An Kuma: Wata Mata Ta Hallaka Mijinta A Katsina

Rundunar ‘Yan Sandan jihar Katsina shiyyar ƙaramar hukumar Malumfashi ta yi nasarar damke wata mata mai suna Rabi Shamsuddeen, sakamakon kashe Mijinta mai suna Shamsuddeen Sani. Lamarin dai ya faru ne a cikin gidan su dake kauyen Almakiyayi Danjanku Tasha dake karamar hukumar Malumfashi da asubahin ranar yau Litinin. An yi gaggawar kai Mijin nata Babban Asibitin Malumfashi na Galadima, inda aka sanar da rasuwar shi daga bisani. Rahotanni sun bayyana cewar Rabi ta hallaka mutum Mijin nata ne biyo bayan wata takaddama da ta shiga tsakanin su. Jami’an hulda…

Karanta...

Kotu Ta Yankewa Maryam Sanda Hukuncin Kisa

Wata kotu a Abuja, babban birnin Najeriya, ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan Maryam Sanda, matar da ta kashe mijinta. An yanke hukuncin ne bayan gurfanar da matar bisa laifin daba wa mijinta mai suna Bilyaminu Bello wuka a shekarar 2017, sakamakon rikici a tsakaninsu. A ranar Litinin ne kotun ta yanke hukuncin bayan dage zamanta a ranar 25 ga watan Nuwamba. Sanar da hukuncin ke da wuya, Maryam ta yi ta kuruwa a zauren kotu. A baya ta musanta zargin inda ta ce mijin nata ya…

Karanta...

Kotu Ta Kama Maryam Sanda Da Laifin Aikata Kisa

Bayan Alkalin kotun Abuja dake unguwar Maitama, Yusuf Halilu, ya kama Maryam Sanda, da laifin kashe mijinta, an yi wani gajeran rikici a cikin kotun. Alkali Yusuf Halilu na furta cewa an kama ta da laifin kashe mijinta, Maryam Sanda ta arce daga cikin akwatin mai laifi a kotu amma ma’aikatan gidan Kurkuku da kotun suka damkota. Rikicin ya tilastawa Alkalin tafiya hutun rabin lokaci bayan mata da suka fara yi masa ihu a cikin kotun. Yayinda daya daga cikin matan tayi kokarin zuwa wajen Maryam Sanda, Alkalin ya bada…

Karanta...

Wasanni: Saudiyya Za Ta Sayi Babbar Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa

Mun samu labari cewa Kasar Saudi Arabia ta na tattaunawa da kungiyar Newcastle United domin sayen kulob din daga hannun Mai rike da ita. Gidan yada labarai na Reuters ya kawo rahoto cewa kasar Larabawan ta na son sayen Newcastle a kan kudi fam miliyan £340 idan har an tsaida ciniki. Kasar za ta biya wannan kudi ne daga babban asusun gwamnati na Sovereign Wealth Fund kamar yadda wata jaridar Wall Street ta bayyana. Fitaccen Attajirin nan, Mike Ashley, shi ne wanda ya ke da mallakar kungiyar kwallon kafar. Tun…

Karanta...

Bani Da Lokacin Saurarar Surutan TY Ɗanjuma – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ra’ayin Theophilus Danjuma ba shi da amfani fiye da na miliyoyin ‘yan Najeriyan da suka kada masa kuri’a don tabbatar da zarcewarsa a 2019. Buhari ya yi wannan tsokacin ne a tattaunawar da shugaban kasar yayi da “The Interview” ta yanar gizo kuma aka saki a Abuja a ranar Asabar. Wata takardar da aka bai wa manema labarai wacce ta fito daga hannun babban editan jaridar a ranar Lahadi, ta bayyana manyan tsokacin da shugaban kasar yayi. Da aka tambayi Buhari a kan kuri’ar…

Karanta...