Muna Da Matasan Da Zasu Iya Rungumar Mutuwa Saboda Zakzaky – Yakubu Yahaya

“Inna lillahi wa inna ilaihirraji’un, dalilin fitowan mu musamman yau da aka kai su Malam Kotu, kuma sukayi abinda suka ga dama wanda ya sabama dukkan dokoki na duniya dana hankali dana ilimi da ka’ida da doka. Ko ba komai bawan Allah kowa yasan halinda yake ciki na Guba da aka bashi, wanda kuma duk duniya ta shaida, koda mutum kisan kai yayi sai ya zamo baida lafiya ko gobe za’a rataye shi sai an kai shi asibiti ya samu lafiya sannan azo a rataye shi”. Ballan tana Malamin nan…

Karanta...

Katsina: Malamin Makaranta Ya Kashe Daliba Da Duka

Ana zargin wani malamin lissafi na makarantar sakandare ta koyon Larabci (Government Girls Arabic Secondary School) dake cikin garin Fago a karamaar hukumar Sandamu ta jihar Katsina da yi wa wata dalibar duka wanda ya yi sanadiyyar mutuwar dalibar mai suna Fatima Tasi’u. Malamin da ake zargi da yin duka, mai suna Abubakar Suleiman, da ake wa lakabi da Sikiti, kamar yadda wasu suke fadi cewa asalinsa ba cikakken malamin makarantar bane, principal din makarantar ne ya dakko shi sojan haya kuma yana biyansa N5,000 duk wata. A lokacin da…

Karanta...

Muna Kira Ga Sanusi Ya Gaggauta Kai Kanshi Hukumar Yaki Da Rashawa – Kungiyar Musulunci

Wata kungiyar Musulunci mai suna Muslim Youth League (MYL) ta yi kira ga Sarkin Kano da ya mutunta kanshi ya gurfana gaban Hukumar yaki da rashawa ta Jihar domin amsa tambayoyin tuhume tuhumen da ake yi mishi. Hukumar ta zargi Sarkin da sayar da wasu filaye ba bisa ka’ida ba mallakar masarautar da kudin su ya kai naira biliyan 2 kuma da karkatar da kudaden ta hanyar amfani da wasu kamfanoni domin amfanin kansa. Kungiyar ta bayyana takaicin ta kan yadda ake yawan zargin Sarkin da aikata rashawa. A cikin…

Karanta...

Babbar Magana: Bashin Da Ake Bin Najeriya Ya Haura Triliyan 26.215

Bayan ganawar sirri sakamakon sabanin da aka fara samu a zauren majalisa, Majalisar dattawan tarayya ta baiwa shugaba Muhammadu Buhari daman karbo bashin $23bn (dala bilyan 22,798,446,773). Shugaba majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis bayan gajeren mujadalan da akayi kan hakan. Yayinda ake muhawara kan lamarin, shugaban marasa rinjaye, Eyinnaya Abaribe, ya gargadi majalisar kan baiwa shugaban kasa daman karbo bashin duka kudaden a lokaci guda. Ya bada shawaran cewa a yi muhawara kan ayyukan da za’a karbo bashi kansu daya bayan daya. Amma shugaban…

Karanta...