Tallafin CORONA: Majalisa Bata Amince Da Tsarin Ba

Shugaban Majalsar Dattawa da na Majalsar Tarayya, sun nuna rashin gamsuwa da rashin amincewa da tsarin da Ministar Ayyukan Agaji, Jinkai da Inganta Rayuwar Jama’a ta bi wajen rabon makudan kudaden da ta ce ta rabas ga talakawa domin rage musu radadin kuncin zaman gida a lokacin zaman kauce wa kamuwa da cutar Coronavirus kamar yadda Premium Times ta ruwaito. Sanata Ahmed Lawan na Majalisar Dattawa, ya nuna rashin amincewar sa a gaban Minista Sadiya Farouq, lokacin da suka gayyace ta domin ta yi musu karin haske daga kura-kuran da…

Karanta...

Abuja: Gobara Ta Tashi A Ofishin Akanta Janar

Ofishin Akanta janar na tarayya na ci ya Kama da Wuta a dazun nan. Ginin da aka fi sani da ‘Gidan baitul mali’ wato Treasury House’ na kusa da hedkwatar hukumar yan sandan Abuja, a unguwar Garki. Har yanzu ba a san abinda ya sabbaba gobarar ba duk da cewa ma’aikata na gida sakamakon dokar hana fita. Amma jami’an kwana-kwana da wasu jami’an tsaro sun shawo kanta.

Karanta...

CORONA: Talakawa Dubu 76,402 Za Su Amfana Da Tallafin Naira Bilyan 1.5 A Jigawa

Mutane dubu saba’in da shida da dari hudu da biyu (76,402) ne za su amfana da tallafin rage radadi na naira bilyan daya da dubu dari biyar da ashirin da takwas da dubu arba’in (N1,528,040,000) na tallafin gwamnatin tarayya na masu karamin karfi. Haka na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Jiha da tarayya ke yaki da annobar covid 19 dake yaduwa a fadin duniya, wanda hakan ya kawo tsanani ga al’umna sakamakon hana yaduwar ta da ya haddasa rashin gudanar da harkoki kamar yadda aka saba. Da yake…

Karanta...

CORONA: ‘Yan Agajin Fityanu Za Su Raba Sinadarin Wanke Hannu

A yayin da hukumomi da cibiyoyin kiyon lafiya suke kokarin kawo karshen yaɗuwar cutar curona virus, yan’uwan mu yan agajin kungiyar Fityanul Islam Ta Ƙasa Reshen babban birnin tarayyar Abuja suke hada sinadarin wanke hannu wato ( Senitizers) don kariya daga cutar CORONA VIRUS da kuma yadda ake dinka Face Mask duk saboda kariya daga Covid 19. Dun haɗa sinadarin wanke hannu da kuma takunkumi don su rabawa al’umma ciki da wajen abuja don kariyar daga wannan Annobar cutar curona virus wanda ta yadu a fadin duniya. Allah Ya saka…

Karanta...

Na Dawo Rakiyar Buhari – Sarkin Yakin Buhari

Daga Yau NI Abdul Ra’uf Matawalle (Sarkin Yakin Buhari) Na Dawo Daga Rakiyar Gwamnatin Karya Da Yaudara A yau na kasance mai nadama da tuba ga Allah da kuma neman gafarar ‘yan uwana ‘yan Nijeriya baki daya soboda mun sanyawa mutane soyayyar wannan Bawan Allah shugaban kasa janaral Buhari ta hanyar karya da gaskiya. Mun tallata shi duk a tunanin mu adali ne mai son talaka da kaunar talaka ne, sai dai kaico wallahi billahi a tarihin Nijeriya ba a taba gwamnati da bata kaunar talaka irin ta Buhari ba.…

Karanta...

CORONA Ta Hallaka Kwararren Likita A Jihar Katsina

An samu bullar cutar nan da ta addabi duniya mai shake numfashi watau Cutar Corona wadda ta yi sanadiyyar kashe wani likita wanda yake da asibiti mai zaman kanta a garin Daura ta jihar Katsina, mai suna Dr. Aliyu Yakubu. Gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya tabbatar da hakan a wani taron manema labarai da ya kira a gidan Gwamnatin Jihar a yammacin yau talata. Masari ya kara da cewa Dr. Aliyu ya dawo ne daga garin Lagos, bayan ya dawo daga tafiyar ne ya ji bai jin…

Karanta...

Katsina: Masari Ya Janye Dokar Hana Juma’a Saboda CORONA

Gwamnatin Jihar Katsina ta sassauta dokar hana zuwa sallar Juma’a wadda za a cigaba daga wannan makon akan wasu tsare-tsare da dokoki da ta yi kamar haka: 1. Bada dama ga wasu manyan masallatai tare da samar masu abubuwan kariya irinsu: i. Tankunan ruwa ii. Sabillai iii. Abin kariyar hanci da baki (face mask) 2. Takaita Hudubobi da Sallah domin sallamar al’uma cikin lokaci 3. An bada dama ga duk wani Masallacin Juma’a yin Sallah matukar zai tanaji duk irin abubuwan da Gwamnati ta tanada a Masallatan da taba damar…

Karanta...

Bauchi: Jami’ar Tafawa Balewa Ta Kirkiri Na’urar Kashe CORONA

Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) da ke Bauchi ta kirkiri wata na’ura da za ta taimaka wajen dakile yaduwar kwayar cutar covid-19 a Najeriya kamar yadda Daily Trust ta ruwaito. Shugaban jami’ar, Farfesa Muhammad Abdulazeez, ne ya sanar da hakan yayin da ya ke magana a wurin kaddamar da na’urar wanda aka yi ranar Talata a Bauchi. Ya bayyana cewa kirkirar na’aurar tamkar sauke nauyin da ke kan jami’ar ne a matsayinta na cibiyar bincike da kirkiro sabbin abubuwa. Farfesa Abdulazeez ya ce yanzu haka jami’ar tana kokarin kirkirar na’urar…

Karanta...

An Haramta Nuna Shirin Kwana Casa’in Da Gidan Badamasi

A ranar Talata Hukumar tace Finafinai ta jihar Kano ta fitar da sanarwa wacce shugaban Hukumar Malam Ismael Naabba Afakallah ya sanyawa hannu, wacce a cikinta aka nemi da Gidan talabijin na Arewa24 da su dakatar da haska shirin Kwana Casa’in da Gidan Badamasi har sai sun kaiwa Hukumar ta tace kamar yadda dokokin hukumar suke. Dokar hukumar tace finafinan ya yi nuni da cewa kowanne irin fim na Hausa da za a haska wanda Kanawa za su kalla, ka’ida ne hukumar tace finafinai ta tantance shi kafin al’umma su…

Karanta...