Babu Sauran ‘Yan Boko Haram A Dajin Sanbisa – Rundunar Soji

Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa Boko Haram sun tarwatse a cikin dajin Sambisa kowa ya kama gaban sa. Kodinatan yada Labaran rundunar Sojin, John Enenche ya bayyana cewa a dalilin luguden wuta da suka rika sha a maboyan su dake dajin Sambisa, yanzu mayakan boko haram din duk sun tarwatse sun dai-dai ce a dajin. John Enenche ya kara da cewa a yanzu haka sun samu bayannan sirri cewa Boko haram suna sake sabon shiri domin afkawa sansanoni da barikin sojoji dake yankin da kuma kai wa mutanen gari…

Karanta...

Kisan Tinno: Hausa/Fulani Sun Koka Da Matakan Gwamnatin Adamawa

Hausa/Fulani a garin Tinno dake karamar hukumar Lamurde a jihar Adamawa sun koka da irin sakacin da gwamnarin jihar Adamawa ta yi wajen dakile rikicin kabilanci da ya barke tsakaninsu da ‘yan kanilar Choba, wanda aka dauki tsawon awanni goma ana yi amma babu wani dauki da jami’an tsaro suka kawo. Daya daga cikin Hausawa mazauna yankin, ya bayyana cewa abin bakin ciki shine daga Tinno zuwa garin mataimakin gwamnan jihar Adamawa bai wuce kilomita biyar ba, amma duk da haka an gagara kawo musu dauki. Wanda suke zaton yin…

Karanta...

Manyan Mutane Ke Daukar Nauyin ‘Yan Ta’adda A Neja – Gwamnan Neja

Gwamnan jahar Neja, Abubakar Sani Bello ya bayyana cewa akwai wasu manyan mutane a jahar dake baiwa yan bindiga, barayin shanu da masu garkuwa da mutane bayanan sirri. Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito kimanin kananan hukumomi 5 yan bindiga suka addaba da suka hada da Rafi, Shiroro, Mariga, Lapai da kuma Munya. ‘Yan bindigan sun kashe jama’a, sun sace na sacewa sa’annan sun lalata dimbin dukiyoyi na miliyoyin nairori, tare da sabbaba dubunnan mutane yin gudun hijira. Kakakin gwamnan, Mary Noel-Berje ce ta sanar da haka a ranar Alhamis, inda…

Karanta...

Abin Boye.. An Bankado Silar Gabar El Rufa’i Da Ganduje

Malam Kabiru Sufi masanin kimiyyar siyasa ne a garin Kano. Ya shaida wa BBC cewa alakar da ke tsakanin gwamnonin biyu ta jike ne bayan Gwamna Ganduje ya yi kunnen uwar shegu da alfarmar da El-Rufai ya nema. El Rufa’i ya roki takwaran sa da kada ya tube wa amininsa rawani, lamarin da ya yi kamar ba da shi ake ba. An gano cewa manyan jam’iyyar APC sun dage wajen kokarin sulhu tsakanin Gwamna Ganduje da Sarki Sanusi amma hakan bai yuwu ba. Sufi ya ce, “Ina kyautata zaton wannan…

Karanta...

CORONA: An Mayar Da Gidajen Diezani Cibiyoyin Killace Marasa Lafiya

Hukumar yaki da cin hanci da tashawa ta Nijeriya, EFCC, ta mika gidajen da ta kwace daga hannun tsohuwar ministan man fetur, Diezani Alison-Madueke, don a yi amfani da su a matsayin cibiyoyin killace masu jinyar corona virus. Hukumar ta EFCC ta damka wa jami’an gwamnatin jihar Legas wasu gidajen ne a yau Juma’a, kamar yadda The Cable ta ruwaito. Legas, wacce ke cikin jihohin da suke kan gaba wurin yawan mutanen da suka kamu da cutar corona virus tana fama da karancin gadon asibiti don ba wa masu jinyar…

Karanta...

Corona: An Samu Karin Mutane 288 Da Suka Kamu A Najeria

Hukumar takaita yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta sanar da cewar an samu karin mutane 288 da suka kamu da cutar a fadin Najeria a yau jumma’a 15 ga watan mayun shekarar 2020. Kazalika ta fitar da adadin masu dauke da cutar a fadin kasar inda yawan su a yau yakai 5445, sannnan Wanda aka sallame su sun Kai 1320,sai Kuma Wanda suka mutu mutum 171. Ga jerin jihohin da aka samu masu dauke da cutar a yau👇🏿 Lagas – 179 Kaduna -20 Katsina -15 Jigawa- 15 Borno – 13…

Karanta...