Karya Doka: Mun Tatsi Milyan Daya Da Rabi Wajen Talakawan Kaduna – Dikko

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce ta tara Naira milyan 1.9 a cikin kwanaki biyu na makon da ya gabata daga kudaden da take cin mutanen da suka keta dokar kullen zaman gida sakamakon bullar cutar coronavirus. Kwamishiniyar Shari’a Aisha Dikko ce ta bayyana haka a cikin wata sanarwa da ta fitar. ”Ta ce akasarin masu laifin an kama su da laifin kin sanya takunkumin rufe hanci, face mask, da kuma fitowa waje ba tare da kwakkwaran dalili ba. ”Gwamnatin ta ce ga duk wanda aka samu ya fito waje babu…

Karanta...

Nasara Akan Boko Haram: Shekau Ya Barke Da Kuka!

A cikin wani sabon sako na daukan sauti, an ji muryar jagoran kungiyar ta’adda ta Boko Haram, Abubakar Shekau, yana rusa kuka yana neman kariyar Allah daga sojojin Najeriya. A baya bayan nan, babu sassauci rundunar sojojin Najeriya ta kara kaimi wajen kai hare-hare, tare da samun jerin nasarori a kan ‘yan Boko Haram musamman a yankunan da ke gabar tafkin Chadi. Cikin sakon daukan sauti na tsawon minti daya da dakiku 22 da jaridar Daily Nigerian ta saurara, an ji muryar Shekau cikin harshen Kanuri yana neman kariyar Allah…

Karanta...

Kaduna: Kotun Tafi Da Gidanka Taci Tarar Sheikh Sambo Rigachikum

Kotun tafi da gidan ka ta jahar kaduna ta ci Sheukh Yusuf Sambo Rigachikum tarar kudi har naira dubu goma (10,000) tare da tarar dubu biyar biyar ga sauran mutanen dake motar sa, sakamakon kin sanya takunkumin kariyar Corona. Laifin da kotun ta tuhume su dashi shine rashin sa takunkumi da basu yi ba, an tare su a dai dai KASU Juction dake karamar hukumar kaduna ta arewa kamar yadda ya fadi da bakin shi a lokacin gabatar da tafseer. Tuni dai malamin ya biya tarar kudaden da akayi musu.…

Karanta...

Katsina: Sarkin Daura Ya Warke Sarai

Bayan kwashe kwana shida a asibitin kwararru na Gwamnatin Tarayya dake Katsina, Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar ya samu sauki sosai inda aka ganshi a wajen harabar dakin da yake kwance, yana hutawa cikin koshin lafiya a zaune ana kai gaisuwa kuma yana amsawa, kuma ya tashi da karfi yana tafiya. Sarkin Labarai na Masarautar Daura, Alhaji Usman Ibrahim ya bayyana mana, a lokacin da muke tattaunawa ta waya da shi dangane da sahihancin bidiyon da ke yawo a kafar sadarwa ta zamani. Ibrahim Usman ya ce…

Karanta...

Babban Labari: Gwamnatin Tarayya Zata Rage Yawan Ma’aikata

Ana iya tuna cewa, a shekarar 2011 ne tsohuwar gwamnatin shugaban kasa Goodluck Jonathan, ta kafa wani kwamitin binciken a kan yadda za a sauya fasali da takaice ma’aikatun gwamnatin Najeriya. Bayan fitowar sakamakon binciken a shekarar 2012, tsohuwar gwamnatin ta yiwa sakamakon binciken lakabi da ‘Oransaye Report 2012’, da ya biyo daga sunan wanda ya jagoranci kwamitin, tsohon shugaban ma’aikata, Mista Steve Oransaye. A yanzu gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta ba da umarni a ci gajiyar wannan bincike na takaice ma’aikatun gwamnatin tarayya a kasar gami da sauya…

Karanta...

CORONA: Buhari Ne Ya Bada Izinin Karbo Magani A Madagascar – Mustapha

Shugaba Muhammadu Buhari ya umurci kwamitin kar ta kwanan fadar shugababan kasa na yaki da cutar COVID-19 da su hanzarta karbo maganin Koronan da kasar Madagascar ta hada. Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, wanda shine shugaban kwamitin ya bayyana hakan ne a yau Litinin yayin ganawar kwamitin da manema labarai kamar yadda ta saba. ” Ya ce kasar Madagascar ta baiwa Najeriya gudunmuwar maganin ta kasar Guinea Bissau kuma tuni ma shiri yayi nisa wurin karbosu. ” Mustapha ya ce shugaban kasa ya kara da cewa sai an gwada maganin…

Karanta...

Jigilar Almajirai : Ganduje Ya Yi Maganin El Rufa’i

Gwamnatin jihar Kano ta mayar da martani ga Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad Elrufai da wasu jihohin da ke korafin cewa ta mayar musu da almajirai masu dauke da kwayar cutar korona, tana cewa ita ma ana kawo mata almajirai masu dauke da cutar korona. Gwamnan jihar kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai kan halin da kwamitin kar ta kwana kan annobar ke ciki. Gwamnan ya bayyana cewa mayar da almajirai jihohinsu na asali batu ne da aka yanke hukunci a kai…

Karanta...

CORONA: Buhari Da APC Sun Ci Amanar Najeriya – PDP

Jam’iyyar PDP tace shugaban kasa Muhammad Buhari da kuma jam’oyyar sa marar cika alkawari ta APC gaba daya sunci amanar almajirai, da kuma sauran gajiyayyu, da talakawan Najeriya bayan sun gama amfani dasu wajen samun nasara a 2015. Jam’iyyar tace sai yanzu mutane suke kara fahimtar kudirorin APC a fili musamman babban halinsu na nuna halin ko in kula ga mutane inda suka dauke talakawan Najeriya ba a bakin komai ba musamman tun daga lokacin da annobar COVID-19 ta shigo kasar nan. PDP tace wannan halin ko in kula din…

Karanta...

CORONA: An Samu Karin Mutum 242 Da Suka Harbu A Najeriya

Cibiyar takaita yaduwar cututtuka ta bayyana cewar an samu karin mutane 242 a Najeriya. Alkalumar cibiyar na nuni da cewar a halin yanzu masu dauke da cutar sun Kai 4641 a fadin kasar inda aka sallami mutane 902 yayin da mutane 150 suka riga mu gidan gaskiya. Ko a dazu jaridar Muryar ‘Yanci ta kawo maku ruhoton cewar kasar Madagascar ta aikowa Najeriya da maganin da take anfani dashi domin rigakafi da magance Cutar Corona. Karin da aka samu a yau litinin 11 ga watan mayu,ya nuna cewar jihar Lagas…

Karanta...