CORONA: Booth Zata Bada Tallafin Buhunan Shinkafa Ga Talakawa

Jarumar Kannywood Maryam Booth ta yi alkawarin tallafawa marasa karfi a wannan lokaci da cutar Coronavirus, tasa wasu jihohin suka bada sanarwar zama a gida. Jarumar ta bayyana yunkurin bada tallafin ne a shafinta na Twitter jarumar tayi hakanne don ragewa marasa karfin radadin wannan lokaci. Inda ta ce “zan bayar da buhun shinkafa guda dari (100), da kwalin magi ajinomoto guda dari (100), da kuma jarkar mai guda hamsin (50), ga marasa karfi. Tace idan kun san wani wurin ‘yan gudun hijira ku sanar dani dan Allah ta hanyar…

Karanta...

Daukar Fansa: Shugaban Kasar Chadi Ya Tunkari Boko Haram

Shugaban Kasar Chadi Idris Deby yayi hijira daga fadarsa dake babban birnin Njamena zuwa jejin tafkin Chadi, domin daukar fansar jinin sojojin kasar kusan 100 wanda ‘yan ta’addan Boko Haram/ISWAP suka hallaka a harin kwanton bauna makon da ya gabata. Ko ba komai shugaba Idris Deby ya nunawa jama’arsa tsananin kishi, ya nuna matukar damuwa da kisan sojojinsa, yayin da mu kuma sai dai a fitar da sanarwa ana jajantawa iyalan sojojin Nijeriya da aka kashe, shikenan an wuce gurin. Muna dada jawo hankalin masoyinmu Maigirma shugaban Kasa Muhammadu Buhari…

Karanta...

Daukar Fansa: Shugaban Kasar Chadi Ya Tunkari Boko Haram

Shugaban Kasar Chadi Idris Deby yayi hijira daga fadarsa dake babban birnin Njamena zuwa jejin tafkin Chadi, domin daukar fansar jinin sojojin kasar kusan 100 wanda ‘yan ta’addan Boko Haram/ISWAP suka hallaka a harin kwanton bauna makon da ya gabata. Ko ba komai shugaba Idris Deby ya nunawa jama’arsa tsananin kishi, ya nuna matukar damuwa da kisan sojojinsa, yayin da mu kuma sai dai a fitar da sanarwa ana jajantawa iyalan sojojin Nijeriya da aka kashe, shikenan an wuce gurin. Muna dada jawo hankalin masoyinmu Maigirma shugaban Kasa Muhammadu Buhari…

Karanta...

Kaduna: Limaman Da El Rufa’i Ya Kama Sun Samu Beli

Wata kotun majastare dake layin Ibrahin Taiwo, a Kaduna ta bada belin wasu Limamai 3 da suka gudanar da sallar Juma’a, duk da dokar hana zirga zirga da aka sanya a Kaduna a daidai lokacin. An bada belin Muhammad Umar, wanda ake zargin ya karya dokar gwamnatin jihar na hana zirga zirga don dalkile yaduwa cutar corona virus. An bada belin Umar ne tare da limamai Yusuf Hamza, Muhammad Ubale, da Auwal Shuaibu, wadanda ke zaune a unguwan Kanawa dake Kaduna, ana zargin su ne da laifin hada baki da…

Karanta...

Ba Malami Bane, Duk Wanda Ya Karyata CORONA – Sarkin Musulmi

Kungiyar Musulman Najeriya ta Jama’atu Nasril Islam JNI karkashin jagorancin Sarkin Musulmai ta ce jahilci ne wani malamin addini ya fito yana ikirarin cewa coronavirus karya ce. Kungiyar ta fitar da sanarwa ne ranar Litinin mai dauke da jan kunne ga malaman da sanarwar ta ce suna dulmuyar da al’umma kan cutar Covid-19 a Najeriya. Sanarwar dai martani ce ga wasu rukunin malaman addinin Islama da suka fito suna wa’azi ga mabiyansu suna karyata cewa coronavirus karya ce makirci ne, cikinsu har da wasu manyan malaman da ke da’awa. A…

Karanta...

Yakar CORONA: Sanatoci Sun Bada Rabin Albashin Su

‘Yan Majalisar Dattawan Najeriya sun sadaukar da rabin albashinsu domin tallafa wa yaki da cutar coronavirus. Kakakin Majalisar, Sanata Godiya Akwashiki ya sanar da cewa daga watan Maris da muke ciki ‘yan Majalisar za su ci gaba da bayar da bayar da rabin albashinsu har sai an magance cutar a Najeriya. Sanarwar gudunmuwar sanatocin na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan ministocin kasar sun sanar da mika da rabin albashinsu na watan Maris a matsayin tallafi ga kokarin kasar na yaki da annobar. Tallafin nasu kadan ne daga irin taimakon da…

Karanta...

Cutar CORONA: Jingir Ya Yi Amai Ya Lashe

Shugaban kungiyar Izala na kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, wanda ya ce coronavirus ba gaskiya ba ce, yanzu ya ce tabbas cutar gaskiya ce. Wata sanarwa da Shiekh Nasiru AbdulMuhyi, shugaban gudanarwa na kasa na kungiyar Jama’atu Izalatul Bidi’a wa ikamatus Sunnah ya aike wa manema labarai ranar Litinin, ta ce za ta yi biyayya ga dukkan dokokin da gwamnatin tarayya da na jihohi suka sanar domin dakile yaduwar coronavirus. “Kwamitin Koli na kasa na JIBWIS a karkashin jagorancin Ash-Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir ya sanar da bin dukkan…

Karanta...

CORONA: Gwamnan Kwara Ya Sadaukar Da Albashin Shi Na Shekara

Gwamnan Jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazak ya bayyana cewa ya sadaukar da albashinsa na watanni 10 domin ganin an dakatar da yaduwar annobar Coronavirus a Najeriya. An ruwaito gwamnan ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ya fitar da yammacin Lahadi, 29 ga watan Maris, a daidai lokacin da attajiran Najeriya suke bayar da nasu gudunmuwar domin taimaka ma gwamnati wajen yaki da cutar. A cikin wannan sanarwa da Gwamna Abdulrahman Abdulrazak ya fitar ya bayyana cewa tun daga lokacin da ya zama gwamnan jahar Kwara ba’a taba biyansa albashi…

Karanta...

Gwajin CORONA: An Bar Jaki An Koma Dukan Taiki – Gwamna Bello

Gwamnan jahar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello, ya caccaki tsarin da hukumar NCDC ke amfani dashi wajen zabar wadanda za a yiwa gwajin cutar coronavirus. Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Gwamna Bello ya bayyana a ranar Lahadi, 29 ga watan Maris, cewa mayar da hankali da aka yi kan rukunin wasu mutane da coronavirus ya kama ba daidai bane. Ya ce kokarin Najeriya wajen hana yaduwar cutar ba lallai bane ya haifar da yaya masu idanu idan har aka ci gaba da dauke idanu a kan mutane marasa galihu…

Karanta...

El Rufa’i Da CORONA: ‘Yan Majalisa Na Cikin Tashin Hankali

Rahotanni sun kawo cewa ‘yan majalisar dokokin jahar Kaduna sun shiga alhini da rudani sakamakon sanarwar da Gwamna Malam Nasir El-Rufai ya yi a ranar Asabar, na cewar sakamakon gwaji ya nuna yana dauke da cutar Coronavirus. Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa sanarwar da El-Rufai ya yi ya sanya fargaba a zukatan wasu ‘yan majalisa musamman wadanda suka yi aiki dab da dab dashi a makon da ya gabata, domin basu na san ya yi gwajin ba. Masu koro jawabi daga gidan Sir Kashim Ibrahim sun bayyana cewa wasu…

Karanta...

CORONA Ta Ziyarci Katsinawa

Hukumar lafiya wacce take kula da cutar Coronavirus (NCDC) ta ziyarci Zangon Marke dake karamar hukumar Bakori a jihar Katsina domin duba wanda ake zargi da kamuwa da cutar COVID19. An zargi mutumin ne bayan dawowar sa daga Lagos, hakan ya sa al’ummar Zangon Marke suka killace shi kafin hukumar lafiya masu kula da wannan cuta su kawo dauki. Hakan ya samu asali ne sakamokon aiki da yake karkashin wata Baturiya da yake zaune a gidanta a jihar Lagos bayan jin ta kamu da wannan sabuwar cuta shi kuma ya…

Karanta...

Kamuwa Da CORONA Ba Mutuwa Bane – Atiku

Corona virus ba mutuwa ba ce,” sakon Alhaji Atiku Abubakar ga Gwamnan Bauchi Bala Mohammed, da Nasir El-Rufai, da Muhammad Babandede, shugaban hukumar shige da fice ta Najeriya (Immigration). Duk mutanen da tsohon mataimakin shugaban kasar ya lissafo gwaji ya nuna cewa, suna dauke da coronavirus, kuma Atiku ya yaba masu saboda “bayyana kamuwa da cutar da suka yi. “Ina so na jinjina musu bisa bayyana kamuwar su da cutar da suka yi. Za mu iya kawo karshen annobar nan ta hanyar yin bayani da ilimantar da mutane da killace…

Karanta...

Na Kusan Warkewa Daga CORONA – Kyari

Shugaban ma’aikatan fadar Shugaba Muhammadu Buhari, Mallam Abba Kyari da ya kamu da kwayar cutar Covid-19 ya isa Legas kamar yadda likitocinsa suka ba shi shawara inda yanzu ya ke samun kulawa. An tafi da Abba Kyari zuwa Legas ne cikin jirgin sama na daukan marasa lafiya duk da cewa kawo yanzu bai fara nuna alamun kamuwa da kwayar cutar ba kamar yadda This Day Live ta ruwaito. A daren jiya Lahadi ne Kyari ya fitar da sanarwar cewa likitocinsa sun bayar da shawarar a tafi da shi Legas domin…

Karanta...

CORONA: Buhari Ya Kakaba Dokar Ta Baci A Abuja Da Wasu Jihohi

Buhari ya ayyana dokar hana fita a jihohin Abuja da Legas da Ogun, a jawabinsa na farko kan Coronavirus ga ‘yan Najeriya A karon farko, Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya yi wa ‘yan kasar jawabi game da matakan da gwamnatinsa ke dauka a yaki da coronavirus. Muhimman abubuwan da ya fada sun hada da: Saka dokar hana fita a Abuja da jihohin Legas da Ogun Agaza wa mutanen karkara da ke kusa da Legas da Abuja Daga wa wadanda suka ci bashin Tradermoni da MarketMoni da FarmerMoni kafa tsawon…

Karanta...