Habbatus Sauda Ce Ta Warkar Dani Daga CORONA – Gwamnan Oyo

Gwamnan jihar Oyo ta kudancin Najeriya Seyi Makinde ya ce, ya yi amfani da karas da sinadarin bitamin C da man habbatus sauda gami da zuma wajen samun galaba kan cutar coronavirus. Gwamnan ya bayyana haka ne a garin Ibadan a yayin zantawar wayar tarho da wata tashar rediyon FM da ke jihar. A makon jiya ne, gwamnan wanda ya killace kansa, ya sanar cewa, ya kamu da coronavirus bayan gwaji ya tabbatar da haka. Sai dai a shekaran jiya, gwamnan ya sake fitar da wata sanarwa, yana mai cewa,…

Karanta...

Ban Ce Babu Yunwa A Najeriya Ba – Lai Mohammed

Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya koka da yadda wasu kafofin yada labarai ke baza labaran bogi. Ya ce masu baza labaran bogin nan na yin haka ne don janye hankalin gwamnatin tarayya a kan yakar annobar coronavirus kamar yadda Channels Television ta ruwaito. Ya yi kira ga jama’ar kasar nan a kan su gujewa sauraron labaran da basu fito daga gareshi ba ko kwamitin shugaban kasar na yakar coronavirus ba. Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya koka da yadda labaran bogi ke yaduwa…

Karanta...

Kaduna: Lallai A Binciko Wadanda Suka Kashe Jama’a A Nasarawa – Rigar ‘Yanci

Ƙungiyar nan mai rajin kare haƙƙin Bil’adama ta Ƙasa da Ƙasa wato Rigar Yanci International tayi kira ga Gwamnatin jihar Kaduna cewa ta Binciko jami’an Mobile Police ɗin da suka yi Haɗaka da ‘yan ƙato da Goran Unguwar Makera Kakuri har suka kashe Sama da mutane bakwai a unguwar Nasarawa. Shugaban ƙungiyar Kwamared Mustapha Haruna Khalifa ne ya faɗi hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai da safiyar yau Talata a Ofishin ƙungiyar da ke jihar Kaduna, Inda yace idan aka yi la’akari da Adadin Mutanen da Corona…

Karanta...

Kawar Da CORONA A Najeriya: Buhari Zai Ciwo Bashin Triliyan 3.2

Ministar Harkokin Kudade Zainab Ahmed ce ta bayyana haka, ranar Litinin a Abuja, lokacin da ta ke bude asusun neman lamunin naira bilyan 500 da za a fara fafata yaki da cutar Coronavirus kamar yadda Premium Times ta ruwaito. Ta ce Najeriya ta fara tsara yadda za a ciwo bashin har na naira tiriliyan 3.2 domin gagarimin aikin kakkabe cutar Coronavirus a kasar nan. Zainab ta bayyana yadda za a ciwo bashin, inda ta ce mafi yawan kudaden za su fito ne daga Bankin Bada Lamuni na Duniya (IMF), Bankin…

Karanta...

Dakile CORONA: Ganduje Ya Tsawaita Hutu Ga Ma’aikata

Gwamnatin jihar Kano ta kara baiwa ma’aikatan ta hutun makonni biyu domin su ci gaba da zama a gida sakamakon dakile yaduwar cutar Coronavirus a fadin jihar. A jiya ne dai Gwamnatin karkashin jagorancin Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ta sanar da karin hutun. Sakataren yada labaran gwamnan Kano, Abba Anwar shine ya fitar da sanarwar mai kunshe da sa hannunsa. An dai kara kwanakin ne bayan cikar wa’adin hutun makwanni biyu wanda gwamnatin ta bayar a baya sakamakon dakile yaduwar cutar ta Coronavirus a Kano.