PDP Ta Kalubalanci Buhari Ya Kawo Karshen Tabarbarewar Tsaro A Najeriya

Babbar Jamiyyar adawa ta PDP ta kalubalanci shugaban kasa Buhari da ya dau mamakin da ya wuce ziyarar da ya kai Borno domin kawo karshen wannan kashe- kashen dake faruwa a jahohin kasar nan. Jamiyyar tace wannan ihun da aka yi masa ya nuna masa cewa ya gaza wajen samar da tsaro a kasar nan wanda shine babban alhakin da ya rataya a wuyan sa. Wannan ihun ya nuna yan Najeriya sun yanke tsammanin samun sauki daga wajen shugaban kasa da jamiyyar sa ta APC . Jamiyyar PDP tace Bai…

Karanta...

Ina Mamakin Yadda Kungiyar Boko Haram Ta Kawo Har Zuwa Yanzu – Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari yaje Borno ne daga kasar Habasha inda ya kwashe kwanaki biyar a taron kasashen nahiyar Afrika. Buhari ya bar Borno misalin karfe 4 bayan la’asar ba tare ziyartar garin Auno, inda aka kashe mutanen ba ko gaishe da wadanda suka jikkata kuma suke kwance asibiti ba. Shugaban kasan ya bayyana cewa a fahimtar da ya yiwa al’adar kasar nan yana mamakin yadda Boko Haram ta rayu har zuwa yanzu. Yace: “Saboda haka a fahimtar da na yiwa al’adarmu, ina mamakin yadda Boko Haram ta cigaba da kasancewa…

Karanta...

Boko Haram Sun Kai Hari Maiduguri Jim Kadan Bayan Tafiyar Buhari

Mun samu ruhoton Mayakan boko Haram sun kai wani sabon hari a garin Maiduguri jim kadan bayan shugaba Buhari ya kammala ziyarar jajen mutane 30 da boko Haram suka hallaka a garin auno. Harin ya faru ne a Anguwar jiddari polo dake birnin Maiduguri a yammacin yau. Wasu ruhotannin sun ce anyi musayar wuta da jamian soji yayin da mutanen yankin keta gudun ceton rai domin gujewa harin na mayakan boko Haram. Ko a dazu da shugaban ya isa garin na Maiduguri an ga wani faifan bidiyo dayake ta yawo…

Karanta...

Boko Haram Sun Kai Hari Maiduguri Jim Kadan Bayan Tafiyar Buhari

Mun samu ruhoton Mayakan boko Haram sun kai wani sabon hari a garin Maiduguri jim kadan bayan shugaba Buhari ya kammala ziyarar jajen mutane 30 da boko Haram suka hallaka a garin auno. Harin ya faru ne a Anguwar jiddari polo dake birnin Maiduguri a yammacin yau. Wasu ruhotannin sun ce jami’an tsaro sun ta musayar wuta da yan boko Haram din indamutanen yankin keta gudun ceton rai domin gujewa harin na mayakan boko Haram Ko a dazu da shugaban ya isa garin na Maiduguri an ga wani faifan bidiyo…

Karanta...

Bunkasa Hasken Lantarki: Najeriya Ta Samu Tallafin Dala Miliyan 1

Hukumar bunkasa kasuwanci ta Amurka ta shiga yarjejeniyar kulla huldar raya arziki da kasuwanci in da ta ba da tallafin dalar Amurka Miliyan 1.1 don samar da wutar lantarki mai karfin Megawatt 1,350 a Najeriya. An sanya hannu kan yarjejeniyar da kamfanin man fetur na Najeriya, NNPC a Abuja don samar da wutar a cibiyar da a ka kebe a yankin Gwagwalada. Wannan tallafi da aikin bunkasa mu’alar cinikaiya na hukumar ta Amurka ya kara bunkasa a rubu’in karni a bangaren iskar gas a kasashen duniya. “Mun taimakawa aiyuka da…

Karanta...

Muna Iya Bakin Kokarin Mu Wurin Kawo Karshen Ta’addanci A Najeriya-Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari y ace, gwamnatinsa ta mayar da ciakken hankali wajen yaki tare da kawo karshen ayyukan ‘yan bindiga da ta’addanci a kasar. Buhari ya bayyana haka ne a birnin Addis Ababa na Habasha a yayin wata ganawa da shugabannin Kwamitin Kula da Al’ummar Najeriya da ke rayuwa a Habasha. Shugaba Buhari ya roki ‘yan Najeriya da su mara baya ga hukumomin tsaron kasar da ke aikin tabbatar da hadin kan kasa. A yayin gudanar da taron, an yi shiru na minti daya domin karrama mutanen da Boko…

Karanta...

Dalilina Na Maka Rundunar Soji A Kotu – Gashash

A ranar talata ce, Sardaunan Matasan Nijeriya kuma mazaunin jihar Kaduna Alhaji Mohammed Ibrahim Gashash ya maka rundunar Sojin Nijeriya a gaban Babbar Kotun Tarayya dake da zamanta a jihar Kaduna. Gashash ya kai karar ce a gaban Mai Shari’a Alkaliyar Babbar Kotun ta daya dake Kaduna Z. B Abubakar. A hirarsa da manema labarai jim kadan da fitowa daga Kotun Gashash ya ce, Sojojin sun kama ni suka kuma tsareni ba tare da wata kwakwarar hujja ba kuma ba tare da sun gabatar dani a gaban Kotu ba. Ya…

Karanta...

Kotu Ta Bukaci Gwamnati Ta Biya Sowore Naira Dubu Dari Biyu

Babban kotun tarayya dake Abuja a ranar Laraba ta nemi Babban mai shigar da kara na gwamnatin tarayya, Abubakar Malami da su biya naira dubu dari biyu bisa abin da kotun ta kira “bata lokaci wajen gabatar da karar Omoyele Sowore.” Sowore da kuma Olawale Bakare, ana zarginsu ne da zarge-zarge guda bakwai ciki kuwa har da na cin amanar kasa, zagin shugaban kasa Buhari da sauran su. Sowore da Bakare DSS sun cafke su ne a ranar 3 ga watan Agusta bisa zarginsu da shirya zanga-zangar nan ta #RevolutionNow.…

Karanta...

Kisan Kiyashin Auno: Shugaba Buhari Zai Kai Ziyarar Jaje Borno A Yau

Fadar shugaban kasa ta bada sanarwar cewar shugaba Buhari zai kai ziyarar gani da ido da kuma jajantawa mutanen Borno akan kisan mutane 30 da boko Haram tayi a garin auno dake jihar Borno Shugaba Muhammadu Buhari ya ziyarci kasar habasha domin halartar taron kasashen afrika inda ya kwashe kwanaki 5 tare da wasu gwamnoni biyu da sauran mukarraban gwamnati. Shugaba Muhammadu Buhari zai dawo kasar a yau laraba, inda zai wuce garin Maiduguri domin ziyarar jaje. Daman dai yan Najeriya nata korafi akan halin ko in kula da sukace…

Karanta...

Yan Bindga Sun Hallaka Mutane 16 A Kaduna

Kimanin mutane 16 yan gida daya sun rigamu gidan gaskiya bayan yan bindiga sun bankawa musu wuta yayinda suka kai hari kauyen Bakali, dake Fatika, karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna. An samu labarin cewa yan bindigan sun dira kauyen ne ranar Talata misalin karfe 4 na yamma kuma suka fara banka wuta kan kayayyakin masarufi, motoci, da babura. Yan bindigan sun kulle yan gida daya a cikin daki kafin banka musu wuta. Daily Trust ta ruwaito. Wani dan garin, Alhaji Sani Bakali, wanda ya bayyana cewa yan bindiga kimanin…

Karanta...

Dakatar Da Hafsoshin Tsaro Ba Zai Kawo Karshen ‘Yan Ta’adda Ba – Burutai

Babban hafsan Sojan kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya bayyana cewa bai kamata a tunzura shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen daukan matakin tsige manyan hafsoshin tsaro ba, saboda shi kadai ya san inda matsalar take. Buratai ya bayyana haka ne cikin wata tattaunawa da ya yi da jaridar TheCable, Thisday da kuma gidan talabijin na Arise a ranar Talata, 11 ga watan Feburairu a jahar Legas. A kwanakin baya ne majalisar dokokin Najeriya ta nemi Buhari ya sallamki kafatanin hafsoshin tsaron Najeriya saboda abin da suka bayyana a matsayin…

Karanta...

Dakatar Da Hafsoshin Soji Ba Zai Kawo Karshen ‘Yan Ta’adda Ba – Burutai

Babban hafsan Sojan kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya bayyana cewa bai kamata a tunzura shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen daukan matakin tsige manyan hafsoshin tsaro ba, saboda shi kadai ya san inda matsalar take. Buratai ya bayyana haka ne cikin wata tattaunawa da ya yi da jaridar TheCable, Thisday da kuma gidan talabijin na Arise a ranar Talata, 11 ga watan Feburairu a jahar Legas. A kwanakin baya ne majalisar dokokin Najeriya ta nemi Buhari ya sallamki kafatanin hafsoshin tsaron Najeriya saboda abin da suka bayyana a matsayin…

Karanta...

Dangote Ya Haye Martaba Ta Farko Na Wanda Ya Fi Kowa Arziki A Afirka

Hamshakin mai kudin Najeriya kuma Bakano, shugaban kamfanin Dangote Group, Alhaji Aliko Dangote, ne mutum mafi arziki a nahiyar Afrika a shekarar 2020. Rahoton Forbes. Wannan shine karo na tara a jere da attajirin ya zarcewa dukkan masu halin nahiyar. Jerin masu kudin ya mayar da hankali kan kasashen Afrika takwas masu kudi; yayinda kasar Masar da Afrika ta kudu suke da masu kudi biyar-biyar a jerin, Najeriya na da hudu, sannan kasar Maroko mai biyu. Rahoton ya bayyana cewa Alhaji Aliko Dangote ya zo na daya da arzikin dala…

Karanta...

Muna Dab Da Kama Shugaban Boko Haram – Rundunar Soji

Wani kwamandan rundunar sojin Najeriya, Janar Abdul Kalifa Ibrahim, ya bayar da tabbacin cewa sojoji sun jajirce a kokarinsu na kamo Shugaban kungiyar yan ta’adda na Boko Haram, Shekau, jaridar Vanguard ta ruwaito. “Da izinin Allah, za mu samu nasara,” in ji shi. Janar Ibrahim ya yi magana ne a wata hira da muryar Amurka a ranar Talata. Da yake magana kan sabon harin da aka kai hanyar Damaturu- Maiduguri, kwamandan sojin ya ce: “zancen gaskiyashine cewa mutane sun yi zarya a hanyar nan ba tare da matsala ba amma…

Karanta...