‘Yan Siyasa Na Da Hannu Dumu-Dumu A Matsalar Tsaro – Yero

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mukhtar Ramalan Yero, ya yi magana a game da halin rashin tsaro da ake fama da shi a Najeriya inda ya bada wasu shawarwari. Mukhtar Ramalan Yero ya ke cewa abubuwa biyu ne su ka jefa kasar a halin da ta ke ciki, A na sa ra’ayin ba komai ba ne wadannan sai talauci da rashin shugabanci. Alhaji Mukhtar Ramalan Yero ya nuna cewa muddin ba a fito an yi yaki da talauci da kuma bata-garin shugabanni ba, ba za a taba samun zaman lafiya a…

Karanta...

Har In Mutu Ba Zan Daina Rawa A Fim Ba – Sadik Sani Sadik

Fitaccen jarumin Kannywood, Sadiq Sani Sadiq ya bayyana cewa ba zai daina rawa ba a fina-finan Hausa har sai ya tsufa kuma baya iya rawan. Sadiq ya sanar da hakan ne a wata hira da yayi da BBC Hausa a ranar Laraba. Sadiq ya ce ba zai daina rawa ba a fim “ba nan kusa ba saboda inason cashewa. Koda kuwa na tsufa zan kada kafafu na”. Sadiq na daga cikin ‘yan Kannywood da ke jan zarensu a masana’antar fim din. Ana ganin hazakarsa da kuma kwarewarsa ta yadda yake…

Karanta...

Kyakkyawan Karshe: Ya Rasu Yana Cikin Sujada A Sokoto

Wani Dattijo mai shekaru 71 mai suna Malam Ahmad Abdullahi, wanda aka fi sani da Asi, ya mutu a yayin da ake sallar Juma’a, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito. Malam Ahmad ya rasu ne a Masallacin Sultan Bello, dake Sokoto a yayin da yake gabatar da raka’o’i biyu na sallar Juma’a. A cewar wasu masallata, ya mutu ne a lokacin da ake gabatar da raka’ar karshe, inda ya kasa dagowa daga sujjada. Babu ciwo babu komai a tare da wannan bawan Allah, an bayyanashi a matsayin mai tsoron Allah,…

Karanta...

Saura Kiris Mu Kawar Da Boko Haram A Najeriya – Buratai

Bayan nasarorin da dakarun rundunar sojojin Najeriya suka samu yayin kai farmaki a mabuya da sansanin ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP tare da kashe wasu kwamandojin da suka yi, Shugaban hafsoshin sojin Najeriya, Laftanal Janar Tukur Buratai ya ce nan da kwanaki kadan za a kawo karshen ta’addanci kungiyar Boko Haram. Bayan hakan, Shugaban sojojin ya kuma taya kwamandojin sansanin sojojin da sauran dakarun sojojin da ke karkashin atisayen Operation Lafiya Dole murna bisa jarumta da suka nuna tare da nasarorin da suka samu a baya bayan nan. Sakon…

Karanta...

Ban Amince Da Sakin Almajiran Zakzaky Da Kotu Ta Yi Ba – El Rufa’i

Gwamnatin jahar Kaduna a karkashin jagorancin gwamnan jahar, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ta dauki alwashin kalaubalantar hukuncin kotun da ta saki ‘yan Shia 92 ta hanyar daukaka kara zuwa kotun daukaka kara. Wata babbar kotun jahar Kaduna ce ta yanke hukuncin sakin ‘yan shi’an tare da wankesu daga tuhume tuhumen dake rataye a wuyansu bayan kwashe tsawon shekaru hudu a gidajen yari, bayan gwamnatin jahar ta kasa tabbatar da laifin mutanen, a cewar kotun. Cikin wata sanarwa da babban lauyar jahar Kaduna, kuma kwamishinar sharia ta jahar, Aisha Dikko ta…

Karanta...