Birnin Gwari Ya Dace Ka Tare Ba Kano Ba – Ganduje Ga El Rufa’i

A jiya ne gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa ranar Sallah da kansa zai je ya tare hanyar Kano dan kar kowa ya shigar masa jiha daga Kanon. Gwamnan ya bayyana hakane a yayin jawabin da yayiwa mutanen jihar tasa, kamar yadda Wakilin Jaridar Muryar ‘Yanci ya saurara. Saidai ga dukkan alama wannan magana ba tawa bangaren gwamnatin jihar Kano dadi ba inda daya daga cikin hadiman gwamna Ganduje wani ya mayar wa da gwana El-Rufai martani. Hadimin gwamnan Kano kan kafafen sada zumunta, Abubakar Aminu…

Karanta...

Buhari Ya Kori Shugaban Hukumar Bada Wutat Lantarki

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sallami manajan daraktan Hukumar Rarraba Wutar Lantarki ta Nijeriya (TCN). Ministan wutar lantarki, Mohammed Sale ne ya amince da sallamar a ranar Talata inda ya nada Sule Abdulaziz don aiki a matsayin mukaddashin shugaban. Daga cikin kokarin kawo gyara da saita fannin wutar lantarki na kasar nan, ministan wutar lantarki, Injiniya Sale Mamman yake sanar da manyan sauye-sauye a kamfanin rarrabe wutar lantarki na Najeriya,” Aaron Artimas, kakakin ministan ya sanar a wata takarda. An tsige manajan daraktan TCN, Usman Gur Mohammed daga kujerarsa a take.…

Karanta...

Pantami Ya Maida Martani Ga Wadda Ta Kirashi Dan Aljannah

Ministan sadarwa, Dakta Isa Pantami, ya bukaci wata matashiya ta tuba bayan ta kira da shi da dan aljanna a dandalin sada zumunta na tuwita. Matashiyar, mai suna Zainab Sani mika1 a dandalin tuwita, ta wallafa cewa, Dakta Isa Pantami Dan aljanna ne” har sau shida a shafinta. Da yake mayar da martani a kan kalaman matashiyar, Pantami ya yi ma ta wa’azi a kan cewa bai halatta a kira wani mutum da ‘Dan aljannah’ ba, tare da bayyana cewa Allah ne kadai ya san waye Dan Allah a yayin…

Karanta...

NCDC Ta Tafka Karya A Adadin Masu CORONA A Jihar Zamfara – Matawalle

Gamnatin jihar Zamfara ta bayyana rashin amincewarta da alkaluman da NCDC ta fitar na wadanda su ka kamu da cutar Coronavirus a jihar a ranar Litinin. A jiyan NCDC dai ta sanar da cewa sabbin mutane 10 sun kamu da cutar Corona a jihar ta Zamfara. Sai dai yau kwamishinan lafiya a jihar Zamfara, Alhaji Yahaya Kanoma ya shaidawa manema labarai cewa mutane biyu ne aka tabbatar da cewa sun kamu da cutar Corona a jihar Zamfara Jiya Litinin amma NCDC sukace 10. Kwamishinan yace tuni gwamnatin jihar Zamfara ta…

Karanta...