Coronavirus: Likitoci Sun Shiga Yajin Aiki A Najeriya

Yayin da kasashen duniya ke kokarin daukar matakan kariya tareda nazari kan yadda za su shawo kan cutar Coronavirus, likitocin a babbaan birnin Tarayyar Najeriya sun sananr dafara yajin aiki a Talatar nan kamar yadda Premium Times ta ruwaito. Kungiyar likitocin Najeriya, reshen Abuja sun sanar da fara wannan yajin aikin ne sa’a guda bayan hukumomin kasar sun sanar da mutum na 3 da ya harbu da cutar ta Coronavirus a birnin Lagos. Likitocin sun ce sai da suka yi nazari sosai kan barazanar da bangaren lafiya ke fuskanta a…

Karanta...

Ilimi: Za A Fitar Da Dalibai 6000 Kasar Waje – Gwamnatin Tarayya

Hukumar kula da asususn cigaban kimiyya ta Najeriya, PTDF, ta fara tantance kimanin dalibai 6,000 da suke neman guraben samun tallafin karatu daga gwamnatin tarayya a jami’o’in kasashen waje na shekarar 2020/2021 kamar yadda Legit ta ruwaito. A cewar hukumar, fiye da mutane 25,000 ne suka nemi guraben samun tallafin a matakin digiri na biyu Msc da kuma PhD, daga cikinsu ne hukumar ta ware mutane 6,000 wadanda za ta yi ma tamyoyin gaba da gaba da kuma tantancewa. Shugaban sashin tallafin karatu na kasashen waje, Bello Mustapha ya bayyana…

Karanta...

Mashaya Sigari Sun Fi Hatsarin Kamuwa Da Coronavirus – Hukumar Lafiya

Yayin da masana kimiya ke gudanar da bincike domin samun kyakkawar fahimtar cutar Coronavirus kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta yi kira ga mutane musamman masu shan taba ko masu shakar hayakin taba da su nisanta kansu da haka cewa busa taba da shakar hayakin ta na sa a gaggauta kamuwa da cutar. WHO ta yi wannan kira ne bisa ga sakamakon binciken da masana kimiya suka gudanar a wuraren gwaji 55,2924 dake kasar Chana. Sakamakon binciken ya nuna cewa dayawa daga cikin mutanen da corononavirus ta yi mummunar…

Karanta...

Zamu Cigaba Da Farautar Sunusi – Hukumar Yaki Da Rashawa

Hukumar sauraron korafi da yaki da rashawar jihar Kano za ta sake sammatar tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, na ba da dadewa ba domin kare kansa kan zargin almundahanar kudin filin Gandun Sarki na kimanin, N2.2 biliyan. Ana zargin tsohon sarkin Kanon ne da laifin sayar da filaye a Darmanawa Phase I da II, da kuma Bubbugaji a Kano. Thisday ta ruwaito cewa a karshen makon da ta gabata, hukumar ta samu isassun hujjojin da zasu isa a sammaci tsohon sarkin kuma a kaddamar da bincike a kansa. Hakazalika,…

Karanta...

Jahilci Ne Jigon Rikicin Addini Da Na Kabilanci – Sarkin Musulmi

Mai alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya ce sarakuna da malaman addini da ya kamata su rika sanya ido kan shugabannin siyasa wajen suna yin abin da ya dace, an rufe musu baki. Sarkin Musulmi ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a wajen taron Tattaunawa a Tsakanin Addinai kan Zaman Lafiya karo na Uku na bana da aka gudanar a Abuja. Taron ma taken “Tattaunawa a Tsakanin Addinai: Karfafa Al’adar Zaman Lafiya da Adalci da Sulhuntawa, Malam Muhammadu…

Karanta...

Coronavirus: An Kulle Masallacin Qudus

Jagororin Masallaci na uku mafi falala ga mabiya addinin Islama sun alanta kulle Masallacin Qudus dake kasar Falasdin sakamakon annobar Coronavirus da ta addabi duniya. Amma sun baiwa mutane damar Sallah a harabar Masallaci. Kwamitin Waqafin Masallacin sun bayyana cewa an yanke wannan shawaran kulle cikin Masallacin har ila ma shaa Allahu domin takaita yaduwar cutar ta Coronavirus. Daraktan Masallacin, Omar Kiswani, ya bayyanawa Rueters cewa “za a cigaba da gudanar da Sallan jam-i amma harabar Masallaci. “ A baya mun kawo muku rahoton cewa Shugabancin Masallacin Harami karkashin jagorancin…

Karanta...

An Tsige Sunusi Ne Saboda Bai San Al’adun Kanawa Ba – Yakasai

Alhaji Tanko Yakasai, dan siyasa a arewa kuma daya daga cikin wadanda suka kirkiro Arewa Consultative Forum, ya bayyana dalilin da ya jawo tsige rawanin tsohon sarkin Kano, Sanusi Lamido a ranar 9 ga watan Maris din 2020. A wata tattaunawa da aka yi da shi da jaridar Punch a ranar Lahadi, Yakasai ya ce dalilin farko da yasa aka tsige rawanin sarkin shine yadda ya ke wa wanda ya nada shi sarki biyayya, wato tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso. Wanda tuni kuwa suke da tsananin rashin jituwa…

Karanta...

Mun Amince Da Dakatar Da Taron Koli Na APC – Gwamnonin APC

Gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki sun gana da shugaba Buhari a fadar Aso Rock don tattaunawa kan hanyar cimma maslaha game da rikicin shugabancin jam’iyyar da ya kai ga shiga kotuna daban-daban. Duk da kotun daukaka kara ta janye dakatarwar da a ka yi wa shugaban jam’iyyar Adams Oshiomhole har sai an gama sauraron shari’ar, babbar kotun Abuja kuma, a wani umarnin, ta ce mukaddashin sakataren jam’iyyar, Victor Giadom, ne zai yi rikon kwaryar jam’iyyar har sai an yanke hukunci ko kuma sai idan kwamitin koli na jam’iyyar ya yanke…

Karanta...

Za A Haramtawa Barayin Gwamnati Yin Takara

Shugaban kwamitin majalisar wakilai a kan rundunar sojoji Abdulrazaq Namdas ne ya gabatar da bukatar a gaban majalisar wakilai ns doka da ke neman a haramta wa wadanda ke da tarihin aikata laifi imma a Najeriya ko waje yin takarar mukamin shugabanci na siyasa. Abdulrazaq Namdas (APC Adamawa) ne ya gabatar da dokar mai taken “National Convict and Criminal Records (Registry) Bill, 2020”. Namdas ya kuma kasance Shugaban kwamitin majalisar wakilai a kan rundunar sojoji. Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, dokar ta nemi a durkushe kudirin ‘yan siyasa da ke…

Karanta...