Coronavirus: Gwamna Matawalle Ya Dakatar Da Kai Dalibai Kasar Sin

Gwamnatin jihar Zamfara ta soke tafiyar dalibai 20 da ta dauka nauyin karatunsu zuwa kasar China a karkashin tallafin gwamnatin jihar. Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito cewa Gwamna Bello Matawalle ya sama wa dalibai 200 na jihar gurbin karatu a makarantu daban-daban na fannin kimiyya da fasaha. An samu guraben karatun ne a kasar India, Sudan, Cyprus, China da sauransu. Hukumar daukar nauyin karatun ta jihar Zamfara din ta tantance daliban da suka samu nasara. A cikinsu kuwa wasu na kasashe daban-daban sun fara tafiya karatunsu. Sakamakon barkewar…

Karanta...

Ban Yi Nadamar Yanke Hannuna Da Shari’a Ta Yi A Zamfara Ba – Lawalli

A zantawar da ‘yan jarida suka yi da shi a wannan makon, an tambaye shi yadda yake rayuwa bayan an cire masa hannu ta sanadin shari’ar Musulunci a jihar. Lawalli ya ce, “Ba ni kadai aka cire wa hannu ba a wannan lokacin. Ni ne na biyu a jihar kuma na karshe. Mutum na farko shine Bello Buba Jangebe wanda aka cire wa hannu a 2000 a kan satar Shanu. Ni kuwa an cire min ne a watan Maris na 2001 kuma daga nan ba a karawa wani ba. Na…

Karanta...

Hana Bara: Ku Nemi Zama Da Gwamnati Ba Suka Ba – Pantami Ga Malamai

A ranar Juma’a ne ministan harkokin sadarwa, Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami, ya bayyana rashin amincewarsa da malaman addinin Islama da ke sukar dokar hana bara a jihar Kano da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar. Ministan ya bayyana matsayarsa ne yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai jim kadan bayan ya kammala gabatar da takarda a wurin wani taron shirin yaye dalibai da kwalejin kimiyya ta Kano (Kano State Polytechnic) ta shirya ranar Juma’a. “A fahimtar da nake da ita a kan wannan batu, ba daidai bane a wurin…

Karanta...