CORONA: Kowa Ya Yi Sallar Idi A Gidanshi – Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III da Kungiyar Jama’atu Nasril Islam, sun umarci daukacin Musulmin Najeriya kowa ya gudanar da Sallar Idi a gida, gudun yaduwar cutar Coronavirus. Cikin wata sanarwar da JNI ta fitar ta hannun Babban Sakatare Khalid Aliyu, ya ce tunda an hana cunkoson jama’a cikin har da gwamutsuwar jama’a a wuraren ibada, ya kamata Musulmi su bi wannan umarni, domin kawar da wannan cuta ta Coronavirus. PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa Majalisar Kolin Addinin Musulunci ta umarci a fara duban watan 1 Ga Shawwal a ranar…

Karanta...

Tsohon Direban Buhari Ya Samu Tallafin Bayin Allah

Wani Bawan Allah Ya Tallafawa Tsohon Direban Shugaba Buhari Da Kayan Abinci Da Kuma Naira Dubu Dari Wannan abincin da kuke kallo da hoton wannan mutumin mai suna Sani Adamu tsohon Soja ne kuma direban shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu tallafin abince daga Kwamandan rundunar G.O.C Maiduguri a jiya Laraba, inda aka kawo masa har gida da dubu dari N100.000. Allah ya saka masa da alkairi. Idan ba s manta ba, a shekarun baya ma uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta tallafa masa da kayan abinci. Daga Comr Khalid…

Karanta...

Zamu Zama Gatan Almajirai A Kasar Nan – Gwamnonin Borno Da Yobe

Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya bayyana cewa ba za su kori duk wani almajiri da ba dan asalin jihar ba, maimakon haka za su yi gyara ne a harkar ta almajiranci, saboda su ma yara almajiran ‘ya’yansu ne. Gwamna Buni ya kara da cewa jihohin Borno da Yobe cibiyoyi ne na neman ilmin addini a tarihance, don haka gwamnatinsa ta shirya yi wa harkar almajiranci kwaskwarima. Idan ba a manta ba a ‘yan kwanakin nan, Gwamnatin jihar Borno ma na tuna cewa ba za ta kori almajirai…

Karanta...

Likitoci Sun Tsunduma Yajin Aikin Sai Baba Tagani

Kungiyar likitocin Najeriya, NMA, reshen jahar Legas ta umarci yayanta su fara yajin aikin ‘baba ta gani daga karshe 6 na yammacin Laraba, 20 ga watan Mayu. Daily Trust ta ruwaito likitocin sun dauki wannan mataki ne biyo bayan cin zarafin su da jami’an Yansanda suke yi a kan hanya, musamman yayin da suke tafiya wajen aiki. Shugaban kungiyar, Saliu Oseni ne da sakatarensa Ramon Moronkola ne suka sanar da haka cikin wata sanarwa da suka fitar inda suka ce: “Duk wani likita dake karkashin kungiyar NMA reshen jahar Legas…

Karanta...

CORONA: Sarkin Bauchi Ya Soke Hawan Sallah

Mai martaba sarkin Bauchi, wanda shine shugaban masu sarautar gargajiya na jihar ya soke hawan daba a yayin sallar Idi mai zuwa. Basaraken ya bada wannan umarnin ne yayin taron da yayi da masu ruwa da tsaki a kan annobar COVID-19 wanda aka yi a masaukin bakin gwamnatin jihar, jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito. Ya ce akwai babbar bukatar hana taro mai yawa don kowa abun zargi ne a kan cutar coronavirus. Rilwanu ya kara da cewa, za a wayar da kan dukkan limaman jihar a kan yadda za su…

Karanta...

Yakar CORONA: Najeriya Ta Karbi Dala Milyan 33 Daga Amurka

Gwamnatin kasar Amurka ta baiwa Najeriya kyautar zambar kudi $33m, kimanin naira biliyan 12.89 kenan a matsayin tallafin yaki da annobar Coronavirus a kasar. jakadiyar Amurka a Najeriya, Mary Beth Leonard ce ta bayyana haka a ranar Laraba yayin hira da ta yi a wani gidan rediyo Lagos Talk 91.3FM. Mary ta ce zuwa yanzu Amurka ta tallafa ma kasashen duniya da dama da kudi dala biliyan 2, duk a kokarinta na ganin an hada karfi da karfe wajen shawo kan cutar. Haka zalika ta kara da cewa Amurka da…

Karanta...

CORONA: Masu Biredi Sun Yi Barazanar Kara Farashi

Masu gidajen biredi na jihar Legas sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta shiga lamarinsu a kan yadda kayayyakin aikinsu ke tashi. Hakan zai iya shafar farashin biredin da karin kashi 60 a nan kusa. Masu gidajen biredin sun koka a kan cewa kayayyakin sun tashi ne sakamakon annobar COVID-19 da ta zama ruwan dare, kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa. A wata takarda da shugabannin kungiyoyin na jihar Legas, Kwamared Taiwo Akintola da Kwamared Ibitoye Oladapo suka saka hannu, kungiyoyin sun nuna damuwarsu matuka a kan halin…

Karanta...

Borno: Zulum Ya Amince Ayi Sallar Eidi

Kwamitin yaki da muguwar cutar korona ta jihar Borno karkashin shugabancin mataimakin gwamnan jihar, Umar Usman Kadafur, ya bayyana amincewarsa a kan yin sallar idi na wannan shekarar a jihar. An kai ga wannan matsayar ne bayan Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya bada umarnin tuntubar Shehun Borno tare da yin taron malamai da limamai na jihar don samun matsaya. Daga nan ne aka samu matsaya tare da gindaya wasu sharudda sannan amincewar ta biyo baya. Kamar yadda kwamishinan lafiya na jihar Borno, Salihu Aliyu Kwaya Bura ya…

Karanta...