An Samo Maganin CORONA A Jami’ar Ahmadu Bello Zariya

Kungiyar Farfesoshi daga sashen hada magunguna na jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria ta ce ta samo maganin cutar corona virus, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito. A yayin zantawa da jaridar Daily Trust a ranar Laraba, daya daga cikin masu binciken, Farfesa Haruna Abdu Kaita, ya ce sun samo maganin cutar COVID-19 daga tsirrai da ake samu a wasu sassan kasar nan. Kaita ya ce nan ba da dadewa ba za su fitar da maganin bayan sun tabbatar da nasararsa wajen kashe kwayar cutar a jikin dan Adam. Ya…

Karanta...

Zalunci Ne Garkame Talakawa Ba Tallafi – Nura Khalid

Babban malamin Addinin Musulunci dake gabatar da tafsiri a babban birnin tarayya Abuja, Sheikh Nura Khalid ya yi Kira na musamman ga gwamnonin kasar nan da su tabbatar sun Samar da Tallafi ga talakawan da suka zaune a gida sakamakon bullar cutar covid 19. Shahararren malamin addinin musuluncin ya Fadi hakan ne a tafsirin da ya gabatar a jiya talata inda yayi Kira na musamman ga sarkin musulmi da ya shige wa duk musulman kasar Nan gaba wurin shuwagabanni domin ganin an samu sassauci a dokar zaman gida dayake wakana…

Karanta...

Mun Shirya Tsaf Domin Maka El Rufa’i Kotu – Kungiyar Kare Hakkin Bil Adama

Wakilin kungiyar Kare hakkin ‘dan Adam (Amnesty)reshen jihar kaduna, Alhaji Musa Jika ya bayyana cewa a shirye suke su maka Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad Elrufai muddin bai biya Korarrun Sakatarorin din din da sauran Ma’ikatan da aka sallama ba bisa ka’ida ba a fadin jihar kaduna. “Alhaji Musa ya bayyana hakan ne yayin zantawa da Wakilinmu inda yace babu inda Dokar ‘Kasa ta bayyana cewar wani gwamna yana da karfin ikon ragewa Ma’ikatan gwamnati da aka sallama aiki kudaden sallama aikin su (Fansho). ” Yace a binciken da…

Karanta...

Buhari Ya Tabbatarwa Gambari Kujerar Kyari

An tabbatar da Farfesa Ibrahim Gambari a matsayin sabon ma’aikatan shugaban kasa Muhammadu Buhari. Farfesa Gambari ya kama aiki a matsayin shugaban ma’aikatan Buhari bayan an gabatar da shi a gaban majalisar zartarwa lokacin ganawarta a ranar Laraba, 13 ga watan Mayu, Channels TV ta ruwaito. Sakataren din-din-din na majalisar, Alhaji Tijani Umar, ya zaga da sabon shugaban ma’aikatan tarayyan don ganin gine-ginen fadar shugaban kasar. Taron ya fara wurin karfe 11:22 na safe inda aka fara tattaunawa a kan annobar Coronavirus da ta addabi kasar nan, jaridar Daily Trust…

Karanta...

Ba A Taba Yin Matar Shugaban Kasa A Najeriya Kamar Aisha Ba – Matasan Arewa

An bayyana Uwargidan Shugaban Kasa Aisha Buhari a matsayin wata Mace mai kamar Maza wadda ta sadaukar da rayuwarta wajen gaskiya da goyon bayanta ko akan waye. Hakika Aisha Buhari Mace ce wadda ta yi abin da ya gagari sauran Matan Shugabanni da aikatawa, domin ita kadai ce a tarihin Matan Shugabanni na Duniya data fito ta nuna damuwa da salon kamun ludayin mulkin mijinta, inda ta bukaci da Lallai a sake sabon lale yadda talaka da sauran wadanda suka wahala a siyasan za’a dama da su. Wadannan bayanai suna…

Karanta...

Zamfara: Uwargidan Gwamna Ta Raba Kayan Tallafi

Uwargidan Gwamnan jihar Zamfara Hajiya Aisha Bello Muhammad Matawalle ta kadamar da bada tallafin kayan abincin da kudin cefane ga mata domin rage musu radadin zaman gidan karkashin shirin tallafawa mata na “Women Empowemt Program” wanda Princes Dr Rabi Shinkafi ke jagoranta. Allah ka taimaki Uwar Marayun jihar Zamfara, Ka ci gaba da dafa mata a dukkan lamurranta na alhair.i Amin.

Karanta...

CORONA: Masu Cutar Sun Doshi 5000 A Najeriya

An Samu Karin Mutane 146 Masu Dauke Da Cutar A Nijeriya 57-Lagos 27-Kano 10-Kwara 9-Edo 8-Bauchi 7-Yobe 4-Kebbi 4-Oyo 3-Katsina 3-Niger 2-Plateau 2-Borno 2-Sokoto 2-Benue 1-Gombe 1-Enugu 1-Ebonyi 1-Ogun 1-FCT 1-Rivers

Karanta...

Kogi: Babu Ko Mutum Guda Da Ya Harbu Da CORONA

Gwamnatin jihar Kogi ta bayyana cewa mutane 111 da aka yi wa gwajin cutar corona virus a jihar babu ko mutum daya daga cikin su da aka samu da cutar. Kwamishinan yada labarai na jihar, Kingsley Fanwo shi ya tabbatar da hakan a garin Lokoja babban birnin jihar ta Kogi. Mista Fanwo ya kara da cewa duk da cewa an gudanar da gwajin ba tare da jami’an NCDC ba, amma sun bi duk wata ka’ida da ake bi na gwajin. Kwamishinan ya kara da cewa wannan gwaji da aka yi…

Karanta...