Bauchi: Hadarin Mota Ya Lashe Rayukan Mata Biyar

Hadarin Mota A Hanyar Bauchi Ya Halaka Mata Biyar Da Yaro Daya Yadda hadarin yammacin jiya Asabar 04/ April/2020 ya yi sanadiyar mutuwar mutane shida, mata biyar da karamin yaro tsakanin garin Zalau da Gumau dake karamar hukumar Toro a jihar Bauchi. Abdulkareem direba Zalau (Hogan) wanda yake a asibiti yanzu haka tare da wasu da suka jikkata. Hadarin ya yi muni matuka domin har da kananan yara wani ya sami karaya a kafada wani a kafa. Allah ya yi musu rahama ya sa aljnna ta zama makoma ya kyautata…

Karanta...

Na Share Boko Haram Daga Chadi – Shugaban Chadi

Shugaban Chadi Idris Deby Itno ya sanar da samun gagarumar nasara kan mayakan Boko Haram da ya ce, ya karkade su baki daya daga tsibirin Tafkin Chadi, bayan dakarunsa sun kwashe kwanaki 6 suna yi wa mayakan luguden wuta. Shugaban kasar Chadi Idriss Deby Itno wanda shi da kansa ya jagoranci farmaki a sansanonin boko haram ya yi nasara akan kungiyar ‘yan ta’addan. Shugaba Itno ya kaddamar da gagarumin harin da aka yi wa lakabi da ‘Fushin Boma’ ne bayan kisan da mayakan Boko Haram suka yi wa sojojin kasar…

Karanta...

Da Dumi-Dumi: Kyari Ya Warke Daga CORONA

Abba Kyari Ya Warke Daga Cutar Corona Virus, Bayan Ya Shafe Kusan Makonni Biyu Yana Killace Abba Kyari, ya warke daga cutar Corona Virus bayan ya shafe kusan makonni biyu a killace na kamuwa da cutar da yayi kamar yadda Daily Correspondents ta ruwaito.

Karanta...

CORONA: ‘Yan Majalisa Sun Bukaci A Daukewa ‘Yan Najeriya Biyan Kudin Wuta

‘Yan majalisar wakilai sun bayyana kudurin su na gabatar da sabon kuduri da zai saka ‘yan Najeriya su sami wutar lantarki na tsawon wata biyu a wannan lokaci da ake fama da annobar Coronavirus. A wata sanarwa da aka fitar jiya Asabar da yamma, Kakakin majalisar ya ce wannan kuduri za su gabatar da shine domin bunkasa tattalin arziki yayin da kasar ke fama da matsalar ta Coronavirus. Gbajabiamila ya bayyana hakane a dakin majalisar a jiya lokacin da aka gana tsakanin shugabannin majalisar guda biyu da ministar kudi, Zainab…

Karanta...