Tallafin CORONA: Har Yau Ban Ga Wanda Ya Amfana Ba – Ndume

Shugaban kwamitin soja a majalisar dattijai kuma Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa, yana mazabarsa amma har yanzu bai ga mutum daya da ya amfana da tallafin gwamnati tarayya ba. Ndume ya kara da cewa, da farko dai ya yaba irin kokarin da shugaban kasa ya keyi Muhammadu Buhari. Hakika yayi kokari sosai saboda daukar matakan gaggawa da ya yi na samar da tallafi bayan zuwan cutar Corona virus saboda musamman talakawa, masu karamin karfi yace, hakika za su shiga halin kunci. Ya kara…

Karanta...

Zamfara: Gwamna Ya Samar Da Cibiyar Killace Masu CORONA

Gwamna Bello Matawalle Maradun na jihar Zamafara ya samar da cibiyar gwaji da kwantar da masu cutar corona virus na daya a duk fadin Nijeriya. Jihar Zamfara ta samu dakin gwaje-gwajen annobar COVID19 wanda a halin yanzu aka kammala kafa na’urori da sauran kayan aikin da aikin zai bukata. Gwamnatin Jahar Zamfara ita ce jiha ta farko da ta samarda ingantattun na’urori don magance matsalar COVID19.

Karanta...

Babu Gaskiya A Rahoton Samun CORONA A Borno – Zulum

Gwamnatin Jihar Borno ta karyata ikirarin da Hukumar NCDC take yi, kan sake samun wasu mutane dake dauke da cutar Corona virus da suka kai har mutum 18 a fadin jihar. Idan baku manta ba, a jiya da dare Hukumar NCDC ta bayyana cewa adadin karin masu dauke cutar, a jihar Borno yakai 18, a lissafin kididdigar da suka fitar.

Karanta...

CORONA: Saudiyya Ta Sassauta Dokar Hana Walwala

Bayan tsawon lokaci da maka takunkumin zirga-zirga a jihohin Saudi Arabiya, mahukuntar kasar sun sassauta wannan takunkumi domin a rike bude wuraren cefanen azumi. Rahotanni daga gidan yadan labarai na Saudi Arabiya sun bayyana cewa gwamnati ta cire takunkumin sa’a 24 da ta garkama a baya, yanzu mutane za su samu damar fita. Hukuma ta bada iznin a rika bude kasuwanni da shaguna daga karfe 9:00 na safe zuwa karfe 5:00 na yamma. Hakan na nufin an ba mutane tsawon sa’a takwas domin su yi cefane. Jawabin da gwamnatin kasar…

Karanta...

CORONA: Muna Fuskantar Matsaloli A Wasu Jihohi – NCDC

Hukumar kula da cututtuka ta Nijeriya, NCDC ta bayyana cewa, tana jin takaicin yadda har yanzu akwai jihohin Nijeriya da ba su aika mata da samfurin jinin mutanen su ba dan a yi musu gwajin cutar corona virus. Shugaban hukumar, Chikwe Ihekweazu ne ya bayyana haka a hirar da ya yi da gidan talabijin din Channels TV, inda ya ce suna tsammanin kowace jiha ta ba su mutanen da za su yi wa gwajin. Zuwa ranar Juma’a jihohi 26 ne cikin 36 da babban birnin tarayya ,Abuja aka tabbatar suna…

Karanta...

CORONA: Zamu Kori Almajirai Daga Jiharmu – Gwamnatin Filato

Gwamnatin jihar Filato ta ce za ta maida daukacin almajiran dake jihar zuwa garuruwansu na asali. Gwamnan jihar Simon Lalong ne ya bayyana hakan, sannan kuma ya sassauta dokar killace jama’ar jihar daga ranar Jumma’a zuwa ranar Lahadi don su samu damar fita sayen kayan abinci kafin a komawa dokar ranar Litinin. Lalong ya ce gwamnati ta dauki matakin maida almajiran ne saboda barazanar cutar coronavirus. Malam Muhammadu Dahiru Alaramman ne a wata tsangaya a Jos, ya ce kamata ya yi da gwamnati ta tuntubesu kafin daukar wannan matakin kamar…

Karanta...

CORONA: Yunwa Na Addabar ‘Yan Najeriya

Al’ummar Najeriya na ci gaba da korafi kan yanayin da kasar ta fada na rashin wadatar abinci yayin da mahukunta ke sake tsaurara matakan dakile cutar korona. A ‘yan kwanakin nan ana samu karuwar korafin yunwa a sassa daban-daban na kasar musamman a arewaci inda galibin al’ummarta ke rayuwa irinta hannu baka hannu kwarya. Gwamnatoci jihohi da na tarayya sun ce suna daukar matakan ragewa marassa karfi radadin talauci ta hanyar rabon tallafin abinci da kudi yayin da suke ci gaba da daukar matakan shawo kan annobar. Sai dai da…

Karanta...

Mace-Macen Kano: Akwai Lauje Cikin Nadi

Bana raba dayan biyu, idan har akwai wani dan Kano dake karanta wannan dan takaitaccen rubutu nawa zai ji na sosa masa in da ke masa kaikayi, ku daure ku bani aron kunnuwan ku. Sanannan abu ne a kusan kowacce shekara lokacin shigowar damina tsakanin watan Aprilu da Maris akan samu yawaitar zazzabin cizon sauro a jihar Kano, a irin wannan lokaci duk in da ka zaga asibitoci da dakunan shan magani na Chimist-Chemis a unguwanni musamman da daddare mutane zaka tarar jingim, da sukan je domin ganin likita. Bana…

Karanta...

CORONA: Gwamnoni Sun Roki Buhari Ya Janye Dokar Ta Baci

Gwamnonin Najeriya sun yi kira ga shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sassauta dokar hana walwala da ya saka a musamman Jihohi biyu da babban birnin tarayya. Hakan ya biyo bayan ganawa da kungiyar ta yi da mataimakin shugaban Kasa, Yemi Osinbajo a wannan mako. Gwamnonin sun ce za a iya ci gaba da hana walwalan jama’a musamman daga wannan jiha zuwa waccan amma a bude gari kowa ya iya wataya wa. Sai dai kuma sun ce za ci gaba da horas da mutane da nuna musu illar cunkoso a tsakanin…

Karanta...