Neja: PDP Ta Dakatar Da Babangida Aliyu

Jam’iyyar PDP reshen jihar Neja ta dakatar da tsohon gwamnan jihar Dr Mu’azu Babangida Aliyu kan zarginsa da cin amanar jam’iyyar da hakan ya haifar da rabuwan kai a jam’iyyar tun 2014. Hakan na cikin sanarwar bayan taro da jam’iyyar ta fitar a karshen taron gaggawa na masu ruwa da tsaki da ta gudanar a garin Minna a ranar Litinin, Daily Trust ta ruwaito. Sakon bayan taron da mutum 22 suka rattaba wa hannu a kai ya ce an dauki matakin kan tsohon gwamnan ne bayan shigar da korafi shida…

Cigaba Da Karantawa

Wasanni: Wasanmu Da Madrid Akwai Hatsari – Kloop

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Jurgen Klopp, ya bayyana cewa wasan da zasu fafata da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid a gasar cin kofin zakarun turai mai hatsari ne kuma komai zai iya faruwa a faftawar da kungiyoyin zasu fafata. Tun bayan da hukumar kula a kwallon kafa ta nahiyar turai ta fitar da jadawalin yadda za’a ci gaba da buga wasannin cin kofin zakaru na nahiyar turai aka kuma hada Liverpool da Real Madrid aka fara bayyana yadda wasannin zasu kasance ganin cewa Liverpool din a wannan…

Cigaba Da Karantawa

Likitoci Sun Yi Barazanar Tsunduma Yajin Aiki

Ƙungiyar likitoci ƙasar nan sun yi barazanar zasu tsunduma yajin aiki matuƙar gwamnatin ƙasar nan bata biya musu buƙatunsu ba. Ƙungiyar tace zata saurari gwamnati daga nan zuwa ɗaya ga watan Afrilu idan ba’a biya musu buƙatun su ba zasu shiga yajin aiki, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito. A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar bayan babban taron ta na ƙasa, ƙungiyar ta bayyana cewa buƙatun nata sun haɗa da biyan likitoci albashin su da aka riƙe.Da kuma biyan albashin watan Maris da muke ciki kafin 31 ga watan Maris…

Cigaba Da Karantawa

An Cafke Dillalin ‘Yan Bindiga

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya (NDLEA) ta bayyana cewa ta yi nasarar cafke wani tsoho dan shekara 70 da ake zargi dai kai wa ‘yan bindiga da ‘yan Boko Haram miyagun kwayoyi. Hukumar NDLEA ta ce tsohon na zuwa ne daga jihar Agadez ta Jamhuriyar Nijar inda daga nan yake shigo da kwayoyin cikin kasar ta Najeriya. Cikin wata sanarwar da hukumar ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce, tsohon mai suna Muhammad Rabi’u Wada da ke kai wa Boko Haram da ‘yan bindiga kwaya…

Cigaba Da Karantawa

Korona: An Yi Kira Ga Buhari Ya Binciki Gwamnan Kogi

Ƙungiyar dake fafutukar kare haƙƙin bil’adama da saka ido kan al’amuran kuɗi (SERAP) ta roƙi shugaba Buhari ya yi bincike kan yadda aka karkatar da Naira Biliyan 4.5 kuɗin tallafin korona a Jihar Kogi. Gwamnatin tarayya ta tura ma gwamnatin jihar Kogi Naira Biliyan 4.5 da ta samu daga rance, da kuma gudummuwa da ta samu don yaƙi da cutar COVID-19, kamar yadda aka ake wa sauran Jihohi. SERAP ta bayyana haka ne a wani jawabi da ta fitar ranar Asabar inda ta roƙi shugaba Buhari da yaba Ministan shari’a…

Cigaba Da Karantawa

Ya Zama Dole Mu Hada Hannu Wurin Ceto Najeriya – Atiku

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar kuma ɗan takarar Shugabancin ƙasa ƙarƙashin jam’iyyar PDP a zaben 2019 da ya gabata, ya ce halin da Najeriya ta tsinci kanta a ciki yanzu ba abu ne da za a zura ido kawai ana kallo ba, ya zama wajibi a tashi tsaye a taimakawa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari domin fidda A’i daga rogo. Wazirin na Adamawa Atiku Abubakar ya bayyana haka ne a cikin wata makala da ya gabatar mai taken: ‘Matsakaicin rashin aikin yi mafi girma a Duniya: Lokaci Don Taimakawa Wannan…

Cigaba Da Karantawa

Najeriya Za Ta Fita Daga Matsalar Tsaro Idan An Zabi Jajirtattun Shugabanni – Kyari

An bayyana cewar ko shakka babu Najeriya za ta fita daga cikin ƙalubalen matsalar tsaro da take fama dashi muddin ‘yan Najeriya suka zaɓi jajirtattun shugabanni waɗanda suka dace a shekarar zaɓe ta 2023. Sanata mai wakiltar mazaɓar Borno ta Arewa Sanata Abubakar Kyari ya bayyana hakan a cikin tattaunawar da aka yi da shi a cikin shirin ‘State Of The Union’ wanda gidan talabijin na Liberty Abuja ke gabatarwa a karshen mako. Kyari ya ƙara da cewar makomar tsaro na hannun ‘yan Najeriya ta hanyar zaɓen Shugabannin da suka…

Cigaba Da Karantawa