Yadda Wani Matashi Ya Kashe Mahaifinsa Saboda Kosai

Mutanen Unguwar Gabas da ke garin Kankiya sun yi buda-baki cikin firgici bayan da wani matashi ya kashe mahaifinsa da tabarya sannan ya karya hannun mahaifiyarsa don sun hana shi daukar kosan buda-baki saboda ba ya azumi. Malam Aminu Nasiru makwabcin marigayi Rabe ne da aka fi sani da Aka ya ce, “Mahaifiyar matashin mai suna Lawal, bayan ta farfado ta shaida musu cewa, da misalin karfe 6 na yamma, tana tuyar kosan da za su yi buda-baki, sai Lawal ya shigo ya nufo inda take don dauka ya ci,…

Karanta...

Za A You Idi Da Hawan Sallah A Katsina – Masari

Duk da hauhawan da cutar Corona ke yi a jihar Katsina, Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya ce zaa dage dokar hana zirga zirga da gwamnatin jihar Katsina ta sanyawa wasu kananan hukumomin jihar Katsina da aka samu bullar annobar cutar Corona a cikin sati mai zuwa, domin al’umma su samu damar yin hidimomin saye-sayen kayan Sallah da yin Sallah idi da Kuma hawan Sallah a jihar Katsina na al’ada. Gwamna Masari ya tabbatar da hakan a lokacin da yake wata hira ta musamman da manema labarai a…

Karanta...

Hidimar Sallah: Zulum Ya Umurci A Biya Ma’aikata Da ‘Yan Fansho Albashi

Gwamnan jahar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayar da umarni a biya ma’aikatan jahar albashin watan Mayu da kudin yan fansho saboda hidimar Sallah. Jaridar The Cables ta ruwaito shugaban kungiyar kwadago ta jahar Borno, Bulama Abiso ne ya bayyana haka a ranar Juma’a, 15 ga watan Mayu. Cikin sanarwar da ya aika ma ma’aikata, Abis yace duk da dai rabin watan kawai aka ci, amma gwamnan ya bada izinin biyan kudaden don a taimaka ma ma’aikata su fara hidimar sallah. “Kungiyar kwadago ta jahar Borno na farin ciki…

Karanta...

Atiku Ya Shawarci Buhari Ya Sayar Da Jiragen Shugaban Kasa Ya Yaki Corona

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya yi la’akari da halin da kasar nan ce ciki, ya zabtare wasu kashe-kashen kudade, domin a kara samun kudin shiga, saboda yadda tattalin arzikin kasar nan ya rufta cikin wani mawuyacin hali, saboda annobar Coronavirus a duniya. A cikin wani bayani da ya fitar a shafin sa na Facebook, Atiku ya na hankalin Buhari da ya datse yawan kasafin da suka hada da: Kasafin 2020, wanda Atiku ya ce ya yi mamakin duk da irin faduwar…

Karanta...

Dole Sai Kasashen Afrika Sun Koyi Rayuwa Da Coronavirus

A wannan yanayi na annobar coronavirus, wacce a zahiri take cinye abubuwa guda: Lafiya da tattalin arziki. A bangaren lafiya, cutar tana kama mutane, wasu suna warkewa, kadan daga cikin masu cutar suna mutuwa. A babun tattalin arziki kuma, coronavirus ta samar da abinda ake kira “Lockdown” wanda yake cinye arzikin kasa kamar yadda wutar daji take cinye itace. Tun bayan 6arkewar cutar a Wuhan na kasar Chana, wasu kasashen suka fara kulle iyakokin kasarsu kamar yadda cibiyar lafiya ta duniya (WHO) ta bayar da shawara. Dokar zaman gida dole…

Karanta...

Gwamnonin Arewa Biyar Sun Bude Masallatan Jihohinsu

Daukar matakin bude masallatan baya rasa nasaba da kiraye kiraye da jama’a suka dinga yi ga gwamnatocin jahohi, musamman a yankin Arewacin Najeriya na cewa a bude Masallatai don a roki Allah. Wasu kuma na ganin ina amfanin an bude kasuwanni, inda dubun dubatan mutane ke taruwa, amma kuma a kasa bude wuraren bauta wanda basu tara jama’an da kasuwanni ke tarawa? Jihohin Arewacin Najeriya biyar da suka baiwa jama’an daman cigaba da gudanar da sallolinsu duk da matsalar Corona da ake fama da ita sun hada da…. Kogi: Gwamnan…

Karanta...

Allah Ka Saka Mana Akan Wadanda Suka Cutar Damu – Jingir

Shugaban Majalisar malamai ta kasa na kungiyar Izalah, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya ce tsagwaron son zuciya ne a hana mutane walwala da zirga-zirga. Shehin Malamin ya kara da cewa “abin takaici kai da gidanka a hana ka fitowa, kana da shago a hana ka zuwa neman abinci. Kuna da masallaci a hana ku zuwa sallah har ta kai ga ana kama Limamai ana dukansu saboda zalunci”. Ya ce “masu dukan limaman Juma’a su yi kuka da kansu. Akwai ranar da mulkin zai shude”. Sheikh Jingir a karshe ya yi…

Karanta...

Buhari Ya Amince Da Samar Da Kwalejojin Ilimi A Jihohi Shida

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da bude sabbin kwalejin horon malamai guda shidda; daya a kowanne bangare 6 na kasa. Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad, ne ya tabbatar da hakan a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter. Za a samar da sabbin Kwalejojin ne a jihohin Bauchi, Benuwe, Ebonyi, Osun, Sokoto da Edo. A wata takarda kuma da ta fito mai dauke da sa hannun babban sakataren ma’aikatar ilimi, Sunny Echono, ya ce an tsayar da ranar 11 ga watan Mayu domin ziyartar wuraren da…

Karanta...