Bauchi: An Garzaya Da Gwamna Asibiti

An kwantar da gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed (Kauran-Bauchi) a wani asibiti can a kasar Landan. Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban mataimaki na musanman ga gwamnan jihar ta Bauchi akan harkokin yada labarai, Mukhtar Gidado kuma aka raba ta ga manema labarai. Inda kuma daga can gadon asibitin gwamnan dake kasar Landan ya aiko da sako na musanman ga al’ummar jihar Bauchi cewa yana shaida masu yanzu haka yana kwance a gadon asibitin ana dab da saurarar hukuncin karar sa…

Karanta...

Yawan Haɗuwar Tinubu Da Atiku Na Ɗaukar Hankali

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi karin haske a kan haduwarsa da jagoran jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu. A cewar Atiku, haduwar tasu bata da nasaba, ta kusa ko ta nesa, da siyasa, kawai sun hadu ne a wurin daurin aure. A ranar Asabar ne shugaban hukumar yaki da rashawa na farko, Nuhu Ribadu a ranar Asabar ya hada manyan ‘yan siyasan kasar Najeriya a karkashin inuwa daya. Dukkansu sun hadu ne masallacin An-Nur dake Abuja a yayin shagalin bikin dan Nuhu Ribadu, Mahmud da matarsa,…

Karanta...

Zargin Damfara: EFCC Ta Yi Shehu Sani Ɗaurin Minti

Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta rufe asusun bankin Shehu Sani, tsohon sanata mai wakiltar jihar Kaduna ta tsakiya, tare da hana shige da fice cikin asusun. A wata takarda da babban mai bada shawara na musamman ga Sani, Suleiman Ahmed, ya fitar a ranar lahadi, ya jajanta yadda aka tirsasa sanatan da ya bayyana kadarorinsa. Hukumar EFCC din ta damke Shehu Sani ne sakamakon zarginsa da ake da damfarar Sani Dauda wasu makuden kudade, a kan zai ba Ibrahim Magu don ya rinjayi wani bincike da hukumar ke…

Karanta...

Sirrin Tara Dukiyata – Ɗangote

Attajirin Afirka Alhaji Aliko Dangote ya bayyana sirrin yadda ya mallaki makudan kudade da ake jin sunansa a ko ina a fadin Duniya. Aliko Dangote ya bayyana wannan ne lokacin da ya yi hira da David Rubenstein na Bloomberg Africa a makon da ya gabata. Attajirin ya tabbatar da cewa ya tashi a gidan arziki domin Kakan kakansa, Alhassan Dantata ya taba zama Mai kudin Afrika. Dangote ya kuma bayyana cewa Kakan Mahaifinsa, Alhaji Sanusi Dantata, ya na cikin masu kudin da aka yi a zamaninsa. Alhaji Dangote wanda shi…

Karanta...

Sojojin Najeriya Ba Su Da Wata Ƙima A Idanuwan ‘Yan Najeriya – Wike

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya bayyana cewa rundunar sojojin Najeriya ta rasa duk wata kima da take da ita saboda ta bari ana amfani da ita domin yin magudin zabe a cikin kasa. Wike ya bayyana hakan ne ranar Lahadi yayin da ya halarci Coci domin bikin ranar tunawa da gudunmawar mazan jiya. A cewar gwamnan, ‘yan Najeriya ba zasu karrama dakarun sojojin da ake hada baki da su domin tafka magudin zabe ba. “Ba zamu karrama dakarun soji da basu da kwarewar aiki ba kuma ake hada baki…

Karanta...

Yau Kotun Ƙoli Za Ta Raba Gardama Tsakanin Ganduje Da Gida-Gida

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, na jam’iyyar APC da abokin hamayyarsa, Abba Kabir Yusuf, na PDP sun bayyana yadda suke kyautata zaton samun nasara a kotun kolin da za’a zauna yau Litinin, 13 ga watan Junairu, 2020. A ranar Juma’a, kotun kolin tarayya ta sanar da bangarorin biyu cewa ta zabi ranar Litinin domin yanke hukunci kan karar Abba Kabir Yusuf, inda yake kalubalantar nasarar gwamna Abdullahi Umar Ganduje, a zaben 9 da Maris, 2019. Dan takarar PDP ya garzaya kotun koli ne bayan ya sha kasa hannun Ganduje a…

Karanta...