Corona: Mun Killace Almajirai 2000 A Kano – Ganduje

Gwamnatin jihar Kano ta sanar da killace daliban makarantun allo da aka fi sani da Almajirai 2000 domin takaita yaduwar cutar Coronavirus a jihar. Kwamishanan lafiyan na jihar Kano Aminu Tsanyawa, ne ya sanar da hakan yau Alhamis a bikin kaddamar da horon ma’aikatan da za’a daurawa nauyin kula da yaran a cibiyoyin killacewan. Ya ce wadanda ake horaswa sun hada da Likitoci, ma’aikatan jinya, da masu gwajin da zasu gwada dukkan yaran. A cewarsa, an ajiye wadannan Almajirai ne a sansanin killacewa uku a kananan hukumomin Kiru, Gabasawa da…

Karanta...

Dukiyar Kasa Kawai Ake Shirin Sacewa Ba Ciyar Da Daliban Makaranta Ba – PDP

Jam’iyyar PDP tace yunkurin da gwabnatin tarayya take na fara ciyar da dalibai daga gida saboda annobar COVID-19 , bakomai bane illa damfara da sata da jagororin APC da Buhari suke suyi inda suke kokarin sace 13.5 biliyan haka kawai a banza. Jam’iyyar ta bayyana cewa abun kunyane ayi amfani da sunan yaran da basuji basu ganiba kawai don a kalmase ko sama da fadi da zunzurutun kudi har naira 13.5. kuma bazamu amince ba. Kowa ya gamsu cewa wannan shirin na gwabnatin tarayya da APC bakomai bane sata ake…

Karanta...

DUk DAN NAJERIYAN DA YA DAWO DAGA WAJE ZAI BIYA KUDIN KILLACEWA – GWAMNATI

‘Yan Najeriya mazauna ketare sun koka bisa matakin da gwamnatin kasar ta dauka na cewa duk mai son komawa gida sai ya biya kudin kula da dawainiyar killace shi. Ofisoshin jakadancin Najeriya a kasashen Kuwait da Hadaddiyar Daular Larabawa sun ce duk dan Najeriya mai son dawowa gida sai ya biya naira dubu dari biyu da casa’in da biyar da dari shida (N295,600) domin kula da shi a Najeriya kafin a dauko shi daga kasashen. Sanarwar da ofisoshin suka aika wa ‘yan Najeriya mazauna kasashen ta ce dole masu son…

Karanta...

DUK DAN NAJERIYAN DA YA DAWO DAGA WAJE ZAI BIYA KUDIN KILLACEWA

‘Yan Najeriya mazauna ketare sun koka bisa matakin da gwamnatin kasar ta dauka na cewa duk mai son komawa gida sai ya biya kudin kula da dawainiyar killace shi. Ofisoshin jakadancin Najeriya a kasashen Kuwait da Hadaddiyar Daular Larabawa sun ce duk dan Najeriya mai son dawowa gida sai ya biya naira dubu dari biyu da casa’in da biyar da dari shida (N295,600) domin kula da shi a Najeriya kafin a dauko shi daga kasashen. Sanarwar da ofisoshin suka aika wa ‘yan Najeriya mazauna kasashen ta ce dole masu son…

Karanta...

Mu Na Kashe Miliyan 679 Kullum Wurin Ciyar Da Dalibai Har Gida – Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa a kullun rana tana kashe naira miliyan 679 domin ciyar da daliban makarantar dake zaune a gida sakamakon bullar cutar covid 19 a fadin kasar Nan. Wannnan alkaluman na zuwa ne duk da cewar kashi hamsin na yara kasa da shekaru biyar dake fadin kasar na fama da karancin rashin abinci mai gina jiki kamar yadda ruhoton majalisar dinkin duniya ya nuna. Duk da makudan kudaden da gwamnatin tarayya ke kashewa a wannnan shiri nata na ciyar da daliban makarantar primary a fadin kasar nan,…

Karanta...

Malamai Sun buƙaci Ganduje Ya Buɗe masallatan Juma’ar Kano

Malaman addinin Musulunci a jihar Kano sun bukaci gwamnatin jihar ta sake bude masallatan Juma’a domin a rika gudanar da salloli kamar yadda aka saba duk mako. Rahotannin sun kara da cewa malaman sun bayyana haka ne a wata takarda da suka aike wa gwamnatin jihar. Bukatar tasu tana zuwa ne a daidai lokacin da cutar korona take ci gaba da yaduwa a jihar ta Kano Ma’aikatar lafiya ta jihar ta tabbatar cewa mutum 707 ne jumulla suka kamu da cutar korona a Kano ya zuwa ranar Laraba da daddare.…

Karanta...

Zulum Ya Janye Dokar Hana Fita A Borno

Gwamnan jihar Borno, be Farfesa Babagana Umara Zulum, ya amince da dakatar da dokar hana zirga – zirga da kulle jihar Borno sakamakon bullar annobar korona. Ya janye dokar ne biyo bayan samun gagarumar nasarar da jihar ta yi a bangaren yaki da nnobar korona. Mataimakin gwamnan Borno, Umar Kadafur, wanda shine shugaban kwamitin kar ta kwana a kan yaki da annobar a jihar, shine ya sanar da hakan a cikin wani jawabi da ya fitar a daren ranar Larabara a Maiduguri. “A cigaba da kokarin yaki tare da korar…

Karanta...

Tabarbarewar Tsaro: Shugaba Buhari Ya Kira Taron Gaggawa

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya Kira taron na gaggawa kan matsalar tsaro da ya addabi wasu yankunan kasar nan. Ko a jiya laraba Shugaba Buhari ya nuna damuwa sosai kan asarar rayuka da akayi a wasu sassan jihar kaduna katsina da wasu jihohin arewa maso gabashin kasar nan. Ko a safiyar yau majiyar Jaridar Muryar’Yanci ta jiyo Mana cewar anyi garkuwa da iyalan Shugaban jam’iyyar APC reshen jihar kaduna har gida da misalin large 1:30 na daren jiya. Wanda suka halarci taron da Shugaba Buhari ya Kira a yau sun…

Karanta...

CORONA: Gwamnatin Neja Ta Kara Wa’adin Zaman Gida

Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya sake tsawaita dokar kulle na tsawon makonni 2 a jihar inda zaa cigaba da zaman Gida. Gwamnan ya sanar da hakan ne yayin jawabi ga manema labarai jim kadan bayan taron mako-mako da yake yi da mambobin kwamitin yaki da cutar Coronavirus na jihar. Sannan ya nuna damuwarsa da yadda mazauna jihar sa ke ta ke dokar nesa-nesa da juna don dakile yaduwar annobar coronavirus. Yace Abin takaici ne yadda muka rufe iyakokinmu tsakaninmu da wasu jihohin amma kwalliya bata biya kudin sabulu…

Karanta...