Da Dumi-Dumi: Ba A Ga Wata Ba Za A Yi Azumi 30 Ne – Fadar Sarkin Musulmi

“Ba mu samu rahotan ganin Wata ba a Nijeriya, don haka a cika Azumi talatin a yi Sallah ranar Lahad” Cewar Fadar Sarkin Musulmi. Wata majiya daga fadar Sarkin Musulmin ta sanar da cewa, a dukkanin yankunan da akace an ga wata, babu wani Hakimi ko shugaba daga yankin da ya kira fadar Sarkin Musulmin ya tabbatar da cewa an ga wata. Daular Musulunci ta Saudiyya ita ma ta bada sanarwar cewa ba a ga wata ba a kasar, saboda haka za a cika azumi talatin ne a tashi da…

Karanta...

Tallafin CORONA: Zamu Rabawa Jihohi Naira Bilyan 200 – Ministar Kudi

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa jihohin Najeriya sun samu tallafin Dala Biliyan 1.5 daga bankin Duniya na tallafin cutar Corona virus. Ministar kudi, Zainab Shamsuna Ahmad ce ta bayyana haka ga manema labarai a ganawar da ta yi da su jiya Alhamis bayan ganawar da kwamitin tattalin arziki ya yi. Ministar Ta bayyana cewa bankin Duniyar ya lura da cewa akwai matsalar tattalin arziki dake fuskantar Najeriya, dan hakane ya ce zai baiwa Jihohin Dala Biliyan 1.5. Ta kara da cewa ana tsammanin zuwa nan da watan Satumba za’a Rabawa…

Karanta...

CORONA: Zamu Mayar Da Yaki Da Cutar Hannun Gwamnoni – Buhari

Kwamitin da fadar shugaban kasa ta kafa a kan yaki da cutar korona PTF, ya ce a yayin da zai ci gaba da hadin gwiwa tare da gwamnonin jihohi, ya kuma fara shirin sauya salon daukar mataki na gaba a kan annobar, Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito. Kwamitin zai dage a kan mayar da akalar yaki da cutar korona a hannu gwamnoni, domin su ci gaba da cin gashin kansu wajen daukar matakai na dakile annobar. Babban jami’i a kwamitin da fadar shugaban kasa ta kafa, Sani Aliyu, shi…

Karanta...

Na Yi Zaton Iskanci Zai Yi Shi Yasa Na Kashe Shi – Amaryar Da Ta Kashe Angonta

An kama wata budurwa ‘yar shekara 18 a duniya da laifin kashe mijinta da yaje zai kwanta da ita a jihar Bauchi, inda tace bata san cewa jima’i wajibi bane idan anyi aure, shi yasa ta kashe shi, domin tayi tunanin fyade zai yi mata. Yarinyar mai suna Salma Hassan, wacce ke zaune a Itas-Gadau, an kai ta ofishin ‘yan sanda na Bauchi a ranar Talata 19 ga watan Mayu, da laifin kashe mijinta da wuka kwanaki 11 kacal bayan aure. Ta bayyanawa manema labarai cewa lokacin da mijinta ya…

Karanta...

Bala’in CORONA: Tilas Arzikin Najeriya Ya Karye – Ministar Kudi

Hasashe da bincike na tsimi da tanadi da hukumar kiddiga ta Nijeriya ta gudanar ya nuna tattalin arzikin Nijeriya zai shiga halin tabarbarewa da kashi -4.4 saboda annobar Coronavirus, kamar yadda Premium Times ta ruwaito Ministar kudi, Zainab Ahmad ce ta bayyana haka ga manema labaru bayan kammala taron majalisar tattalin arzikin kasa daya gudana a ranar Alhamis. Hukumar kididdig ta gudanar da bincike, kuma sakamakon binciken ya nuna tattalin arzikin Najeriya za ta shiga mawuyacin hali, za ta fadi da kashi -4.4. Najeriya na cikin kasashen da suka fi…

Karanta...

Shugabanci: Buhari Ka Ji Tsoron Allah – Sheikh Gombe

Fitaccen Malamin addini Sheik Kabiru Gombe ya yi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya ji tsoron Allah a irin mulkin da yakewa Nijeriya da al’ummarta. Malamin ya bayyana haka ne a wajan Tafsirin AlQur’ani wanda yake gabatarwa a Kaduna ofishin Manara TV a wannan wata na Ramadan. Sheik Kabiru Gombe ya ce “Muhammadu Buhari kiwo Allah ya baka na Nijeriya kuma dole sai ya tambayeka yadda ka tafiyar da kasar nan. Ya ce “kai sani cewa ranar tashin kiyama Allah zai tsaida kai gabansa ka fadi irin adalcin…

Karanta...