Yanzu Ne Ya Dace A Saki Zakzaky Da Zeenatu – Deji Adeyenju

“Abin burgewa ne da Shugaba Buhari ya bada dama tare da yin afuwa ga fursunoni guda 2,600 saboda gujewa yaduwar cutar Corona, tare da daukewa mutane kudin wuta na tsawon watanni biyu. “Wannan shine lokacin da ya fi da cewa a saki Malam Zakzaky da Matar sa, yakamata a kawo karshen bakin cikin da ‘yan Shi’a suke fama da shi” Inji shi Sama da shekaru 4 a na tsare da Malam Zakzaky cikin mawuyacin hali na rashin tabbas, mutane, kungiyoyi sun yi ta kira da a sake shi amma hukumomi…

Karanta...

CORONA: Inyamurai Sun Baiwa Gwamnatin Kano Tallafin Kayayyakin Abinci

Shugaban Kwamitin tattara tallafin cutar Corona virus da gwamnatin jihar Kano ta kafa wato Farfesa Muhammad Yahuza Bello tare da ‘yan kwamitinsa sun karbi kayan tallafi daga kungiyar masu sayar da magunguna na kabilar Ibo domin a tallafawa mabukata. Kayayyakin sun hada da: 1. Indomie katon 100. 2.Hand sanitizer 500ML ×12=120 bts. 3.5 ctns Sabulu × 15= 75bts. 4.70 packets of disposable gloves. 5.100 bags of rice. 6.50 cartons of macaroni Kayayyakin wanda kudinsu ya kai kimanin naira milyan 5.1. Daga Abubakar Aminu Ibrahim SSA Social Media.

Karanta...

Fitinar Corona Ta Tursasa Buhari Zaftare Kasafin Kudin 2020

A bisa faduwar farashin mai a kasuwannin Duniya a sakamakon barkewar annobar COVID-19, Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta na neman amincewar majalisun tarayya da su sake duba kasafin kudin 2020 daga Naira tiriliyan 10,594, 362,364,830, kamar yanda ya ke a baya zuwa ga Naira triliyon 10,276, 887,197,728. A cikin wannan sabon kasafin kudin da gwamnatin ke shawara an sami ragin Naira bilyan 317,475,167,102 a kan kasafin kudin da a ka zartar da shi a can baya, wanda kuma Shugaban Kasa ya sanya ma sa hannu. Sabuwar shawarar gwamnatin ta tarayya, wacce…

Karanta...

CORONA: Mutane Bakwai Sun Warke A Najeriya

Gwamnan jihar legas Babajide Sanwo-Olu ya bayyana cewar an sallami mutane bakwai yau wanda suka warke daga cutar covid 19. Gwamnan ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter inda Ya bayyana cewa dukkan gwaji biyun da aka yi musu na karshe na bayyana cewa basu sun warke sarai daga cutar . Gwamna Babajide Sanwo-Olu ne yayi sanarwar a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis kuma jaridar The Nation ta wallafa. Ya ce, “Jama’a nagari da ke jihar Legas, Ina farin cikin yi muku bushara daga cibiyar killacewa da kula…

Karanta...

Na Sha Kama Mijina Turmi Da Tabarya Da Matan Banza – Uwargidan Tsohon Gwamna

Florence Ajimobi, uwargidan tsohon gwamnan jihar Oyo, ta ce ta kama mijinta yana cin amanarta har sau biyu amma ta yafe mishi. Uwargidan tsohon gwamnan ta bayyana hakan ne a wata tattaunawar kai tsaye a Instagram da tayi da diyarta mai suna Bisola, yayin da take bayanin kalubalen da ta fuskanta a aurenta da tsohon gwamnan. Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, Florence ta kwatanta Ajimobi da “ragowarta” wanda dole ya dawo gareta. Ta kara da cewa maza na cin amanar matansu ne kawai ta hanyar kwanciya da matan banzan…

Karanta...

Maganin CORONA Ya Iso Najeriya Daga Chana

Bayan isowar Likitoci 15 daga kasar Sin (China) yanzu haka an sauke maganin yaki da cutar Corona virus, wanda aka kawo daga kasar ta Sin. An sauke wannan magani a filin tashi da saukar jiragen sama na Dr. Nmandi Azikiwe dake babban birnin tarayya Abuja.

Karanta...

Yakar CORONA: Za A Garkame Duk Bakon Da Ya Shigo Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna ta yi gargadin cewar yin balaguro zuwa cikin jihar ya saba wa dokokinta na kare yaduwar annobar cutar covid-19. A wata sanarwa da gwamnan jihar ya fitar a shafinsa na tuwita, ta bayyana cewa za a dakatar da matafiya a iyakokin jihar tare da basu zabin su koma inda suka taso ko kuma su fuskanci killace wa ta tsawon kwana 14 a cibiya ta musamman. A cewar gwamnatin jihar, dokar za ta fara aiki ne daga ranar Alhamis, 9 ga watan Afrilu, 2020. Tun a ranar 24…

Karanta...

CORONA: Gwamnatin Buhari Zata Fara Yin Afuwa Ga Fursunoni

A yau Alhamis 9 ga watan Maris ne gwamnatin tarayya za ta fara sakin fursunonin da shugaban kasa ya yi wa afuwa ta musamman a yunkurin ta na rage cinkoso a gidajen na gyaran hali. Za a fara sakin fursunonin ne bayan amincewar shugaban kasa Muhammadu Buhari da bukatar da ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ya gabatar masa don rake cinkoso a gidajen yarin. Gwamnatin tarayyar ta Najeriya ta dauki wannan matakin ne domin rage yaduwar cutar coronavirus a kasar. Wannan sakon na cikin wata takardar gayyata ta…

Karanta...

Yakar CORONA: Gwamnatin Bauchi Zata Rage Albashin Ma’aikata

Gwamnatin jihar Bauchi ta ce a watan Mayu da Yuni masu zuwa, ma’aikatan jihar ba za su samu cikakken albashi ba, za su sadaukar da wani kaso. Mai baiwa Gwamnan Jihar Bauchi shawara kan yada labarai Mukhtar Gidado ne ya fitar da sanarwar a yau. Ya ce kudin zai kasance gudunmuwar ma’aikatan ga gwamnati wajen yakar annobar Corona virus. Ya ce an yi yarjejeniyar haka ne a zaman da shugaban ma’aikatan jihar, sakatarorin din-din-din, diraktoci da kungiyar kwadago suka yi ranar 3 ga wannan wata na Afrilu. Yace a yarjejeniya,…

Karanta...