci ko rashin wajabcin shugaban ƙasa Buhari ya miƙa mulki ga mataimakinshi Osinbajo a yayin tafiya ganin likita, inda ta bayyana cewar ba dole bane shugaban ya yi haka. Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya bayyana hakan a ranar Talata lokacin da ya bayyana a matsayin bako a shirin Politics Today na gidan talbijin din Channels. Ya yi bayanin cewa Shugaba Buhari bai sabawa…

Cigaba Da Karantawa