Dalilin Da Yasa Na Bar Siyasa – Jonathan

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan ya bayyana cewa ya janye jikinsa daga siyasa tun bayan faduwarsa zabe a shekarar 2015 ne don ya kula da gidauniyarsa. Punch ta ruwaito Jonathan ya bayyana haka ne a ranar Lahadi, 10 ga watan Mayu yayin da gwamnan Bayelsa, Duoye Diri ya rantsar da shuwagabannin jam’iyyar PDP a garin Yenagoa. Jonathan yace yana janye jikinsa daga siyasa, amma kuma ya fahimci jama’a da dama basu fahimce shi ba, saboda basu gane muhimmancin matakin daya dauka a wajen sa ba. “Kada ku karaya…

Karanta...

CORONA: Madagascar Ta Aiko Da Magani Najeriya

Jamhuriyar Madagascar ta bukaci aiko da maganin gargajiyar da take amfani da shi wajen yaki da cutar coronavirus ga Najeriya da sauran kasashen nahiyar Afrika. Kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa, ana amfani da maganin wajen kariya da kuma maganin cutar. Wakilan Najeriya sun garzaya kasar Equatorial Guinea inda za a karbo maganin tare da dauko shi zuwa Abuja. Don saukake al’amarin sufuri, a raba kasashen Afrika zuwa yankuna inda Najeriya ta fada yankin Equatorial Guinea. A daren jiya Lahadi ne Najeriya ta tabbatar da kamuwar mutum 4,399 da…

Karanta...

Tsaro: Dakarun Soji Sun Dandanawa Boko Haram Mutuwa

Dakarun Sojojin Nijeriya Sun Aika ‘Yan Boko Haram Da Dama Lahira A Jiya. Karar kwana ya fito da karnukan wutar jahannama a yammacin jiya Lahadi a garin Banki na jihar Borno inda dakarun sojojin Nijeriya suka yi wasan kura da ‘yan ta’addan ta hanyar aikasu lahira ba shiri. Yaa Allah Ka cigaba da agazawa dakarun Janar Buratai, Ka tabbatar musu da nasara akan ‘yan ta’addan Boko Haram. Amin

Karanta...

CORONA: Ya Shiga Damuwa Bayan Mutuwar Budurwarshi ‘Yar Amurka

Rai bakon duniya, wata Baturiya ‘yar shekarar 60 daga kasar Amurka ta rasu a wani Otal dake Warri bayan ta kawowa saurayinta ziyara a jahar Delta. Mai karatu, ba’a yi kuskure ba idan aka ce wannan baturiya ta kira ma saurayinta ruwa, saboda a yanzu haka yana can ido ya raina fata a hannun rundunar Yansandan jahar Delta. Kamfanin dillancin labarun Najeriya ta ruwaito matar ta mutu ne bayan da wasu alamu dake nuna ta kamu da annobar cutar Coronavirus mai sarke numfashin mutum. Kwamishinan Yansandan jahar Delta, Hafiz Inuwa…

Karanta...

Hukuncin Duk Wanda Ya Zagi Annabi Shine Kisa – Sanusi

A yayin da ake ta ce-ce-ku-ce game da masu fitowa su zagi Manzon Allah, Annabi Muhammad SAW, wasu malaman addinin musulunci sun fito sun bayyana matsayar addini. Daga cikin wadanda su ka yi magana a game da wannan batu akwai tsohon sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II wanda aka tunbuke daga gadon sarauta a watan Maris. Muhammadu Sanusi II ya na yin karatun addini a gidansa da ke Legas a cikin wannan watan Ramadan mai alfarma. A wajen karatun ne aka bijiro masa da wannan magana. Wasu Bayin Allah sun…

Karanta...