Takin Zamani Na Dangote Zai Bunkasa Tattalin Arzikin Kasa – Dangote

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya bayyana cewa samar da ma’aikatar Taki ta Dalla Biliyan 2 da kamfanin zai samar a yankin Lekki Jihar Legas, zai taimaka wajen habaka ayyukan noma da bunkasa tattalin Arzikin Kasa. Ya kara da cewar ma’aikatar zata taimaka matuka wajen samar da ayyukan yi ga Matasa masu yawa, da taimaka wa Gwamnati ta bunkasa ayyukan noma da samar da abinci ga ‘yan Najeriya. Dangote wanda ya samu wakilcin babban Darakta na kamfanin Injiniya Ahmad Mansur a rana ta musanman da aka ware wa…

Karanta...

Mulkin Buhari Bai Tsinanawa Arewa Komai Ba – Ango Abdullahi

Shugaban Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) Farfesa Ango Abdullahi, ya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gaza kuma ya kunyata ’yan Arewa a idon ’yan Najeriya. Ya bayyana haka ne lokacin hirarsa da manema labarai a Gombe jim kadan bayan kammala kaddamar da shugabannin Gamayyar Kungiyoyin Arewa (Coalition of Northern Group. Kuma ya ce tsarin karba- karba ba dimokuradiyya ba ne: Me za ka ce kan tsarin karba-karba a siyasar Najeriya ganin mulki zai koma Kudu a shekarar 2023? Babu inda aka rubuta cewa za a rika yin karba-karba tsakanin Kudu…

Karanta...

Hatsarin Mota Ya Lashe Rayukan Masu Halartar Wa’azin Kasa

Ayarin matafiya wa’azin ƙasa da ƙungiyar Jama’atul Izalatul Bidi’a Wa’iƙamatus Sunnah (Nat. HQT Jos) za ta gudanar a babban birnin tarayya Abuja sunyi hadari a jihar Neja, inda mutane bakwai suka riga mu gidan gaskiya yayin da mutane huɗu suka samu mummunar raunuka waɗanda ake cigaba da duba lafiyar su a babban asibitin Aminu Goje dake garin Bangi. Matafiyan waɗanda suka taso daga garin Bangi dake Jihar ta Neja sunyi hatsarin ne a tsakanin garin Galma zuwa Igwama dake ƙaramar hukumar Mariga a yau asabar, inda rahotanni suka tabbatar da…

Karanta...

Barin Kan Iyakokin Kasa Bude, Shine Silar Sabbin Hare-Hare – Matawalle

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya bayyana cewa rahin tsare iyakoki yadda ya kamata shi janyo sabbin hare hare da aka kai a Zamfara kwanan nan. Gwamnan yabayyana hakan ne a wata takarda da Zailani Bappa, mai bada shawara ta musamman ga gwamnan a kan wayar da kai da yada labarai ya rabawa manema labarai a Jihar. Gwamna Bello Mohammed ya jajanta yadda tsagerun suka kutsa kauyukan Gummi, Bukkuyum, Anka da Maru da ke jihar Zamfara ya kuma kwatanta lamarin da mara dadi kuma abun alhini. Lamura dai na kara…

Karanta...

Gwamnatin Tarayya Zata Ciwo Bashin Bilyan 45 Domin Sanya Yara Makaranta

Ministan ilimi Adamu Adamu ya bayyana cewa gwamnati za ta ciyo bashin Naira biliyan 45 daga asusun ‘Global Partnership for Education (GEP)’ domin rage yawan yaran dake gararamba a kasar nan. Adamu ya ce gwamnati ta ciyo bashin Naira biliyan 220 daga Bankin duniya domin cin ma wannan buri a kasar nan. Bincike ya nuna cewa akwai yara sama da miliyan 10 da basu makarantan boko a kasar nan. Ministan ilimi ya fadi haka ne a taron kungiyar kasashen rainon Ingila ta shekarar 2020 da aka yi a Abuja. Taken…

Karanta...