Coronavirus: Buhari Ya Bada Umarnin Rufe Dukkanin Jami’o’i Da Makarantun Sakadare

Yayin da annobar Coronavirus ke cigaba da yaduwa a duniya, gwamnatin tarayya ta umurci dukkan shugabannin jami’o’i da makarantun sakandare mallakin gwamnatin tarayya su rufe cikin gaggawa. Gwamnati ta yanke wannan shawara ne domin takaita yaduwar cutar Coronavirus da ta addabi kasashen duniya. Kawo yanzu, akalla mutane 300 sun kamu da cutar a nahiyar Afrika, yawanci wadanda suka shigo nahiyar daga kasashen Turai da Asiya. Sakataren din-din-din na ma’aikatar Ilimi, Sonny Echonu, ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis inda yace an dauki matakin ne domin kare rayuwar daliban makaranta.…

Karanta...

Coronavirus: Fushin Allah Ne Ya Sauka A Duniya – Daurawa

An dade ana gamuwa da ibtila’i da jarrabawa a fadin duniya, kwalara da Annoba da yaduwar cutaka ya dade yana addabar duniya, Kuma ana yi masa farrasa iri iri, kowa gwargwadon abinda yake dauke da shi na akida, ko hankali, ko ilmi ko al’ada, ko surkulle. Amma mu a mahanda ta addini muna daukar wadananan a matsayin jarrabawa da Jan kunne da Allah yake yiwa mutane domin su saduda, su sallamawa Allah, su yadda wananan duniya akwai me ita, Kuma yana da iko akanta kuma zai Iya tashin ta duk…

Karanta...

Kurungus: Babu Coronavirus A Katsina – Ma’aikatar Lafiya

Ma’aikatar kiwon Lafiya ta jihar Katsina ta tabbatar da wani malamin Jami’ar Gwamnatin Tarayya dake Dutsinma da aka yi masa zargin kamuwa da cutar coronavirus, a halin yanzun an tabbatar ba shi da cutar kwata-kwata. A lokacin da yake zantawa da manema labarai game da gwajin da aka yi masa, kwamishinan lafiya na jihar Katsina, Yakubu Nuhu Danja, ya ce an gwada an kuma tabbatar malamin bashi da cutar. A jiya ne dai hankulan ‘yan jihar Katsina ya tashi matuka sakamakon labarin da gwamnatin jihar ta fitar na cewa, an…

Karanta...

Kazafi: Kotun Shari’a Ta Gayyaci Baban Chinedu

Sakamakon maganganun da Haruna Yusuf (Baban Chinedu) yayi wadanda a cikinsu yake zargin Ismael Na’Abba Afakallah da cinye kudaden marayu, hakan ya sa shi Afakallah ya garzaya zuwa kotun Musulunci domin neman a fito da gaskiyar maganar dashi Baban Chinedu yayi akansa. Bayan da kotun wadda take a unguwar Hausawa a Filin Hocky ta saurari korafi daga mai kara, sai ta saka ranar 1 ga watan 4 na shekarar 2020 domin fara sauraren shariar. Tuni kotu ta turawa da Baban Chinedu takardar gayyata zuwa ofis dinsa dake Kano.

Karanta...

Annobar Corona: Gwamnatin Jihar Kaduna Zata Tsuke Bakin Aljihu

Gwamnatin Jihar Kaduna ta dauki matakai na tsuke bakin aljihunta saboda tunkarar taɓarɓarewar tattalin arziki sakamakon yaɗuwar cutar Korona Baros kamar yadda yake a wata sanarwa da ta fito daga gidan gwamnati na Sa Kashim ta hannun Mai Ba Gwamna Shawara a Kan Yada Labarai, Muyiwa Adekeye. Sanarwar ta nuna cewa gwamnatin ta yanke wannan shawarar ne bayan Gwamna Malam Nasir El-Rufai ya karbi rahoton daga wani kwamiti na musamman na samar da mafita na matsin tattalin arziki wanda Jimi Lawal Ke shugabanta da mataimakinsa Muhammad Sani Dattijo ya bayar…

Karanta...

Matsalar Tsaro: An Bar Jaki An Koma Dukan Taiki Ne – Sheikh Rigachikum

Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai ta Kasa na kungiyar Izalatil Bid’a Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS), Shiekh Yusuf Sambo Rigachikum, ya bayyana cewa, an bar gini tun ran zane a sha’anin matsalar tabarbarewar a Nijeriya, ya na mai cewa, hakan na da nasaba da yanayin yadda a ke daukar jami’an tsaron ne. Bugu da kari, sai ya yi kira ga al’ummar kasar da su kara hada kansu su cigaba da yin addu’a ga Allah (SWA) ya kawo karshen matsalar rashin tsaro da yanzu kasar ta ke fuskanta. Sheikh Sambo Rigachikum ya yi…

Karanta...

Zamu Hada Hannu Wajen Kawar Da Ta’addanci A Arewa – Gwamnoni

Gwamnonin yankin Arewa maso yammacin Najeriya tare da na jahar Kwara da Neja sun gudanar da wani taron gaggawa a ranar Laraba, 18 ga watan Maris a fadar gwamnatin jahar Kaduna inda suka tattauna matsalar tsaro da ta addabi jahohinsu. Daga cikin gwamnonin da suka hadu akwai gwamnan jahar Katsina, Aminu Bello Masari, na Kebbi, Atiku Bagudu, na Jigawa Abubakar Badaru, na Kaduna Malam Nasir El-Rufai na Sakkwato Aminu Tambuwal da na Zamfara, Bello Matawalle. Sauran sun hada da gwamnan jahar Kano wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Nasiru Yusuf Gawuna…

Karanta...

Cutar Corona: Ku Daina Shan Hannu Da Juna – Sheikh Bauchi

Babban Shaihi a Darikar Tijjaniyya Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya yi kira ga al’umma su bi umarnin likitoci su daina musabaha domin kauce wa kamuwa da cutar coronavirus. Malamin addinin Musuluncin ya shaida wa BBC haka ne bayan sanarwar da suka fitar ta jinkirta taron Maulidin Sheikh Nyass wanda da za a yi a Abuja da Sokoto saboda yaduwar cutar coronavirus. Sheikh Dahiru Bauchi ya ce an jinkirta Maulidin ne saboda yadda cutar ke yaduwa a makwabtan Najeriya, kuma taron maulidin ba na ‘yan Najeriya ba ne kawai, har da…

Karanta...

Buhari Ya Bada Umarnin Dakatar Da Daukar Sabbin Ma’aikata

Gwamnatin tarayya ta sanya takunkunmi kan daukan aikin yi a ma’aikatun gwamnatin tarayya gaba daya. Ministar kudi da tattalin arziki, Zainab Shamsuna Ahmed, ta bayyana hakan ne yayinda take hira da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan taron majalisar zantarwa da shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta ranar Laraba. Ta ce gwamnatin tarayya za ta cigaba da biyan ma’aikata albashi kuma ba zata sallami ma’aikata ba amma ba za’a sake daukan sabbin ma’aikata ba. Tace“Kan batun daukan aiki, an rigaya da bada umurnin dakatar da daukan aiki. Abinda ma’aikatun keyi…

Karanta...

Tsige Sunusi Ya Bamu Damar Bincikar Shi Yadda Muke So – Hukumar Yaki Da Rashawa

A ranar Laraba ne wata babbar kotun tarayya da ke zama a jihar Kano ta saka ranar 23 ga watan Maris don ci gaba da sauraron karar da tubabben sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya mika a gabanta na bukatar ta dakatar da hukumar korafi da yaki da rashawa ta jihar a kan bincikarsa. Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa, Sanusi ya mika bukatar ne gaban kotun a kan ta dakatar da shugaban Hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano Muhyi Rimingado, Antoni janar din jihar Kano da Gwamna…

Karanta...

Annobar Corona: Gwamnatin Tarayya Zata Kulle Masallatai Da Coci-Coci

Kwamitin shugaban kasa dake yaki da yaduwar cutar Coronavirus ya kafa wani kwamiti wanda zai tattauna da shugabannin addinai daga bangarorin addinin Musulunci da kuma Kiristanci don duba yiwuwar kulle wuraren ibadu. Ministan watsa labaru, Lai Muhammad ne ya bayyana haka yayin da yake bayar da jawabi game da shirye shiryen kwamitin a gidan talabijin na NTA, inda yace ba kai tsaye gwamnati za ta rufe wuraren ibada ba, har sai ta samu goyon bayan shugabannin addinai. “Bayan zaman farko na kwamitin, daga shawarwarin da aka bayar akwai bukatar kara…

Karanta...

Cutar Corona: Dan Wasan Liverpool Ya Bada Tallafin Miliyoyin Kudi

‘Dan wasa Sadio Mane na kasar Sanagal, ya bada kudi har £41,000 ga kasarsa a matsayin gudumuwa domin a yaki cutar nan ta Coronavirus da ta ke ratsa Duniya. Jaridar BBC Hausa ta bayyana wannan abin kirki da ‘Dan wasan gaban na Firimiya ya yi. Sadio Mane ya bada wannan gudumuwa ne domin a hana cutar yawo a Sanagal. Mane ya na cikin masu yunkurin kira na ganin cewa an dauki lamarin cutar da muhimmanci. ‘Dan wasan ya kan fadakar da masu bibiyarsa a shafukansa na zumunta. Kwanakin baya Mane…

Karanta...